Zarrah

754 30 6
                                    


_*Zarrah*_

_*Fauziyya Tasiu Umar*_

_*Elegant online writers*_

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

_*61-62*_

Wannan abu ya sosa zuciyar Mimee hakadai ta share ta koma dakinta ta kwanta abinci wannan kasaci tayi Aseem yayi mugun raina mata hankali watanta na biyu kan uku da yin bari amma tunaninsa baima basa yayi felling dinta ba saboda ya mayar da ita jakka, tashi tayi ta dauko maganin da Mal Dada ya bata ta duba tayi murmushi ta sake kwanciya sai dare sannan ta tashi tayi wanka ta bude kayanta ta dauko rigar bacci ta zura ta sanya turaren da Naja'at ta bata tace tayi amfani dashi, shiga tayi bathroom ta dauki kwalbar maganin ta tsuguna ta dangwalo da auduga ta matsa a gindinta ta miqe ta koma ta kwanta tanajin yanda maganin keyi mata zugi  ji takeyi ksmar taje ta wanke  tuna maqudan kudaden data kashe ne yasata bajewa fanka da a.c na hureta sakaryar ta manta illar iskar gareta.
Tananan kwance ya dawo a hankalinsa nakan Asmah bai shiga dakin mimee ba saida ya shiga dakin Asmah har yanzu tananan da nauyin baccinta na qaddara ya jima yana kallonta yanajin son kasancewa da ita a wannan dare me ni'ima amma babu dama, tsaki yayi ya tsugunna yayi mata addu'a sannan yajs mata bargo ya fice, ya rufenta qofa

Fita yayi ya shiga dakin Mimee tana kwance a gado ya kawar dakai ya shige bathroom yayi wanka ya dawo yana dube²nsa  ta miqe ta nufisa ya nemi guri ya kwanta itama kwanciyar tayi tace “Aseem ni naga kamar bakayi farin ciki da zuwa na ba" kawar dakai yayi tare da miqewa yace “wanne irin turare kikai amfani dashi?" Kallon kanta tayi tace “turare kuma?" Daga kai yayi yace “banson qamshinsa yana tasar min da zuciya yasa kaina ciwo yakeyi bazan iya kwanciya a dakin nan ba"
Miqewa yayi ya fice daga dakin ya koma falo ya kwanta ta miqe da sauri tabisa.

Tarar dashi tayi kwance a kujera ya juya baya ta tsaya akansa tana tunanin ta inda zata fara masa mgn tsoro na neman hanata daqyar ta zauna a kusa dashi ta tabashi tare da kiran sunansa cikin murya me rauni batare daya juyo ba yace mata menene?" A sanyaye tace “meye yasa kakeson nunamin iyakata a gurinka yanzu hakan mutunci ka siyamin matarka ta fito taganka a falo a kwance bayan tasan cewa inanan" numfashi ya sauke ya tashi zaune ya zuba idanunsa masu rikitata a kanta yace “to yanzu me kikeso nayi miki?" Rausayar dakai tayi wai ita kirsa tace “katashi muje mu kwanta mun dade bamu hadu ba wata uku ai ana marmarin juna"
Wani murmushi yayi na qeta tare da qudurcewa a ransa duk abinda zatayi saidai tayi amma bazai kusanceta a yau ba hannu yasa ya toshe hancinsa yace “wannan turaren naki amai yake neman sakani duk da nasan Asmah bacci takeyi amma ranta bazaiso qamshinsa ba karki qara saka manashi anan banson ya cutar da babyna" wani abune me tuquqi ya rinqa taso mata ta miqe a zuciye tace “sannu Alh Qaseem ubana da har kake ganin ka isa ka samin sharadi akan abinda nakeso kuma ma akan wata banzar iskar matark....." Daganta hannu yayi cikin qaraji yace “karki qara zagarmin mata wlh yanzu zan yankanki way kibi jirgib dare dubeki ko fasali babu ni mema zanci dake wata guzuma dake dalla bacemin da gani anan" sosai kalamansa suka sosa zuciyarta ta miqe fuuuuu ta shige daki tare da banko qofar da qarfi yayi murmushi ya koma ya kwanta abinsa.

Tana shiga dakin wayarta ta dauka ta duba Naja'at a online tace _“nifa wannan dan rainin hankalin mutumin yaqi saurarona turaren ma cemin yayi bayason qamshinsa amai zaisashi"_ murmushi naja'at tayi tace _“kuma sai kikayi yaya"_ alamun bacin rai ta tura mata tace _"Kawai nabar masa falon ne na dawo daki"_ zaro ido Naja'at tayi tace _“amma kinkai wawuya takanas saboda aiwatar da wannan aikin kikazo sannan har kiyi fushi gsky kin bani kunya"_
Takaici ne ya cika mimee tace _"to ya kikeso nayi masa ne yaqi saurarona fah har mgn ya fadamin wai nice guzuma"_ murmushi Mimee tayi tace _"to saime indai buqata zata biya aidai ya riga ya shaqi qamshin turaren mgn ta qare ki tashi ki caza dress ki yi wanka ki kashe qamshin ki koma masa ki zama kalar tausayi Aunty Maryam da qauna tsakaninki da Aseem nasan zai kulaki indai muka samu ya shiga maganin da kika matsa ya ratsashi ai magana ta qare yariga ya shigo hannu sai yanda mukayi dashi kuma da hannunsa zaima yarinyar nan dukan da sai cikin jikinta ya zube sannan ya saketa kinga kuwa riba ai tamu ce kamar yanda boka ya fada mana yanzun ke meye yafi miki wannan zaki tsaya kina wani bacin rai na asara"


ZARRAHWhere stories live. Discover now