A kwana a tashi ba wuya, Hadiza da Ibrahim sunyi shekara biyu da aure. Rayuwar auran su abun kwatance ne wurin wasu sabida irin so da fahimtar juna da ke tsakanin su. Zuwa lokacin mutane sun fara ma Hadiza tsegumi akan maganar haihuwa amma koh kadan Ibrahim be taba nuna mata damuwa akan rashin samun cikin ta ba. Wasu mutane su kan ce wai qilan tana tazarar haihuwa ne sabida karatun da take, sai kaji ana fadin 'wai ita baturiya bata so ta hada haihuwa da karatu' alhalin kuma ba hakan bane, haihuwan ne kawai be zo ba. Duk Hadiza bata bari wannan ya dame ta ba tana ta karatun ta. Ta kan yi two weeks a school kan ta dawo gidanta a kaduna tayi weekend sannan ta koma school. Shima Ibrahim a duk sanda ya sama sarari daga aiki ya kan kai mata ziyara a Zaria, abun sha'awa matuqa da su. A zuwa lokacin Hadiza ta kammala 100l dinta ta fara 200l, tana da kawaye iya gwargwado wanda take mutunci da su dan ita dama tun asalin ta ba me kwashe kwashe bace. Ibrahim kuwa ya fara bunqasa matuka dan kwangilar da ya samu wanda yayi silar sa dawowa kaduna an sama alkhairi matuqa a ciki, har ya siya fili ya fara musu nasu ginin, sannan ya je qasa me tsarki ya sauke faralli sannan ya yiwa matarsa alkawarin cewar zuwa zagayowar shekara da yardan Allah itama zai kai ta qasa me tsarki.
Fusam a nata gefen ta gama karatun secondary dinta kuma Ibrahim yayi iya kokarin sa na riqe alkawarin da ya daukarwa Hadiza dan sosai Fusam ta sama sassauci. Kan ta gama secondary a kullum in ta taso makaranta sai taje gidansu a nan zata ci abinci tayi nak har Umma tayi mata yan kunshe kunshe kan ta wuce gida. Nan da nan ta zama yar gida, yar gaban goshin Umma. A kai a kai kuma Ibrahim din zai aikawa yan uwansa kudi kyauta zai hada har da ita dan haka fannin abinci da abubuwan buqata Fusam ta sama wadata sosai. Sai dai rayuwar gidan ubanta har zuwa wannan lokacin ba abunda ya sanja, dan ma dai Fusam din me baki ce ba shuru shuru ba kamar Hadiza, wani abun nan da nan take kwatar ma kan ta 'yan ci.
Kamar yadda ya faru da Hadiza haka itama ya same ta, Yaburra ta hana a biya mata kudin furthering education dan haka sai zaman gida tana cin bauta sai Islamia da take zuwa. A hanyar ta na dawowa daga Islamia wataran Allah ya hada ta da wani bawan Allah, Abdulra'uf wanda ya nuna yana son ta. Abdulra'uf ya kasance ya futo gidan rufin asiri dan mahaifin sa yana riqe da babban muqami a gwamnatin jahar Borno. Soyayya ne aka fara sosai tsakanin Fusam da Abdulra'uf har ya nuna mata yana son ya zo gida ya gabatar da kansa a wurin mahaifinta dan son ta yike da aure. Farkon wadda Fusam ta fara shawara da ita ne yar uwar ta Hadiza. Dama duk sanda take son waya da ita gidansu Ibrahim take tafia dan suna da telephone, itama kuma Hadizan tana da shi a can gidanta a kaduna kuma Fusam ta san weekends inda Hadiza ke kasancewa a gidanta ba makaranta ba. Dan haka ranar cike da murna ta je gidan dan har Umma sai da ta lura Fusam na cikin farin ciki ranar. Sun jima suna hira, Hadiza nata ba yar uwar ta labarin garin kaduna da kuma rayuwar jami'ah. Sai da suka kusa gama wayan tukunna Fusam ta fara fadiwa Hadiza maganar da suka yi da Abdulra'uf dan dama Hadiza ta riga da ta san da maganar Abdulra'uf din. Hamdala Hadiza tayi ta nuna farin cikin ta da hakan kan ta fara ba Fusam shawarwari.
'Amma kada ki sama Baba kai tsaye kada hakan ya zama miki. Ki fara magana da Yaburra tukunna. Kin san ba wuya ta kama mutum da laifi' Hadiza ta fadi Fusam tace haka ne. Sai da suka gama tsara komi tukunna suka yi sallama Fusam ta ba Hadiza assurance cewar zuwa nan da sati biyu da Hadiza zata kuma dawowa gida weekend Fusam zata kira ta da update.
