_*Zarrah*_
_*Fauziyyah Tasiu Umar*_
_*23-24*_
Juyawa yayi ya fice daga dakin yaja qofar ya rufe ta miqe ta bude labule tana kallonsa ya bude dayan bangaren ya shiga ya mayar ya rufe taja fasali tare da ajiyar zuciya ta koma ta bude ledar gasasshiyar hanta ce da taji kayan lambu sai qamshin takeyi dayar ledar kuma kaza ce itama ta hadu taja fasali ta zauna da farko kamar kartaci zuciyarta ta raya mata garama taci rabonta ne idan bataci bama ba gwaninta zatayi ba.
Sake budewa tayi ta dauki hantar takai bakinta saida taci iyakar cinta ta kora da lemon ta miqe ta cire mayafinta ta shiga bathroom ta bata lkc tana kallon bayin tana mamakin irin tsaruwarsa kafin ta dauki sabon brush ta bude ta matsi man goge haqori ta wanke ta cire kayanta ta fara kokawa da shower ta hada ruwa tayi wanka ta fito ta shafa mai ta bude wadroop din ta dauko doguwar rigar bacci tasa ta karkade gadon ta haye taja bargo tayi kwanciyarta.Baccinta tayi cikin kwanciyar hankali saboda gajiyar biki bata farka ba sai safiya ta tashi tayi wanka tayi sallah tana saman sallaya taji an taba qofar ta juya ta kalli qofar jin shiru baa qara tabawa ba yasata tunanin babu kowa taxi gaba da lazuminta sake taba qofar ne yasata miqewa tana tambayar “waye" ba ayi mgn ba ta bude qofar taja da baya da sauri Aseem ne tsaye cikin shirinsa na tafiya aiki da tarkacen laptop da takardu a hannunsa.
Qasa tayi cikin ladabi tace “ina kwana" Idanunsa ya dauke daga kanta ya juya ya fara tafiya saida ya kusa step din benen sannan yace “Mimee tana jiranki kije ki hada mata break" wani abune ya caki zuciyarta tana kallonsa ya fice hawaye suka sulalo mata na baqin ciki wannan baqin qasqanci da mahaifinta ya siya mata Allah wadarai dashi, komawa tayi ciki ta dauki wayarta da keta ring ganin number ya mudam tasan Innah keson mgn da ita ta kara a kunnenta a sanyaye, yanayin yanda tayi sallama ya tabbatarwa Innah ba qalau ba taja ajiyar zuciya tace “ya akayine ma'uh na?" Cikin kuka ta durqushe a qasa ta kwashe duk abinda Aseem din ya fada mata ta sanar da Innah Sosai Innah ta girgiza dajin wannan qasqanci da rayuwar Asma'uh ta tsinci kai a ciki amma a fili sai tace “duk a cikin ibada ne kiyi hqr zakiga ribarsa a gaba don Allah badon niba ki mayar da komi ya zama ba komi ba koda anyi abinda ya kamata ki kalla ki kawar dakai wataran sai labari"Cikin mutuwar jiki tace “yanzu Innah yimata zanyi?" Murmushi Innah tayi tace “qwarai kuwa yi zakiyi domin Allah ai lalura ta kori komai kema wataran zata taimakeki" haka inna ta rinqa tausar Asmah hardai ta hqr ta saki ranta ta miqe ta dauki hijjab dinta ta nufi part din Mimee ta qwanqwasa aka bata izinin shiga ta bude ta shiga cikin nutsuwarta me tsayawa a rai tayi sallama, a qasan maqoshi mimee ta amsa tanajin wani kishi na taso mata duk yanda su Saimah sukazo suke koda kyawun matar yayan nasu ganin idonta sai taga tafi haka duk da kasancewar ba fara bace amma a sahun kyawu dole ta karbi lambar yabo.
Rusunawa tayi tace “Ina kwana Aunty...." Numfashi Mimee ta sauke tace “normal ina fatan Honey ya zayyana miki aikinki a gdannan ko?" Jinjina kai tayi Mimee tayi murmushi tace “ok sai a tashi a fara ina buqatar kunun tsamiya ne da qosan bread" miqewa tayi ta fara neman kitchen din ta nuna mata tace “ai basai kin wahala ba da part dinki da wannan duk iri daya ne bambamcin kawai a matsayi yake " duk da Asmah tasan mgn Mimee ta fada mata bata kula ba ta nufi kitchen din a hargitse yake gabadaya kayan sunyi qura ta jinjina kai ta lalubi tukunya ta dora ruwa ta rinqa bude kitchen cabinet din har allah yasa ta samu duk abinda take buqata ta hada ruwan kununta sannan ta debi surfaffen wake tasa masa ruwan zafi ya tashi ta hada tattasai da albasa da attaruhu da duk abinda tasan zata buqata ta wanke ta zuba a blander, a wannan lkcn ilimi ne kawai yake aiki bawai sani ba duk kayan aikin baqine a gurinta hakanan dai ta ganganda ta gama hada komai ta Jere a dinning din ta koma kitchen din ta fara gyaransa saida ta gyareshi tsaf ta wanke kayan da sukayi qura ta mayar dasu muhallinsu sannan ta fita parlor shima ta gyara tayi duk abinda ya dace sannan ta juya zata tafi taji Mimee dake zaune tana kallo tace “ki hau sama ki gyara masa dakinsa"
YOU ARE READING
ZARRAH
General Fictionlbrn wata yarinya yar jagora me burin ganin tayi zarrah a rayuwarta qarshe ta taro fadan da yafi qarfinta