Kashe gari Haji Bukar ya iske Baba a kasuwa da maganar da yayi da Ibrahim. "Magana dai tana nan sai dai an dan sama aqasi". Haji Bukar ya fara."Toooo... Aqasin mene fa abokina". Haji Modu ya tambaya.
"Yaro dai da yazo gida yaga wata yar wajen naka yace hankalinsa ya fi kwanciya da ita". Dariya duka suka kwashe da shi.
"Toh ai duk bata baci ba". Haji Modu ya fadi "Burin mu dama a qara karfin zumunci. Wannan bazata zama matsala ba ai abokina. Wacca yar nawan kenan ya gani dan ka san wanda suka taso din su uku ne akwai Hadiza akwai kuma kanwar ta Fusam".
"Ita Hadiza yike son a bashi izinin ya qara sanin ta, in an sama fahimtar juna sai mu sha biki".
"Ai wannan ba matsala bane, zan yi magana da iyalina a daren yau in na koma gida koh zuwa gobe in yana da lokaci yana iya zuwa su gaisa a dan fara sanin juna".
"Hakan ma yayi. Dama abunda ya kawo ni kenan, barin sauri na koma office kan mutane su fara zuwa nema na". A haka sukayi sallama da juna Haji Modu yana sai yaji daga Ibrahim din gobe, Haji Bukar yayi assuring abokinsa cewar zai turo sa kuma.
Sosai Ibrahim ya sama kansa da yin farin ciki da mahaifinsa ya kirasa da dare ya masa bayanin yadda sukayi da mahaifin Hadiza. "Gobe da yamma sai ka shirya kaje. Zasu saurari zuwanka". Godiya Ibrahim yayiwa mahaifinsa ya tashi ya wuce zuciyar sa cike fal da farin ciki.
Su kuma can a nasu gefen Yaburra ta daka tsalle sama ta duro tana buga hannu a qasa tana baza ayi haka ba. "Haji na ka taba ganin inda kanwa tayi aure ta bar yayarta. Takan me zai sa Hadiza tayi aure kafin Shatu kuma ma dai wanda asali aka ce yazo gun yayarta. Gaskia idan be son Shatu ina ganin gara an haqura da maganar, Kace musu Hadiza ba a shirya mata aure ba. Ai yarinya ce kwata kwata nawa take. Shekaru sha takwas fa!".
"Koh sati daya ba a yi ba nan kika gama cewa ta haqura da karatu in miji ya futo ayi aure, yanzu kuma kice in koma in ce musu aah bayan na riga na amincewa abokina. In zama mutumin banza a idanunsa? Aah kam Yaburra, yaro zai zo ganin Hadiza gobe in sun fahimci juna muka saka rana ayi musu aure. Ita kuma Shatu in Allah ya kawo rabon ta itama muyi mata auren ta tafi gidanta. Ai ba addini bane yace kanwa bazata iya aure kafin yaya ba kuma in ba naki ba Yaburra kan auran ya taso qilan itama Shatu wani ya futo mata sai a hada su biyu". Ita dai Yaburra duk bata gamsu da wannan bayanin ba, tana ganin ta ya Hadiza zata riga yar ta aure kuma auran ma a gidan hutu. Da me ta fi shatun ta da zai ce ita ya fi so. Hawayen takaici ta goge tace toh shikenan ba wai dan ta gamsu ba sai dan bata da yadda zata yi. Amma ta san dole ta sake komawa Benisheik gun malamin ta dan kamar asirin ta ya fara rage tasiri kan Haji Modu. Ta san dole ayi aiki a qara karkato mata da hankalin sa sannan a rusa wani zance na aure tsakanin Hadiza da Ibrahim Bukar Baba-Ganah. Ba yadda zata bari Hadiza taje aure gidan hutun nan ta bar nata diyar wadda gashi tana neman shiga shekara na ashirin da hudu ba manemi.
Baba da kansa yayi sallama qofar dakin su Hadiza dan mata bayanin komi. Bayan sun ansa ya shiga ya zauna qasa tare da su, Fusam ta taho da sauri ta kwanta kan qafar sa sai a lokacin Baba ya san da zazzabin da take yi. Damuwa sosai suka ga ya shiga, rabon da suka ga Baba ya shiga damuwa akan lamarin su har sun mance haka ya sa su jin dadin, suka fara having hope din cewar koma me Yaburra ta yi wa mahaifin su ya fara warwarewa. Haquri Baba ya ba Fusam yace da safe zai aiko mata da magani in ta sha ba sauki sai taje asibiti. Fusam ta so fadawa Baba abunda Yaburra ta mata amma Hadiza ta dinga mintsilin ta tana mata ido cewar kar ta fadi ta ja musu matsala. Hakan nan ta haqura tayi shuru bata ce masa komi ba. Amma ranar suka kasance cikin farin ciki ganin yadda Baba ya nuna damuwan sa da lamarin su. Dama indai so ne baza suce mahaifin su baya son su ba, aqasin da aka samu shine Haji Modu mutum ne mara zama sosai a gida kullum akan kan hanya neman halalin sa dan kula da iyalin sa sannan kuma mutum ne shi mara maida hankali sosai akan abubuwan da ke faruwa cikin gidan sa. A ganinsa matar sa tana riqe masa yaransa tsakanin ta da Allah, wannan saken da yayi kuma shi ya sa Yaburra ke samun damun musguna musu ga kuma asiri da kowa aka fi yarda da Yaburran tayi masa dan wasu abubuwan da yike yi da wuya ace da yina cikin cikakken hayyacin sa zai aikata. Tun zuwan ta gidan a amarya, Yaburra da ta lura da yadda ya dau son duniya ya dora kan yaranshi, da kuma yadda kullum be da maganar da ya wuci na matar shi da ta rasu, sannan kuma ta lura da cewar ba wai dan yana son ta ya aure ta ba sai dan yana buqatar mace a gidanshi wadda zata riqe masa gida dalilin auranta kenan, hakan ya sa Yaburra ta bazama bin malamai neman asirin da zata mallake Haji Modu da shi ya zama sai yadda ta so zaa yi a gidan.
YOU ARE READING
Lawh-Al-Mahfouz
General FictionIna hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kow...