Sosai Hadiza ta dinga murna ta zauna ta dinga tunanin fara yan shirye shiryen ta da yadda zata yi tattalin kudinta dan tayi ma Fusam hidima. Sarai ta san halin Yaburra, ta san qarshe a kuma yin yadda aka yi a lokacin nata auran aka so a ji kunya in ba dan Allah ya sa surukanta mutane ne masu ganewa ba. Ibrahim yana dawowa daga site ranar Hadiza ta tare shi da labarin shima yayi farin ciki ya taya su murna sannan yayi addu'an fatan alkhairi.
Kamar yadda suka tsara haka Fusam tayi. Wata ran alhamis da yamma da ta lura da Yaburra na cikin nishadi sai ta tare ta da maganar. Yaburra dama tana lura da zuwan Abdulra'uf din wurin Fusam amma bata yi tunanin maganar yayi nisa ba haka. 'Shine wani me zuwa da koriyar marsandi?' Ta tambaya tana taunar goro Fusam ta ansa ta da ehh.
'Ah tirqashi!' Ta fadi Fusam ta rasa gane me take nufi da hakan 'Toh ranar asabar kice masa ya zo nan gida ya gaishe ni. Sai na gansa na gamsu da tarbiyyar sa kan na kai maganar gaban Babanku'. Godia Fusam ta mata ta miqe. Kashe gari da Abdul ya zo zance ta sanar da shi saqon Yaburra aikuwa ranar asabar bayan la'asar sai ga shi niqi niqi da ledoji ya yo uban sayyaya wai shi a dole zai zo ganin suruka. Sosai Yaburra ta gama qare masa kallo tana ta washe haqoran ta da goro ya gama maida su ja, ta anshi ledojin siyayya tana godia ta miqawa Mairam ta wuce da shi uwar dakan ta. Tsaf ta qare masa kallo taga shigar da yayi na alfarma, fatar sa sai walkiya take ga wata hadaddiyar shaddah da ya saka yana ta kamshi. Nan da nan ta gama shawara da zuciyar ta cewar kuskuran da tayi da Hadiza bazata bari a maimaita ba. 'Baza su taru duka su tafi gidan hutu ba! Ga tawa a gida ta zaman mun kaya' ta fadi a zuci amma a fili sai washe baki take tana ta fara'a.
'Ke yar matsiyaciya ina ke ina dan gidan Alhaji Maidugu? Kawai dan neman magana?' Yaburra ta fara kwararowa Fusam zagi kala kala wanda ta saba da jin su, tun daga nan Fusam ta san magana ta dau hanyar baci hakan kuwa ya faru dan maganar koh gaban Baba be je ba, shi Abdul da kan sa ya dauke qafar sa daga zuwa wurin Fusam, Yaburra ta yi aiken qawayenta zuwa ga Hajja Uwani mahaifiyar sa an gama bata Fusam a wurinta, a qaryar su har sharrin kwana da maza da cire ciki suka ma Fusam dan haka Hajja Uwani ta ma yaronta iyaka da Fusam. Sosai hakan ya ma Fusam ciwo dan ta saka rai da Abdul, ya kwanta mata a rai kuma zuwa lokacin a matse take da tayi auren ta bar gidan ubanta. Ta sha kukanta, ranar da taje gidan Umma ta sha kuka su Umman suka dinga bata baki, Hadiza ma tayi kokarin ta wurin ganin ta kwantar mata da hankali. Haka ta haqura ta bar ma Allah komi.
Da yike shi Allah ba azzalumin bawan sa bane nan da nan wani saurayin ya kuma futowa Fusam. Da shike Allah yayi su da matuqar kyau, ga diri ga kuma natsuwa duk namiji da ya gan su dole yaje sun kwanta masa a rai. Alhaji Kamal sai ya kasance ya dama Abdulra'uf ya shanye a arziki dan babban dan kasuwa ne shi yana da matar sa guda daya da yara hudu. Yana ganin Fusam yace ba wata wata shi auranta zai yi baya ma buqatar komi daga gare ta iyakar yardan ta da kuma na magabatan ta amma duk wani abu da ya kama daga kayan daki har na kitchen da hidimar biki duk ya dauka zai yi shi dai a kawo masa matar sa. Wannan karon Fusam bata ma bari Yaburra ta ji da maganar ba, Alhaji Kamal ta ce ma ya sama Haji Modu kai tsaye a rumfarsa da yike zama a kasuwa. Hakan kuwa aka yi, Haji Modu sosai yayi na'am da Alhaji Kamal amma da yike baya taba iya daukar mataki ba tare da ya sanar da Yaburra ba ya sa ya kasa basa takamamman ansa yace masa sai yaje gida yayi shawara tukunna. Yana zuwa kuwa yayi shawara da Yaburra tace sam kada ya yarda tunda ta gano Alhaji Kamal me arziki ne.
