2_Back 2 sch

50 6 0
                                    

🖤🤍CRAVES🤍🖤

By_nanatoou
Wattpad_@nanatoou

ELEGANT ONLINE WRITERS


                    2_Back 2 sch.


     Muna fita parlour mukai kicibis da Iya, haka na tsaya nai mata sallama, dan sauran tuni sun kama hanyar gaban su. Abinda muka fi tsana kuwa ta fara yi min, tambayar abinda bai shafe ta ba, ina zamu kar mu dade, dama mubar fitar sai gobe yamma tayi. Haka ta fara zaiyano min. I was like na mangare ta, matar nan tana wuce iyakarta, amman kuma na lallashi zuciya ta. Nasan tabbas ko na fusata, dariya su Samha zasuyi min, suce iyayi nane ya janyo min. Haka ya saka na controlling din my risen anger.  Nace mata ai ba nisa zamuyi ba, mukai sallama na fice.

A parking lot na same su, already they were business snapping pics. Na karasa wajan su. Ban tsaya na biye musu dan nasan nace za'ai hotunannan yunzu, ina da tabbacin mu da fita sai maghrib.

Sai da suka tabbatar na tada motar sannan suka shiga. Nai horn mai gadi yazo ya bude mana muka kara gaba.

Sai da aka dauki titi sosai sannan na samu na dube su tare da fadin, "wai ina muka nufa ne?"

"Ask them, ban san inda ya dace mu fara zuwa ba" cewar Fauzy.

"Kunga ba wani jan zance anan, kawai muje mu fara shopping then sai muyi sauran abubuwan" cewar Samha.

Na gyada kaina kafin na dauki hanyar our favourite best shopping complex. Bamu isa wajan ba sai da ana maghrib. Nima dai ban ji dadi ba, ana sallah muna yawo a gari, Allah ya yafe mana ameeen.

Siyayya mukayo sosai, dan komai da mukasan zamu bukace sa sai da muka siya.

Sanda muka fito daga super market din, already dare ya riga da yayi ma.

Mun settling a cikin mota kenan, har nasa key a ignition din, waya na, ya kawo haske, naga Baby Minal. Na saki murmushi taya ma zanyi ignoring call din ta.

Na daga tare da fadin, "that's my little angel ya kike"

"Not good," ta bani amsa, murmushi nayi, duk da bana ganin ta, nasan ta bata fuskan na tata, kai Minal dai ita.

"Oh my goodness, what's wrong with u, i hop is nothing serious" na tambaye ta kamar gaske.

"I'm just missing u, u know there wasn't anyone to play with me. Kuma Mahfouz zalina yake ci" ta kuma maganan muryar ta a karye.

"Okay, don't cry little angel ki barni dashi, tun da ya karya rules din ya sani, mun bata dashi, kuma bazan basa tsarabana ba" na gaya mata cikin lallamin ta.

"Yeeee, nice ni kadai taiki ko?"

"Sure angel" na fada mata ina dariya kasa kasa, kai wayannan yaran sai ni din. Cikin serious tace min,

". Face time, pleassseeee, mum tace zaku fita, so i want to see have beautiful u look kinji...." Ta karasa maganan cikin karye murya, kafin nace wani abu ta kuma rokana, then sai kawai na amsa mata. Mikai disconnecting call din. Na juya baya tare da fadin, "waye zaiyi driving din...?"

Harara Fauzy ta makomin kafin cike da kumfar baki ta fara fadin, "dan tsabar iskanci, ki shanya mu, sannan kuma ki wani zo kinq tambayar mu wani iskanci ko..."

"Okay, i'll drive shikenan," Munaya ta katse Fauzy.

Na fita na koma baya, Munaya kuma ta ja mota muka wuce. Muka fara face time da Minal, kai my angel is the best. Tana gani na, ta fara yimin complaining that she missed me, sannan tai min compliment din shigata. Ta tambayi su Munaya, na haska mata wayan ta gansu, suka gaisa.

Kiranta, da Nannyn su taje yine ya tsayar da hiran da take bani, Minal is a talkative being, duk abinda akayi da bananan take zaiyano min, da yacca sukeyi Mahfouz, haR da gaya min cewa yayi fada yau a makaranta.
Da nannyn ta shigo, inaji tana gaya mata, lesson teachern su yazo, ganin yacca ta turo baki, nasan the next thing she'll argue,  shi ya saka nai mata magana,

"Sweetheart, be a good girl, kije kinji, we'll talk later, kinji darling," na gaya mata cikin kasa da murya, ina lallashin ta.

