4_ GONE

56 4 0
                                    

  

4_Gone

Ba wanda yace wani abu a gurin, sai dan shasshekar Haule da yake tashi. Yusuf ya kuma taba Fateema yare da fadin, "ummi mu koma daki". Maganan da yayi yasaka ta dube sa, kafin daga bisani ta kuma mai da dubanta kan malam Shu'aibu.

Wannan karan sai ya kauda kansa, ya zo yama wuce ta gaban ta yai hanyar fita daga gidan ba tare da ya kuma fadin koda kallama gida bace.

Ta juya ta bisa da kallo yana kuma jin yacca zuciyar ta ke bugawa har yunzu. Fargaba da rashin sanin takameme mai zai ma faru shi ne abinda ke kawowa zuciyar ta farmaki a halin yunzu.

Tana kallo, ya fice, Abban Yusuf ma ya bi bayansa. Ta lumshe idanunta yana maida numfashi. Sannan taja hannun Yusuf suka koma daki, ba tare da tabi takan abincin dake kan wuta ba, ko kuma Haule da ta saka dankwali ta rufe fuskarta take tajan shassheka, ba tare da tasan cewa Malam Shu'aibu ya fice ma tuntuni ba.

Fateema na shiga daki ta saki hannun Yusuf, ta samu ta kwanta, tana fatan zamun sassaucin farmakin dajin yana barazana ga lafiyar ta.

Bata dade da kwanciya ba taji, yusuf kisa da ita yana tabata yana magana, " ummi baki da lafiya ne?" Ya tambaye ta cike da kulawa.

Ta samu ta bude idanuwan ta ta dube sa, wayanda a yunzu sun sauya launima gabaki dayansu.

Yai saurin mikewa tare da fadin, "ummi zazzabi kike yi.." Daga haka ya fice daga dakin da gudun sa. Tabi sa da kallo kafin daga bisani ta mai da idanuwan nata ta rufe su.

"Fateema, fateema, mai ya same ki " muryar Hadiza ta tayar da ita. Ji tayi kanta yai mata nauyi. Ta saka hannu akan tare da fadin, "washhh..."

Hadiza tai saurin tashi daga zaman da tayi a gefen ta tare da fadin, "sannu, zazzabi ne ke damun ki, bara na samo miki magani" daga haka tai saurin ficewa.

Bata dade ba ta dawo da itatuwa ta jika, ta tashe ta dakyar ta bata tasha. Haka suka wuni a ranar bata da lafiya

Washe gari ma jikin nata, gashi gashi nan dai. Haka taci gaba da zama, har sai da tayi kwana uku, kafin jikin ta yai sauki. Amman kuma walwalar ta yaki ya dawo.

Ba komai ke damin ta ba, sai yacca Malam Shu'aibu, ya watsar da lamarin ta, bai zo inda take bama, ballan tana ta samu damar yi masa bayani, har ta kare kanta. Kuma takaicinta ganin yaki ya bata ko wacca dama kuma ya dauki lamarin da girma.

Hadiza ta tuntube ta akan lamarin barin da akace Mairo tayi, amman kuma sai ta kasa ce mata komai ma.

Hadiza itqma sai ta damu da lamarin, dan Haule da Mairo basu da aiki sai yada magana a tsakar gida, hakan ya saka tasan cewa da akwai matsala amman kuma Fateema taki ta gaya mata, meya faru, balle su san bakin zaran.

Har akayi wata gudq da faruwan lamarin, Amman Fateema lamura sun mata zafi, ta sakawa kanta damuwa, Hadiza tayi lallashi da lallamin amman komai a iska. Sai ramewar da takeyi.

Hadiza har maganan tayi da mijin ta akan ya tambayi Shu'aibu ko yasan abinda ke damunta amman koda aka tuntubesa, sai yace shima bai sani ba ta takurawa kan tane kurum.

Bayan an kuma kwana biyu, ranar wani talata da safe. Hadiza taga har rana ta take amman Fateema bata fito ba. Hakan ya saka taje ta buga mata kofa. Amman kuma sai taji shiru tana turawa taga ta bude sai ta shiga.
Tana shiga kuma taga dakin ba kowa. Hakan ya saka taja burki ta tsaya. Tasqn ceww tun dazu tana tsakar gida balle tace ko fateema ta fita ne. Gashi Yusuf ya tafi makaranta. Tai sauri ta fita daga dakin, Fateema bata taba fita daga gida nata gaya mata ba. Kuma bata fita ita daya sai da Yusuf, to ina tayi kenan?. Ta dade tana zirya a tsakar gida, gasu Haule da suka kasa suka tsare a tsakar gida, muku yunzu mazajan nasu suna can gona. Gashi hankalinta yaki kwanciya da rashin Fateema, abubuwa da dama na kawo farmaki a kwakwalwar ta, tana dai fatan, ko daya bazai kasance a ciki ba, tafisan dai ace dayan tunanin ya tabbata na cewa fitar gaggawace ta sameta, to wacce fitace haka Fateema ba zatayi mata sallama ba.

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now