'Haji na Fusam yarinya qarama ina ita ina zama da kishiya. Haba! Yarinya qarama taje a daga mata hankali a sa mata ciwon zuciya' ta fadi cikin kissa harda yar shesshekar hawayen qarya 'Haji na sai kace ka gaji da ita kake neman aura mata me mata'.
'Toh ai Hajjaju ita ta aiko shi. Ina ganin sun sasanta'.
'In ba kai ba megida me Fusam ta sani? Yarinya qarama yar shekara ashirin me ta sani? Amma mu iyayen ta baza mu sa mata ido muna kallo ta kai kanta ga halaka ba koh ba haka ba. Ka same shi ka gaya masa ba yanzu ka shirya mata aure ba yayi haquri'. Yadda Yaburra ta so haka aka yi. Takaici ya ishi Fusam ta rasa wani irin jaraba ne wannan. Tsananin ciwon da abun ya mata ranar har daki ta sama Yaburra tana kuka take fadin 'A rayuwa me muka miki? Menene ya sa kika tsana ganin farin cikin mu? Baki kaunar zaman mu a gidan mahaifin mu kamar mun tare miki wuri toh ki bari muyi aure mana mu tafi mu bar ki da yaranki ku cinye gidan'.
Fusam bata ankara ba Yaburra ta kwashe ta da mari. Kan ka ce me ta rufe ta da duka ta mata dukan tsiya tana fadin 'Ni asararriya ce? Ance maki rako mata nayi duniya in sake maimaita kuskuren da nayi da waccan shegiyar akanki. Ku taru ku tafi gidan hutu? Ina!' Ta fadi tana tofo dussan goro a jikin Fusam.
'Ba zai taba yiwuwa ba! Hankali na bazai taba kwanciya ba. Na fi so na ganku a wulakance a kaskance dan haka muddin bazaki kawo mun matsiyaci dan uwan ki gidan nan ba a matsayi wanda zaki aura. So dari kina kawo maza wallahi ina bata maganar. Yar iska kawai' ta tsallake Fusam ta wuce dakin ta. Gyale ta dauko ta jefa a kafada ta fice fuuuuu zuwa gidan wata figaggiyar qawar ta take kwashe mata yadda suka yi da Fusam sai da ta gama bata labari tas tukunna qawarta ta gabatar mata da shawara cewar yarinya fa tana da kyau dan haka masu arziki zasu ta futo mata.
'Muddin baki dau mataki da kan ki ba' qawar ta fadi mata.
Kwana Yaburra tayi ranar tana juye juye kan gado tana ta juya maganar qawar ta a kwakwalar ta har sai da ta sama mafita tukunna barci ya iya kwashe ta. Kan a kai qarshen wannan sati kuwa har an fara shirin maganar auran Fusam dan Yaburra ta riga ta yo mata miji bayan dukan tsiya da ta sa Baba ya mata sabida sharrin da Yaburran ta qulla mata.
Allah Allah Fusam ta dinga yi sati biyu su cika dan ta sama yin waya da Hadiza ta kwashe mata komi. Ranar kuwa Hadiza na daga waya maganar farko da Fusam ta fara fadi mata shine 'Hadiza qarshen wata Baba zai mun aure'. Hamdala Hadiza ta fara dan a tunanin ta komi ya tafi daidai da Alhaji Kamal an daidaita komi. Cikin hawaye Fusam tace mata 'Ki daina hamdala Hadiza. Baakura Baba zai aura mun'. Ras Hadiza taji gabanta ya fadi.
Salati ta saki kan tace 'Baakura kuma! Me ya faru?'. Nan Fusam ta fara kwashewa Hadiza komi da ya faru. Tun daga yadda Yaburra ta kuma bata maganar auranta da Alhaji Kamal har zuwa sharrin da ta mata na cewar ta sha kamata ita da Baakura suna abubuwan da basu kamata ba. Tana gudun kan su yi aika aika su ja musu abun surutu a al'umma gara ayi musu aure. Ranar ran Baba matuqa ya baci yayi ma Fusam shegen duka, irin wanda be taba mata koh wani yaron sa ba. Sannan ya ci ma Baakura mutunci, dama yana bin sa kasuwa yana masa yaron shago yace baya son ya qara ganinsa a runfar shi.
'Daga qarshe kuma ya sa ranar auran mu' Fusam ta fadi tana kuka kan ta qara da 'Me muka ma Yaburra? Me ya sa ta tsane mu haka ne? Wannan wana irin rayuwa ne Hadiza? Yaushe duk wannan wahalan zai qare ne?'.End Of Chapter🎊🎉
Toh! Ga babban magana?
At this point can you guess where the story is heading???
YOU ARE READING
Lawh-Al-Mahfouz
General FictionIna hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kow...