6_Friends

32 5 0
                                    

    6_Friends.

Haka Shu'aibu ya amshi wannan kyauta dabe taba tsammanin taba. Koda fateema taji abinda ya faru, ita karfafa masa gwiwa tayi tare da fada masa sheikh yasan abinda ya hangone shi yasa ya basa.  Wannan karfin gwaiwar daya samu itace ta saka shima ya karfafawa kansa gwaiwa tare da alwashin zai rike komai yacca ya kamata.

Sheikh Muhammad Nuraddeen, ya zage dantse yana koyawa sirikinsa duk abinda ya kamata ya koya na harjar kasuwanci, koda yake, yariga da yasan wasu da dama. Watanni biyin da suka biyo baya, ba inda sunan Shu'aibu bai zaga ba, daman ga tambarin ya auri the billionaire daughter, to yunzu shima gashi a matsayin billionaire din.

Wata rana yaje wajan Sheikh Al-Rashid, yana zuwa ya tarar dashi a gala baice baya haiyacinsa. Haka aka garzaya aka kaisa asibiti. Bayan zuwan su asibitin ne likitoci suka dukufa akan sa. Domin ceto rayuwarsa.

Bayan wasu hours, Shu'aibune gaban likita yana masa bayanin ciwon Sheikh Al-Rashid ne ya tashi. Bayan ya tambayi wani ciwone haka, anan doctor din ke gaya masa yana fama da ciwon tumor cancer. Wannan abu ya girgiza Shu'aibu, bai taba tsammanin haka ba. Koda wasa bai taba gaya masa cewa yananda wannan cutar ba. Likitan yacigaba da yi masa bayanin cewa zasu shiga dashi theatre nan da awa biyu, in anyi nasara zai tashi, amman sabadin haka he's sorry to say. Jikin Shu'aibu ba kwari, ya gyada masa kai, yace ayi duk abin daya dace ayi kawai, shi dai fatansa, Ubangiji ya tashi kafadun sa.

Sheikh Muhammad Nuraddeen duk sun zo. Nan Shu'aibu yaje wajan sa ya zauna jikinsa gaba daya babu laka, idanun sa yayi jajir. Zaiyi magana, yai masa alamun yai shuru. Ya saka aka kawo ruwa, ya basa yasha. Sannan ya hau yi masa nasiha da nuna masa ciwo da mutuwa da lafiya duk na Allah ne. Ya fawwalawa ubangiji komai, insha Allahu zai tashi.

Akazo aka shiga da Sheikh Al-Rashid theatre.

Shu'aibu ya cigaba da jinyar sa har sati biyu sannan Allah ya saka ya farka. Akai ta zuwa dubiya. Shu'aibu kuwa Farin cikin sa baya boyuwa na Tashin Sheikh.

Bayan an sallamosa. Shu'aibu yace ya koma gidansa da zama, shima bai musa ba suka koma can.

A lokacin Fateema nada cikinta almost 4-5 months.

Bayan wata uku, a lokacinne rana tsaka ciwon Sheikh Al-Rasheed ya tashi. Kafin sun karasa asibiti kuma ya amsa kiran mahaliccinsa.

Shu'aibu yayi kuka sosai, raunin sa ya fito, bai taba tsammanin zai rasasa a lokacin ba. Dan ya zame masa kamar komai nasa, yana kallansa a matsayin dangin sa.

Bayan wata guda, fateema ta haifo danta namiji, ina Malam Shu'aibu ya mayar da sunan Sheikh Al-Rashid.

Tun bayan mutuwar sheikh ya zama hankalin Shu'aibu yayi gida hakan ya saka yaron ko shekara guda bai rufa ba, yace zaije ganin dangin sa. Fateema tace zata bisa. Sukai sallama da abokan arziki.

Sheikh Muhammad Nuraddeen, shi ya karfafa masa gwiwa akan yaje gida, dan tunda akayi rasuwar sai ya zamo wani iri, yana ganin in yaje kafin ya dawo abin mutiwar ya bar jikinsa.

Shu'aibu ya bar harkokinsa gaba daya a hannun sirikinsa sannan ya kama hanya da iyalansa sannan ya nufi mahaifarsa.

    __________________________________________

   Bayan zuwan Yusuf Egypt ne, Rasheed ya dawo daga Canada, inda yake karatunsa.

Rasheed gaba daya kamanninsa na mayaifiyarsane, daka gansa zakaga cikakken balarabe. Ga hutun da ya shiga jikinsa. Yacca Khadija ta iya fillanci shi bai iya ba, hakan kuma bazai rasa na nasaba da cewan bai cika zama da iyayensa ba.

Yana da saukin kai ga wanda suke zauna tare kan fahimce shi. Bashi da shiga shirgin mutane.

Jinin sa yazo daya da Yusuf. Ko bayan zuwansa da ake shawarar ina Yusuf zaije yaci gaba da karatu, shi ya zaba masa.

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now