10: Ibrahim

137 36 18
                                    

Koh da na dawo gida na sama Hadiza tare da Bibi a kitchen suna kokarin hada dinner. Abincin dare muka ci muka dan zauna muka yi kallo before we decided to call it a night. Bamu nunawa Bibi sabuwar motar da na siya mata ba sai washe gari da safe da ta sauko qasa a shirin ta na zuwa asibiti. Cheerfully ta sauko qasa ta gaishe mu kamar yadda ta saba tana jan mu da wasa. Sai da muka bari ta gama breakfast tukun nace ta zo taga wani abu a waje.

Ihu Bibi tayi ta daka tsalle da taga motar da na siya mata. A guje ta fada jikina tana fadin "Thank you my darling Papa. I love you I love you". Tana sauka daga jikina ta fada jikin Hadiza tana fadin "I love you too mommy. Nagode muku sosai". Hannunta na riqo na danka mata key din motar a hannu cike da murna ta buda motar ta shiga tana duba features din sa.

"Mommy yau zan kai ki yawo". Ta fadi happily tana ta duba cikin motar.

"Ai ban gama yarda da iya tuqin ki ba Bibi. Kada kije kina ma mutane barna fa". Dariya duka muka kan nace "Aah Bibi fa yanzu ta iya mota sosai ba wanda zata buge". Gwalo Bibi tayiwa Hadiza dan nayi picking side dinta. Mun tsaya wurin mun dan taba hira har sai da waya na yayi ringing na duba naga secretary dina ne calling to remind me of a meeting that morning.

"Kash ba na mance ba" na cewa Hadiza "Akwai meeting a government house akan wannan project na bridge dinnan. Gwamna na son ganin construction team din". Ina magana muna koma cikin gida ni da Hadiza dan Bibi bata gama murnar motan ta ba. Abubuwan da nike buqata duka Hadiza ta hada mun ta rako ni har zuwa mota na da su. Sai da na zauna a cikin motar tukunna ta leqo kanta tayi kissing saman kai na.

"I love you" tayi fadi ba tare da sautin muryar ta ya futo ba. Nima na ce mata "I love you more". Ina kissing hannunta kan nace mata ta kula mun da kanta da baby dinmu. Har na fita daga harabar gidan suna waje ita da Bibi standing in each other's arms. Ina ganinsu a haka na gama sanin cewar that image of them standing together was going to linger in my memory all day, it was the highlight of my whole day that day. Ba abunda ya fi mun farincikin su a kaf duniya.

Koh da na isa government house ba a riga an fara meeting dinba. Ga dai mutane an taru masu breakfast suna yi masu taba hira suna yi. Nima hirar na dan taba da yan few people. Ina tsaye ina magana da wani engineer da na sani naji an tabo ni, koh da na juya senator Shehu Musa na gani, mahaifin best friend din Bibi.

Dariya muka yi muna shaking hands nace masa "Kai Senator ka boye abunka gaba daya an daina ganin ka".

"Ah haba dai architect" ya fadi yana shafa tumbin sa "Ka san election ya kusa babu zama. Kullum ana cikin hidima". Fatan alkhairi na yiwa senator Shehu kan muka cigaba da tattaunawa akan abubuwa da dama.

"Yawwa kamun na mance ma ai muna da magana" ya fadi "Akan dan waje na Kamal". Lokaci guda na tattara gaba daya attention dina na maida kan Senator.

"Ka san anyi masa transfer" ansa masa nayi da na sani ai jiya jiyan nan Hadiza take fada mun dan da na dawo da yamma ta fadi mun cewar sunzo gidan. "Madallah. Toh dama ya zo hutu ne kuma sannan yazo mun da wata magana me dadi. Akan diyar wurin ka". Dariya duka muka kwashe da muka sha hannu.

"Ka san ni dama na dade ina son hadin zuri'a tsakanin mu. Ban so yiwa yaran shisshigi bane cikin lamuran su". Senator ya fadi.

"Ashe kuma already suna da nasu shirin". Dariya muka kuma yi kan Senator Shehu yace "Wannan haka yike".

"Toh ai wannan abu ne mai sauki. Ina ganin zan zauna da Bibi da kuma mahaifiyar ta tukunna naji nata take din on the matter daga nan ina ganin kawai sai muyi taking next step".

"Madallah, madallah" ya fadi kan ya qara da "Da zaran kuna gama shawara sai ka bamu go-ahead mu zo ayi formal introduction koh. Tunda abun na gida ne ba sai an wani bata lokaci ba". Na'am nayi da shawarar Senator kuma na tabbatar masa da cikin wannan sati zan nime shi in Allah ya so. Bamu jima ba da yin haka muka yi sallama da juna senator ya wuce nasa meeting din nikuma na cigaba da socializing da sauran mutane muna jiran time inda gwamna zai iso a fara namu meeting din.

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now