15_ Baby naming ceremony

23 2 2
                                    


15_ Baby naming ceremony

Abubuwa sukan faru a rayuwar kamar kiftawar ido. Komai aka sa masa lokaci dole sai ya zo, kamar yadda bahaushe kecewa rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya.

Gashi Munaya ta zama Mrs Zain, ta hada komatsan ta ta ƙara gaba, ta barni da kewa.

Abun daya faru bayan rabuwar mu ni da ita, bazai fadu ba.

Munaya itace ni, ni nice Munaya. Akwai wani bond a tsakanin mu wanda nake da tabbacin ba kowani ƴan uwa ne suke sharing ɗin sa ba. Irin bond din da ake samu a tsakankanin identical twins dinnan ne. One can't do without the other.

Nayi kuka kamar ba gobe, rabuwa ta da ita, wanda hakan yai leading dina har akai admitting dina a asibiti.

Everyone was so worried alokacin, babu wanda bai shiga damuwa ba.

Kawai sun san basu saba gani na a wannan yanayin ba, thank god ma, Fauzy tana kusa dani, Tana bani baki, on the other hand kuma ga Samha.
G ta kasa zaune ta kasa tsaye. Haka suka dunga yi min.

A asibitin kuwa, Munaya face timed me, kamar babu gobe. Ranar da akayi admitting dina, har da kukanta, Zain kuma shi aka bari da rarrashi. Nice a kwance amman sai da nayi murmushi ganin yadda takeyi, she was acting like a real baby, irin shakwaɓaɓbun yaran nan, a sangarce. I even tease her a lokacin, irin ko kunyan nan bazata ji ba, ta tuna dai she's married.

Daga baya ma kuwa har da ce min tayi, ita wlh Nigeria zata tawo gani na. Ba zata iya jira har sai ya gama al'amuran sa ba. Sosaai ta bani dariya, lallai da sauran Munaya. Fauzy ce ta samu ta lallaɓa ta kar ta ɗaga zance su Momma su ji ta ma.

Kwana uku a asibitin aka sallame ni. Sosai aka dunga nan nan dani. Ko da yake ma, ana sallamo ni part din G akayi dani, dan acewar ta gwara ta sani a gaba ta dunga tsaro na.

Sosai dangi suka dunga kira na. Business partners din daddy kuwa da suka dunga zuwa dubiya kai kace ba zasu kare ba.

Ni har gajjiya nayi da kiran naji sauki su dai na damuwa, amman magana ta duk a banza.

Haka na samu nayi coping nacigaba da rayuwata, har muka koma makaranta.

Munaya sunyi honeymoon din su sun more sannan suka dawo nigeria.

Haka muka koma makaranta, a lokacin ma har na hakura na saba da rashin ta, sai dai abu daya a koda yaushe ina face timing dinta itama haka, in kuma bama face time, to muna kan voice call . Ta nuna min abubuwan da takeyi na gaya mata nawa.

Munaya ta dauki responsibilities din ta na mace, dan she's claiming the perfect wife.

Har mamaki take bani in tana abubuwan ta.

Komawa makaranta ya kuma dawo da ita kusa da ni. Lectures din mu tare, in mun gama kuma mu samu mu dna tattauna sannan ta wuce gida.

Ranar da ba makaranta kuma na kan daure na je, ina keeping din ta company dan ba ko da yaushe bane Zein yake nan, musamman da hankalin sa kwana biyu ya rabu, shi ba'a Sudan ba ba'a Nigeria ba.

Samha kuwa tananan da kule kulen samarin ta yunzu kusan ko da yaushe sai tayi saban saurayi ina kule da ita. Ni ban san yaushe ta zama haka bama, kula mazan ta yayi yawa.

Fauzy kuwa soyayya take tasha tsakanin ta da Yaya Haseeb.

Ni kuwa bangare guda na killace kaina, har yunzu ni ba wanda na bawa wani dama a fanni na.

Munaya takan dan sako min zancan saurayi lokaci zuwa lokaci, acewar ta wai na samu na bawa wani chance tukunna.

Ni dai kawai ina jin sune amman ba tare da wai na dauka bane.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 27, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now