12_ Holiday

9 3 0
                                    


🖤🤍CRAVES🤍🖤
By_Nanatoou
Wattpad_@nanatoou





            Elegant online writer's

 





              12_Holiday




Muna landing a kano, i felt home. Gida na dabanne. Mommace tazo tarar mu. Yacca take murmushi kai kasan cewa, ba karamin murnan dawowar mu take yi ba.

Tun a mota kuwa ni da Munaya mun saka ta tsakiya, mun danne ta wai mun gaji. Fauzy kuwa cewa momma take ta dena barin mu wlh tunda mu har yunzu banu san mun girma ba.

Samha kuwa, tun a airport muka rabu da ita, ba hanyarmu daya ba, tace driver ya tawo daukan ga.

Gida muka fara sauke Fauzy. Bamu shiga ba, mukace sai wataran. Driver ya juya muka dau hanyar gida.

Anan parking na fito, ina ta zabga murmushi tare da fadin, "Sweet home".

Momma tayi dariya, ganin yacca mukayi, wai muna perceiving kanshin gidan mu, muna murmushi muna kalle compound din mu.

Sannan mukai cikin gidan. Abu na farko da mukayi shine yin bangaren tsofaffincan.

Munaya ta rike hannuna tana radamin cewa, " bara muje mu rugurguza su"

"I'm right here saba muku zanyi..."

Muka juya muka kalli momma muna dariya kasa kasa. Momma ta wullo mana warning glance, mu shiga taitayin mu.

Daga haka mukayi bangaren su muga rabin ruhin namu ya suke.

Kamar yacca mukayi tsammani mun same su, a sittingroom din  Alhajin Allah.

Yana zaune da fararen kayansa kal, sai daukan ido suke. Gefen sa kuma fruits ne an yanka masa, da alamun ci yake.

"To, me wuri ya dawo me tabarma ya nade sa" Muka fada muna daga kai, wanda yai daidai da juyowar tsofaffin biyu a tare, sun sakar mana murmushi na basu zace mu ba a wannan lokacin ba.

"Su waye wayan nake gani ne..." Tsohuwa me ran karfe ta fada, fuskarta dauke da murmushi.

"Mu ne dai ya san ranki..." Cewar munaya

"Fari tas..." Ta fada G dinmu kenan.

Adedai nan muka karasa. Muka zauna.

"Ja'irai shine ko ku sanar dani zaku zo yau, na san me zan muku.. Na tanadar muku wani abun"

Mukai dariya kafin mu murkusheta. Ta rungume mu. Tayi pecking din mu gaba daya a duka cheeks din mu.

Na dago ina mirmushi tare da fadin, "G... I missed u"

"I missed u too..." Ta fada tana jan kunci na. Sannan taima Munaya. Nai saurin tashi na zibe a gaban Tsohon mu. Sai mirmushi yake. Na dan bata fuska ina fadin, "Ni.. Allah... Allah..."

"To rigimammiya kin dawo zaki fara ko??" Ya tambaye ni, sannan yai kasa da murya yaci gaba da fadin, "ki sha kurumin ki, sai ta tashi zamu saka labule" yana nufin G.

Nai dan murmushi, sannan na rungume sa, mayi pecking kumatunsa.

Munaya ma, tazo tai masa tana fadin, "bazan iya fushi dai kai ba, ko dan kar ai mana dariya"

Mukai dariya ni da G. Na dauki fork en dana gani a wajan na fara shan fruit din ina lumshe idanu. Munaya ma ta zo ta fara tayani.

Nan suka saka mu a gaba da tambayan ya makaranta. Munaya ta bata fuska yare da fadin, "Baccin da kuka dawo da Egypt anan ya kamata ace, kunyi landing kunga lafiyar mu. Amman sai kukaki..."

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now