Zarrah

984 48 7
                                    

_*Zarrah*_

_*Fauziyya Tasiu Umar*_

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

_*57-58*_

Tunda su Asmah suka daga zuwa Germany ranar da sukaje ta kwanta rashin lfy kwananta uku a kwance yana kula da ita yana harkar data kaisa suna rayuwar ne a yanda suka farota tun a 9ja duk da cewar yana cutuwa matuqa amma yayiwa kansa alqawarin iyakar lkcn da zata sauko don kanta bazai taba takura mata ba shi kansa yasani ya cutar da ita a baya shekara daya suna kallon juna babu uwar da yake tsinana mata lkcn da ya kamata ta samu kulawar tasa kuma ya bullo mata ta wata sigar to shi meye zaisa ya takurata sai ta tausaya masa bayan shima baiji tausayinta ba a lkcn da ya dace yaji tausayin nata?
Kwanakin nasu sunayi mata dadi kulawar da yake bata tana tsumata sosai baya gajiya da tarairayarta  da nuna kulawarsa akan cikin jikinta, kwanakin sunata tafiya tausayinsa na nunkuwa a ranta sosai musamman yanda taga da dare baya iya bacci ya tashi yakai sau goma a dare kafin asuba idan ta farka kuma yace mata karta damu yana nazarin wasu Abubuwa ne, ta ayyana hqr yafi sau nawa amma kunya ta hanata nuna masa mubaya'arta gani takeyi kamar zaiga rashin kunyarta ko zaqewarta,
Ranar wata Asabar tana kwance a daki tana duba littafin Hisnul muslum wayarta ta shiga ruri ta kifa littafin a kan cikinta ta dauko  wayar number Jiddarh tagani ta kara a kunnenta tare dayi mata sallama suka gaisa ta tambayeta gda ta jikin Innarta.

Shiru ce ta dan ratsa kana Jiddarh tace “meye yake damunki ne Asmah? Ina hankalinki da iliminki ya tafi da kika yarda kike daukarwa kanki wannan nauyin me girma da baki da gurin ajiyeshi?" A mamakance tace “me kuma nayi Jiddarh?" Numfashi Jiddarh ta sauke tace “dazun Inna ta kirani take fada mani cewa mijinki ya kirata yace ta tayashi baki hqr kina fushi dashine akan wani dalili da yaqi fada mata, nasan bazai wucce akan abubuwan da suka farune kika dauki abin kikasa a ranki har ya bawa shaidan gurbi a zuciyarki kike ganin ba komai bane don kinyi watsi da haqqoqin mijinki ko?" Shiru tayi cikin sanyin jiki tama rasa meye ya kamata tace murmushi Jiddarh tayi tace “idan ya kasance mijinki ya cutar dake a cikin rayuwar aure kada kice zaki rama ta hanyar qauracewa shimfidarsa wannan laifine kuma kuskure ne mai girma da mu mata mukeyi Asmah idan wani ya jure wani bazai iya jurewa ba shin kinsan irin azabtuwar da yakeyi da har ya kasa jurewa ya iya tunkarar Inna da mgnr nan?"
Hakana taji zuciyarta ta karye hawaye suka tsiyayo mata jiddarh ta katse shassheqarta da cewa “a matsayinki na wacce take dauke da sabon mutum a jikinta ya kamata kiyi qoqarin zamowa uwa ta kwarai abar koyi da alfahari a rayuwar al'ummar da zasu wanzu ta dalilinki shin ya zaayi hakan ta kasance bayan kin kasance mara yafiya da jin qai ga mahaifinsu a lkcn da yafi kowanne lkcn buqatar jin qanki? Ita mace ta qwarai kullum cikin gaggawa take akan abinda zai faranta zuciyar mijin da ubangiji ya hadata dashi koda kuwa shidin ya kasance cutarta yakeyi Asmah ina baki shawara don Allah kiji tausayin mijinki kada ku zame masa uku bala'i saboda ke uwarsa na neman yi masa baki saboda matarsa sannan kedin kuma ki kasa basa farin ciki don Allah da wanne zaiji?"

Kukanta ne yayi qarfi yanda har Jiddarh take jiyo shassheqarta taja fasali tace “ya zanyi Jiddarh Allah tsoronsa nakeji inason na nuna masa komai ya hucce amma tsoron jizginsa yana hanani kaiwa ga hakan Jiddarh Aseem wani irin mutum ne da bazaki gane ya yake ba indai baki zauna tare dashi ba......" Katseta tayi da cewa “haba don Allah saikace ba mace ba asmah duk yanda zakiyi ki saita mijinki bazai gagareki ba saidai idan haka kikaso dama ki zauna kuna kallon kallo namijin daya fishi taurin kai ma ana juyashi bareshi da rauninsa ya riga ya gama bayyana akanki kiyi qoqari ki zame masa matar da idan ya kalleki zai rinqajin farin ciki a ransa kema Allah zai faranta taki rayuwar kada ki yarda ki zamo mahadin dayar ku taru kuyi baqi a gurin mijinku plz don Allah idan ya shigo kije ki durqusa a gsbansa ki basa hqr nasan zai tambayeki dalili idan ya tambayeki kice, yakai mijina mafi alkhairi sama da duk mazajen dake duniya nasan na sosa zuciyarka da qaurace maka ds nayi tsayin kwanaki inajin tsoron kada wannan dslilin ya zamo silar fushin ubangiji a gareni shiyasa nakeso kace ka yafemin kuma ka tabbatarmin da hakan yanda zuciyata zatayi sanyi na samu nutsuwar cewa mijina ba fushi yskeyi dani ba"
Sosai Jiddarh ta rinqa bata shawari har saida taji a ranta komai ya wucce sannan take fada mata itama ankawo kudinta Dr Mus'ab na Asibitin Aseem shine wanda Allah ya zaba mata, sosai Asmah tayi farin ciki tare dayi musu fatan Alkhairi sukayi sallama ta ajiye wayar tanata tuntun tunin kalaman tabbas gsky Jiddarh ta fada mata dolene ta zamo salihar mata me rangwame yafiya da afuwa ga mijinta kafin ta zamo managarciyar uwa abar alfaharin yaya.
Miqewa tayi ta gyara dakinta ta fito parloun dakin hotel din da suka sauka shima ta gyara ta nufi kitchen abin mamaki babu abinda bai aje musu na amfani ba dangin kwadayi tayi murmushi tanajin wani yanayi game dashi iyakar abinsa bai yarda da wasa da haqqin ciyarwa da tufatarwa da abinda ya shafi lfy ba, ji tayi tanason burgeshi hakanan ta dauki flower ta kwaba ta gasa ta gashin gurasa ta koma gefe taja da baya tayi masa miyar ganye da taji naman rago sai zuba qamshi takeyi ta zuba a mazubi me kyau ta dawo ta hadansa lemon kankana shima da yaji sugar da madara tasa qanqara ta mayar dashi freedge ta ja da baya tayi farfesun hantar ta kasancewar ita kadai takeci ta zauna a cikinta.

ZARRAHWhere stories live. Discover now