11_Suitor

13 4 2
                                    


🖤🤍CRAVES🤍🖤
By_Nanatoou
Wattpad_@nanatoou








            Elegant online writer's

 


                  11_Suitor





Muka cigaba da karatun mu, a gefe guda kuma lokaci na ta tafiya.

Kamar yacca mukayi da Momma, su Mahfouz na samun mid-term break kuwa suka tawo abuja hutu.

Kasancewar ranar da suka zo, munayin yest a makaranta, bamu muka dauko su, a airport ba. Already daman mun hada kayanmu suna booth din motan mu, daga sch kuma, sai wajan momma.

Kusan three mukabar sch. Wasu zasuce har yunzu basu ji muna da kawaye ko daya ba na sch. Well, haka abin yake, ban tunanin har yunzu ko fuskar yan class din mu gaba daya na sani.

Ni da Munaya ko da yaushe mu kadai muke abinmu a tare kuma lokaci daya. Akwai fews among them da muke gaisawa da su, dana rike fuskar su.

Most of yan school din mu suna referring din mu da "Arrogant, Spoiled, daddy's girls." Wannan sune sunayen mu, ko kuma kuji ana Sexy slay queens. Wasu kuma bamu ma san sunayen da suke referring din mu, da su ba.

Mu kam bamu san sunayi ba, mu dai a koda yaushe muna jan girman mu bama san raini. Akwai ranar danaje school ma, ina lattin lectures dina. Zan wuce ta wajan wasu mata, naji suna fadin, "game girman kan nan" dayan kuma tace, "Nan bata yadda ba wai ita yar billionaire"

So, duk irin wayannan maganganun ni dariya ma suke bani, ba tun yunzu ba, tun secondary school wai yar'billonaire, to wana taba tara nace masa mu gidan mu muna da kudi, banda dorawa kan su da suka yi.

I guess most of the girls are jealous yacca muke catching attention din kowa. Musammam ma the hot guys, da su matan are akways casing them, amman kuma the guys are after us. Mu kuma ko a jikin mu, basu ishe mu kallo bama. Wannan yana daya daga cikin abinda ya saka yammatan basa sanmu.

Wacca ma, take da yawan kula maza Samha ce, ni har bansan iyaka samarin da take kulawa ba. Da zata zo ta isheni da na hadu da wani sexy hot, gove ta canza tace ta gano wani wanda yake hotter than the first one, jibi haka ma.

Daga karshe kuwa na nuna mata, gaskiya ta dena min wannan hirar bana so. Hakan ya saka ni banma san sanarin ta ba.

Fauzy kam, she's always interested in love stuffs, shi yasaka tafi kauri wajan kallan bollywood movies. Amman kuma duk wayannan love stories din sai dai tayi sa a baccin ta, dan har yunzu bata samo prince charming din nata. She always that person, da zata koma kefe tana magana akan yacca soyayya take, amman bata ma bawa maza chance din kulata. She's always bossy just like me i guess.

Munaya nayin parking, na fita har da gudu gudu nama. Tun kafin na kara shiga ciki sai ga minal da Mahfouz sun tawo da gudu. Na bude hannuna ina fadin, "Oohhh..., my lovely sweet pie......"

Suka daneni nayi baya zan fadi, thank god yau flat shoe ne a kafata, ba stiletto na saka ba, da nasha kayi.

Ina dariya nace, "easyy guys" . suka sake ni suna dariya, sun kasa magana dan hakin da sukeyi, alamun sunyi tseran gudu.

Suka sakeni, suna yar dariyar su, kuma sukayi bayana da gudu. Na juya ina kallansu ina dariya. Suka dane Munaya, itama tai taga taga zata fadi kasa, sai dakyar ta samu tayi stable.

Bayan ta sake ta sun kama hannun ta, ta fara fadin, "Chab, yarannan kunji nauyin da kuka yi, kuna cinye wa Momma abinci ko?'

Suka dan bata fuska, suna fadin, "Haba Adda...." Sukayi rau da ido.

MURADI KO SAN ZUCIYA (craves)Where stories live. Discover now