ZARRAH

621 15 2
                                    

*ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*

_Bismillahir Rahamanur Rahim_

_Page 3-4_



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7




____________________________
____________________________

Wani matsiyacin kallo yayi Mata ya watsar da ita sosai kalamanta sun Sosa zuciyarsa tunda yake baitaba katarin haduwa da tsageran daya taba duban tsabar idonsa ya fada Masa kwatankwacin wadannan tasassun kalaman ba sai wannan kucaka Kuma qazamar yarinyar almajira lallai ta daukowa kanta bala'in dazai addabi rayuwarta ko mutum me cikakken gata yace zaija dashi wahala yakesha balle matsiyaciya almajira da ko arziqin yar aikin gdansa batakai ba.
Juyawa yayi ya fice daidai lkcn da Inna ta bude idanunta ta saukesu akan Asma'u ta yafitota da hannu ta matsa da sauri ta tsugunna tare da cewa “sannu Inna inane yanzu yakeyi Miki ciwo?" Girgiza Mata Kai tayi cikin muryar ciwo tace “naji sauqi Asma'ul Husnah meye yasaki kuka" sunkuyar da kanta tayi tare da saurin goge hawayenta tace “karki damu Inna zaki iya tafiya mu fita mu samu dan sahu mu tafi wani asibitin?" Zuro qafarta tayi ta miqe tace “zan iya Mana Asma'u dama sarqewar numfashin ne kawai Kuma yayi sauqi ince dai ba wanine ya sake farautar mutuncinki ba?" Murmushi ta qaqaro cike da tausayin Innanta tace “aa Inna muje gda zan baki labari yau na hadu da wani taqadirin dan iska da baisan darajar uwarsa ba bakiga cin mutuncin da yayi min ba harda Marina kawai don na tareshi ya taimakemu ya kawomu asibiti qememe dake dan dudun maguzawa ne yaqi  harda tukuicin baqaqen maganganu yayi tafiyarsa sai wanine ya tare Mana dan sahu mukazo nan asibitin ashe Wai na dan bamagujiyar nanne infadamiki yazo ya duba kowa yana ganina ya juya zai tafi nikuwa na rama maganganun daya fadamin nace indai bai dubaki ba kika mutu ya jira ZARRAH ta sai nayi shari'a dashi".....


Dariya Inna tayi ta lalubota ta rungumeta tace “ho ma'u na baki barin ta kwana do Allah ki rage zafin zuciya Kinga ke macece gdan wani zaki ki rinqa hqr da lamarin rayuwa kinji" cuno baki tayi gaba tace “waike waike Inna saikiyita cewa mutum yayi hqr Kuma mutanen duniya ba mutunci da hqr suka sani ba Ni kawai in anyimin ramawa zanyi idan mutum ya cika zaqewa nace ya jira lkcn da zan zama babbar likita wlh idan tsohuwarsa tazo hanuna allurar mutuwa zanyi Mata"
Dariya sosai Inna tayi tace “Ma'ulele ma'un Inna tashi mu tafi kinji kar yazo yaci Mana mutunci" miqewa tayi ta Kama hannuta suka fito harabar asibitin cikin sa'a kuwa suka samu sahu suka hau zuwa unguwarsu Asma'u tabashi kudinsa a gurin bada kudin ma saida akaso ayi fada da dan sahu Saida Inna tasa baki sannan ta hqr suka tafi tanata mitar ita Inna komai akayi tace ayi hqr kamar wacce akayiwa wankan farko da ruwan alwalar La'asar🤣
Suna shiga gdan taci karo da Dije yar kishiyar Inna ta debo ruwa a bohol tana ganin Inna ta shige daki ta angije Dijangala ruwan ya tuntsire akan Lamunde dake tsugune gaban murhu tana hura wuta da bakinta, kafin kace kwabo kokawa ta rincabe tsakanin ita da Dije kiciki kiciki daqyar Malam Husaini dake shigowa ya raba fadan Dije ta tsaransa karya da gaskiya ya kuwa hau ya zauna ya dauki sanda ya shiga bugun Ma'u aikuwa ta angajeshi saura kadan ya fadi tayi waje ta zauna saman dakalin qofar gdan ta rinqa kuka.


Anan Saurayinta Sadiqu yazo ya sameta da qunshin kifinsa ya zauna yayita aikin rarrashinta daqyar ya samu tayi shiru shima Saida yace idan batayi shiruba mutuwa zaiyi aikuwa dake dama kukan na iskanci ne sai tayi shiru ta dago ta kalleshi tace “jiyafa a gabanka Dijangala ta angizani kwata na fasa qwauri sannan ruwana ya zube Amma shi malam babannan saboda suna bashi abinci baice Mata qalaba harma Kaine ka kaini chemist din Sallau shine yau danna rama ya Kama dukana Allah duk ranar da nacimma ZARRAH ta duk sai narama cutar da akayimin


ZARRAHWhere stories live. Discover now