Ibrahim har ya isa gida tunanin Hadiza kawai yike. In ya tuno da murmushin ta me tsananin kyau sai ya lumshe idanu wani dadi na ziyartar zuciyar sa. Yana isa gida dakin mahaifiyar sa ya wuce direct dan bata labarin Hadiza dan dama duk duniya Ibrahim bayi da abokin shawarar da ya wuce Umman sa, wanj shaquwa na tsanani ne tsakanin su."A gaskiya ta kwanta mun a rai sosai Umma. Kin gan ta kuwa gashi zuwan da nike na lura akwai nutsuwa Umma". Ya fadi Hajja Falmata tana fadin iyeee su Ibrahim koh kunya babu "Dan Allah nidai ki fadawa Abba ban so a ja maganar auran mu, in so samu ne ayi nan ba da dadewa ba.".
"Toh sarkin rashin kunya, ai da ka same shi da kanka". Ummah ta fadi tana dariya yace mata ai shi in yayi maganar Abba zai ce be da kunya. "To kana da shi din ne? Ta tambaya tana hararar sa playfully "Har kun gama samun fahimtar juna?".
"Ai wallahi Ummah yarinyar ni ta gama yi mun, koh gobe kuka ce in aure ta a shirye nike". Pillow Ammah ta daga ta jefawa Ibrahim tana fadin "Abba Ganah tashi ka fice mun daga daki da wannan rashin kunyar naka".
Ita dai Hadiza gaba daya daren ranar ta rasa samun sukuni ta kuma rasa gane yadda take ji a cikin zuciyar ta. Shi dai wannan Ibrahim din bazata ce ya kwanta mata a rai tana son shi ba, haka kuma bazata ce be mata ba bata son shi. Bata san me taji akan shi ba dan haka kawai tayi making up mind dinta akan samun lokaci tayi salatul Istikhara dan neman guide din Allah akan al'amarin. Cike da farin ciki ta kwana ranar, ta dade bata zauna tayi having discussion da mutum wanda ya zauna ya saurare ta ya nuna damuwar sa akan lamarin ta, yike son jin opinion dinta on so many things ba sai yau da Ibrahim ya zo.
Safiyar washe gari da duka Yaburra ta tashi Hadiza. Duk takaicin Ibrahim ya zo gun ta, aiki ranar aka dinga kirkiro mata da shi, tana yi ana bin ta da zagi da duka. "Baqar mayya kawaii. Na dade da sanin hassada kike bi na da yarana da shi. Daga yaro ya fara zuwa gun Shatu kin je kin qulla wata muguntar ke da shegun dangin ubanki da ke mani hassada". Yaburra ta dinga jaraba, ta inda take shiga ba ta nan take futowa ba.
"Wallahi duk kun yi kadan. Sai inda karfi na ya qare kan auran nan. In Shatu bata aure shi ba kema bazaki aure shi ba. Shegiya me idanun mujiya".
Shikam Ibrahim kamar yadda yayi alkawari ranar jumu'ah ya zo gun Hadiza. Daga nan ya cigaba da zuwa, da ya lura tana son karatu sosai in zai zo sai ya dinga kawo mata takardu tana karanta. Hakan ya kuma sa shi kafuwa a zuciyar Hadiza. Alkhairi kam baa cewa komi, dan kusan kullum in ya zo sai ya zo ma Hadiza da siyayya tunda yaga in ya bata kudi bata ansa. Sai dai duk abubuwan da yike siyowa Yaburra da yaranta ke kwacewa. Dama da ya zo ya tafi tana jiran bakin Hadiza a bakin qofa ta kwace abunda ya kawo mata. Kwata kwata cikin watanni biyu sun sama fahimtar juna sosai, sunyi wata iriyar shaquwa. Ibrahim din kuma yana lura da abubuwan da ke faruwa gidan Haji Modu, yana lura da irin zaman da Hadiza da Fusam suke yi da matar ubansu da yaranta. Har da ya fara lura siyayyan da yikewa Hadiza kwacewa suke sai ya daina ya fara bata kudi ne. Tun bata karba har da ya shawo kan ta ta fara karba kuma da yike ita din me wayo ce, da kudin take biya musu buqatun su sannan kuma take tattalin sauran canjin koh da wani abu ya taso musu.
Wahalar da su Hadiza ke ci gidan ubansu ya sa Ibrahim gaba daya yaji yana son a hanzarta auransu dan ya raba ta da rayuwar qunci da bauta. Dan wasu lokuta in yaje gun ta zance da hawaye take futowa koh ta futo idanu a kumbure alamun ta sha kuka.
Wata ranar asabar bayan ya dawo daga wurin Hadiza ya shiga ya same iyayenshi zaune tare. Gaishe su yayi kan ya fara gabatar musu da qudurin sa. "Zuwa yanzu mun sama fahimtar juna iya gwargwado dan haka nike ganin ya kamata Abba in ba zai zama damuwa a gare ku ba, ku sama lokaci kuje ku hadu da magabatan ta a fara zancen auranmu". Ibrahim ya cira kunyar shi ya ma iyayenshi bayani, Umman shi nata gyara masa zance dan dama ya kasa daure ya kai mata qorafi akan yadda matar Haji Modu ke treating din su Hadiza sannan itama tunda tana hulda da gidan tana ganin alamu dama kuma tana jin qishin-qishin din maganar a bakin mutane.
YOU ARE READING
Lawh-Al-Mahfouz
General FictionIna hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kow...