Haji Bukar na zaune suna cin abincin dare da mai dakin sa ya dauko maganar su da Haji Modu. "Aikam kinga Haji Modu ya same ni yau a office da wata shawara me kyau". Sauraron sa Falmata tayi har ya gama zayyano yadda suka yi da Haji Modu bata katse shi ba. Har sai da ya gama tukun tayi magana."Toh shawara tayi bazan ce bata yi ba tunda kaga auro ni kayi naga kuna abota, kun dade tare dan haka maganar hada zuri'a shawara ce me kyau amma a gani na ayi magana da yaro tukun aji daga gareshi mu tabbatar bayi da maganar aure da wata. Kasan yaran nan, yana iya yiwuwa yina da wadda yike so dan haka kada mu masa shisshigi. Muji daga gare shi tukun". Sosai Haji Bukar yayi na'am da shawarar matarshi. A kullum shisa yike son zuwa gareta da duk wata matsalar shi dan ya san bazata bashi shawarar da bata dace ba. Cigaba suka yi da hirar su suna cin abinci daga kwano daya. Bayan sun gama cin abincin yan aiki suka kwashe kayan su kuma suka cigaba da hirar su. Suna zaune suna hirar d'an nasu ya shigo da sallama, dawowar shi kenan daga site inda yike dan zuwa aiki.
"Abba na, an dawo" Falmata ta fadi tana washe baki. "Wushe".
Durqusawa yayi ya gaida iyayen nasa duka suka ansa mahaifin sa ya qara da "Nda kida?". Yana tambayar shi ya aiki a harshen su na kanuri. A muryar shi qasa qasa ya ansa da aiki lafia lau.
"Ka shiga ka watsa ruwa ka ci abinci ka huta kazo muna da magana da kai". Da toh ya ansa su kan ya miqe ya wuce zuwa dakinsa. Nan da nan kanwar sa Hansatu ta biyo shi da abincin shi har zuwa dakinshi a boy's quarters din qatoton gidansu. Sai da yayi wanka yayi sallan nafila tukun ya zauna cin abincin gefe kuma ga flask din shayi wanda kullum sai ya sha kan ya kwanta barci an ije masa. Sai da ya gama cin abinci har ma ya dan huta tukun ya tashi ya koma parlorn mahaifin su dan jin waca magana iyayen nashi zasu masa. Ba wata boye boye Haji Bukar ya tambayi dan nasa koh da wadda yike so, shikuma ya shaida musu cewar babu.
"Toh dama dai maganar ita ce muna ganin tunda ka gama karatu har ka dawo kana bautar qasa kuma ana kokarin saman maka aiki muna so kayi aure, na dau alkawarin zan dinga tallafa maka har zuwa sanda zaka sama abun yi ka cigaba da kula da iyalin ka". Kasancewar shi mutum me tsananin miskilanci ya sa be ce musu komi ba face toh da yace, koh musawa be yi ba duk da koh kadan shi a lokacin bayi da ra'ayin yin auran koh zance ma shi baya zuwa wurin kowa.
"Yawwa kuma akwai yarinya yar wurin aboki na Haji Modu, kana iya tuna shi? Gidan shi na nan jiddari Polo da ina zuwa da kai".
"Ehh na tuna shi". Ya fadi muryar shi a sanyaye.
"Madallah, akwai yar wurinshi Aishatu. Muna son hada ku da ita". Again toh kawai yace ma iyayensa "Dan haka in ka sama lokaci koh zuwa ran jumu'ah ne tunda naga ranar ana tashi da wuri sai kaje ku gana da juna, in ta maka sai a fara maganar aure koh?". Toh kawai ya kuma fadi Abban shi da Umma duka suka hada baki wurin sa masa albarka kan Abba yace dama shikenan kiran yana iya tafia. Sai da safe ya musu ya miqe ya wuce. Koh kadan maganar bata dame shi ba bare har ta tsaya masa a rai tunda har Abba ya bashi zabi, yaje yaga yarinya sai in tayi masa za a fara maganar aure dan haka da ya yi jayayya da iyayensa yana ganin zai fi ranar jumu'ah din yaje gidan ya ganta in ya dawo yace bata yi masa ba a kashe zancen, shikenan ba wanda zai ce be yi biyayya ba.
Ibrahim Bukar Baba-Ganah matashi ne dan shekara ashirin da tara da haihuwa, dogo ne irin tsayin yan Borno kuma shi ba fari bane amma kuma baza a kirashi da baqi ba. Namiji ne me kyau iya gwargwado ga kuma kwarjini da farinjini da Allah yayi masa wurin mutane. Mutum ne shi mara surutu, dan miskili ne baya shiga harkar kowa baya kuma cika so a shiga tasa harkar dan koh yan uwan sa da suka futo ciki daya baya cika son suna yawan shiga sabgogin sa bare kuma wani. Yana da shekaru Sha takwas Abban shi ya biya masa kudi ya tafi qasar Canada dan karanta Architecture, can yayi shekaru goma sha daya na rayuwar sa ya sama degree and Master's degree in Architecture har ya dan yi aiki temporarily kan ya dawo gida inda a yanzu yike yin bautar qasan shi. Shine d'a na fari wurin Haji Bukar Baba-Ganah tare da matarshi Hajja Falmata, yana da qanni shidda mata uku maza uku wanda duk mace daya ta haife su dan bayan Falmata Haji Bukar be qara aure ba, Zanna shi ke bin Ibrahim sai Halimatu wadda ita ta riga tayi auranta tana zaune garin Lagos tare da mijinta da yar su daya, daga Halimatu sai Hamidu wanda daga shi kuma sai Hansatu daga ita sai qaninta Auwal sai autar su Safiyya. Ibrahim yana da kamun kai da kuma hankali, yana da features inda duk wata macen kwarai take so a cikin mijin aure.
YOU ARE READING
Lawh-Al-Mahfouz
General FictionIna hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kow...