Tadan kara turo bakin ta, sannan tace, "okay"

Na saki murmushi, i know it, shi ya saka, nake san Minal no matter what in na lallashe ta, to zata yadda tayi abu.  Ina kallo tayi disconnecting.

Nasan yunzu zuwa anjima Mahfouz shima zai kira ni, yai min nasa rigiman shima.

Ba'a jima ba, muka karasa best spot din mu. Duk sanda zamuci abu a waje to nan shine wajan da mukafi zuwa. Kai da kaga gun kasan ya hadu,  ko bakai niyar shiga ba, zaka so ka kashe kwarkwatar idanuwan ka, and the best part ma, abincin su ya hadu.

Muka samu muka shiga, muka sami table of
Four. Muna zam waitress ta karaso, tare da menu. Ta ajjiye mana bayan ta mana sannu da zuwa. Tare da tambayan mu kwana da yawa, Fauzy da yake mutuniyar tace nan ta hau yi mata bayanin ai bama nan ne.

Na ture menu din na dubi waitress din tare da fadin,

"As always, shrimp scampi pizza, with grape juice."

Tai min murmushi, tare da daukan menu din, ta dubi Samha da take ta faman dube dayan. Ni dariya ta bani, kai kace zataga saban abu a ciki, kullum haka ita take.

Munaya tace abu daya za'a kawo mana, ita kuwa fauzy vegetable supreme ne best taste din ta daman.

Samha ta gama kyalkyalin ta daga karshe ta kare a burger dai, tare da iced tea.

Koda aka kawo mana ordern mu, muna ci, muna labarin duniya, bayan mun gama kuma mun biya kudi, mukai ordern wasu ice cream zamu tafi dasu.

Gashi muna san mudan kara wani yawan amman kuma, dare yayi, kuma munsan za'a sami matsala aka kira bama gida. Haka. Ya saka muka dauki hanyar gida. Samha na fama da mitan wai ya kamata ba yunzu zamu koma ba.

Sanda muka koma gida tara da wani abun. Muka samu Iya a parlour tana kallo, nai mata sannu da gida na bata tsaraban ta da muka tawo mata da shi.

Munayin settling a daki kuwa, na fada toilet nai alwala nazo na biya sallar da take kaina, haka suma su Fauzy.

Sai da na gama shirin bacci sannan kiran  daddy ya shigo wayana. Mun dade muna waya, ya bawa momma itama mukai sai da safe.

Sanda na gama wayan kuwa, kowa ya kama gaban sa, sun dauki wayoyi suna ta fama, na dubi time, Momma ta gaya min Minal tayi bacci, shi yasa bazan kira taba.

Ni dai daganan a yacca nake a kwance bansan sanda bacci yai awan gaba dani ba.

The next day, tun Asuba ban koma bacci ba. Dan inasan na shiga makaranta. Na samu na shiga kitchen nayi mana breakfast, sannan na koma na shirya. Ina shiryawan kiran Mahfouz ya shigo min, na dauka muka gaisa yai min complaining wai ban kirasa jiya ba. Na basa hakuri, sannan ya bawa Minal muka gaisa da ita sannan mukai sallama suka tafi sch.

Itama Munaya ta, tashi ta shirya, mukaje muka sha tea, a lokacin Iya nata yan gyare gyaren ta.

Bayan mun gama muka dauki hanyar makaranta muka bar sy Fauzy suna baccin su, ko attempting tashin su bamuyi ba, dan nasan wayan nan biyun kuwa ba lallai ma zuwa goma in zasu tashi ba.

Munyi lectures sosai bamu samu kanmu bama sai sha biyu. Sannan muka samu mukayi free, straight cafeteria muka nufa mukaje muka sa wani abun a cikin mu, dan wlh ji muke uwa tea din da muka sha ma, ba a cikin mu ya shiga ba.

Sai four muka nufi hanyar gida, gaba dayanmu a gajjiye muke.
Ni karan kai na nasan we're back 2 school back to business.


ASTAGFURILLAH WA'ATUBI'ILAIK

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now