04: 1996

162 46 13
                                    

Abincin rana tayi ranar da yawan gaske ta kawo kwano babba ta cika ma Ali abinci a ciki. Abincin da ta zuba a kwanon ta san koh ita babba babu yadda za ayi ta iya cinye shi bare kuma Ali dan yaro qarami. Da ya ci abincin ya kai sauran kitchen yace ya qoshi Yaburra ta kirashi ta ce ya dau farantin abincin "Ka wuce ka cinye shi tas! Koh kwayan shinkafa daya bana so na gani a kwanon". Kujera ta samu ta zauna gaban sa tana jira ya cinye abincin.

"Ba ka qoshi koh? Yau zaka qoshi da kyau" ta fadi tana ta jaraba. Zagi iri iri tana ma dan yaron da be san komi ba "Koh amai zaka yi yau sai ka cinye abincin nan. Sannan kayi aman sai ka kwashe ka cinye".

Kuka sosai Ali ke yi yana ta cin abincin har yaji bazai iya turawa ba kuma amma haka ya dinga ci sabida dorinar da Yaburra ke ta zabgar sa da shi in ta ga ya tsaya. Su Hadiza suna gefe suna kallon qanin su suna kuka ba abunda zasu iya masa. Kan abincin da yike ci ya kwaro amai amma Yaburra ba imani haka ta sa Ali ya cinye komi tas, har da aman da yayi ta sa duk ya cinye. Sai da ta tabbatar ba komi a farantin tukun ta miqe ta shige ciki ta bar shi a nan wurin yana kuka. Yan uwansa ne suka matso kusa da shi suna kuka suka daga shi Hadiza ta je ta wanke shi ta sanja masa kaya. Ranar kwana Ali yayi yana amai har da kashi, kan gari ya waye duk ya galabaita ya bata jikin sa da amai. Lafiyayyar duka Yaburra ta kuma masa da safe tana fadin ita bazata ci kashin dan wata ba.

"Sai dai uwar ka ta taso daga kabari ta zo tayi wannan hidimar ba dai ni Yaburra ba". Ta fadi tana dukan shi. Koh da su Hadiza suka dawo makaranta Ali ya riga ya gama galabaita ga ciwo da duka. Ciwon sa ne ya tashi kuma Yaburra ta qi fadiwa mahaifin su sannan ta hanasu fada. Haka Ali yayi last few days din sa a duniya cikin kunci da wahala dan koh sati biyu ba ayi ba Allah ya masa rasuwa, ya bar duniyar ya huta da azaban Yaburra.

Bayan rusuwar Ali rayuwa ta cigaba normal a gidan Haji Modu dan ba a wani jima ba Yaburra ta sama ciki ta haifa diyanta na uku da Haji Modu wato Umar Farouq bayan shi tayi auta Marwan. Kwata kwata auran Yaburra da Haji Modu shekara goma amma irin azaba babu irin wanda Hadiza da Fusam basu gani ba, gashi a gaban mahaifin su sai ta nuna tana matukar son su, gashi dama ta riga ta gama da shi sai yadda tace don haka koh sun kai qarar ta aikin banza ne dan ba mataki zai dauka ba. Yan uwansa ma sun saka baki a cikin al'amarin abun ya gagara har ya kai ga qaninsa Adamu ya so ya anshi yaran su dawo karkashin kulawar shi amma Yaburra tayi tsalle ta zuga Baba kar ya yarda cewar yan uwansa suna nema su raba masa kan yaran sa.

"Wataran kema haka za a zo gidan nan ganin ki" Fusam ta fadi tana dariya dan ta lura da hirar na saka yayar ta kunya, ita kuma Hadiza ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga "Sai Baba ya amince, sai yazo ayi auran ku ki koma can gidanki ki huta". Fusam ta qarashe tana me matuqar murna akan tunanin wataran fa zasu sama maza suyi aure su bar gidan mahaifin su su huta da zagi da wulakanci.

Yar dariya Hadiza tayi kan ta ansa ta "Bana so nayi aure na bar ki Fusam dan na san duka wahalar kanki zai dawo. Na fi son in za muyi aure Allah ya futar mana da maza rana daya muyi aure mu tafi mu huta da wahalar gidan nan". Rungumar junansu sukayi suna fatan Allah ya amshi addu'ar su nan kusa.

Kira Yaburra ta kwalawa Hadiza dan dama dai for no reason kamar ta fi tsanar ta, tace mata taje ta dau hijaab tazo zata aike ta nan maqota kai zubin adashi. "Ban ga ta zama ba dole na dage da adashi kan biki Shatu yazo". Take fadi as tana kirga kudin da zata ba Hadiza. Haka nan for no reason Hadiza ta zo zata wuce aiken da ta sa ta kawai Yaburra ta sa mata qafa ta yi wata mummunar faduwa a qasa.

"Makauniyar banza". Ta fadi tana tsaki dan dama Hadizan ba gani take ba sosai sai da taimakon eye glasses.

Futowar Hadiza tare da Fusam da tace bari ta rakata yayi daidai da futowar baqin parlor zasu wuce. Daga idanun ta da suka ciko da kwalla tayi kawai suka yi ido hudu da babba cikin maza biyun da sukazo wurin Shatu, dauke kai tayi ta ja hannun Fusam suka fice daga zauren da sauri sauri zuwa inda aka aike su, saurin ya sa Hadiza ta qara cin karo ta kusa faduwa. Ibrahim didn't know what propelled him, kawai ya sama kan sa da yin hanzarin kamo ta. Zuqunawa yayi ya daga glasses dinta da suka fadi ya miqa mata. Ansa tayi tana masa wani irin kallo da ke cike da haushi da bacin rai, tana sauke haushin Yaburra a kansa. Ba tare da ta masa godiyan abun da ya mata ba ta ja Fusam suka fice.

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now