5_EPGYT

23 2 0
                                    

5_EGYPT

Bayan sati biyu ya dawo daga Egypt din. Da labarai guda biyu, the good and the bad news.

Hadiza taji dadin dawowarsa sosai, haka ta dunga shige da ficen tarbansa.

Sai bayan magariba sannan suka samu suka zauna, alokacin ne yake gaya mata, Fateema na garinsu. Hadiza taji dadin hakan amman kuma sai murnar taso komawa ciki. Dangin Fateema sunce bazata dawo ba, kuma itama ta goya musu baya. Amman takamemen abinda ya saka tace bazata dawo bane bata fada ba.

Hadiza taji babu dadi, amman kuna sai tayi addu'ar ubangiji ya zaba abinda yafi alkhairi a lamarin.

Wannan shine dalilin barin Fateema gidan. Bayan kamar shekara da faruwar haka, ba wanda yasan meya faru, rana tsaka Malam Shu'aibu ya saki Mairo. Haka ta zauna tana kuka tana basa hakuri amman kuma yace shi baisan zance ba. Hadiza taji ba dadi sosai.

Haule tazo ana gayama Mairo ta dena wahalar da kanta akan namiji Malam Shu'aibun me, sai me dan ya sake ta. Daga wannan magana, suka kaure da kokawa a tsakanin su. Suka dunga zagin juna ta uwa ta uba. Nan kowa ya zage yana tonawa sirrin junansu. Makota kuwa duk an shigo an tsattsaya ana kaan ikon Allah.

Anan ne kuma Haule take fadin, ai ita ta raba Malam Shu'aibu da mayar arzikinsa, shi yasa da Allah ba azzalimin bawan sa bane, sai abin ya dawo kanta.

Haka suka kai tayi, daga karshe dakyar aka samu aka rabasu, sakamakon malam Dikko daya shigo, yaga tabargazar da suke ma juna, nan ya gayama Haule itama taje gida ta huta sai ya neme.

Wannan shiya raba kokawar, Haule ta fashe da kuka, amman baibi takan taba. Yai ficewarsa.

Bayan komai ya lafa kuma, sai da Haule ta kusanyin watq biyu a gida sannan ya dawo da ita da Allah da Annabi. Ita kuwa Mairo tana can tana iddar ta kafin ta shiga layin zaurawa.

A wata na hudu ne da faruwar lamarin, Malam Shu'aibu ya tattara inasa inasa yace ya bar zaman garin ya tafi nema abinsa.

Wannan karanma, Malam Dikko baiji dadin tafiyar aminin nasa ba, amman ba yacca ya iya, sai yayi masa addu'ar Ubangiji ya hada sa da Alkhairan sa ameeen.

Malam Shu'aibu bai tashi dawowa ba, sai bayan shekaru takwas (8).

Sanda ya dawo al'amura da dama sun canza. A lokacin ma, Allah yai ma mahaifansa rasuwa. Malam Dikko ya zama babban mutun, ya tara iyalai, ya aurar da ya'yansa manya mata, ga samari yana dasu, gefe guda ga yara kanana da matar sa ta uku ta haifar masa.

Alokacin Yusuf ya girma har ya kammala karatun secondary dinsa, ya zama saurayi, kyakkyawan bafulatani.

Hadiza kuwa tananan ta zama babbar mace. Ta manyanta, kamala ta fito mata.

Bayan zuwa malam Shu'aibune, ya rasa inda zai saka Yusuf, shi dai yana kaunar yaran ga hankali. Shima Yusuf din sai ya zamana duk inda Malam Shu'aibu yake to yana gurin. Yana darajtasa, kuma hakan ya kara wa malam Shu'aibu kaunarsa.

Watan malam shu'aibu day da zuwa yace shi zai koma, amman kuma tare da yusuf. Yana fadan haka Malam dikko yayi murmushi kawai.

Koda aka gayama Hadiza bata da tacewa, sai mirmushi da tayi kawai, tasan in dai Malam Shu'aibune bata da haufi akan sa.

Haka suka shirya suka tafi. Suka sauka a kano. Gidan da Malam Shu'aibu ya gina. Babban gidane kato, daka ga gidan kasan ba magana akwai dukiya. Haka yusuf yaita kalle kalle a gidan. Sabida shi a wajansa saban abune, bai taba saka kafa yabar gaya ba. Karkarinsa shiga wasu kauyukan na kusa, su siyo shanaye.

A kano aka samu akai masa passport da visan su. Bayan sati guda suka tashi zuwa kasar egypt.

Sanda suka sauka a Egypt, sai Yusuf ya kuma ganin wata sabuwar duniyar. Domin kuwa bai taba zatan kawun nasa yakai haka a arziki ba.

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now