Mairam ce ta shigo gida tana kuka bayan sun dawo daga makaranta. Hadiza na tsakar gida tana cin wankin Hamza da ya tara mata, ranar tun safe take wanki dan sai da tayi na Yaburra ta gama kan ta kama na Shatu. Tana gab da gama ma Shatu nata sai ga Hamza ya shigo ya wuce daki ya watso mata nasa wankin. Haka kuma in ta gama zata kwashe kayan duk ta goge su tas sannan ta kai tayiwa kowa arranging a drawer dinsu. Tana wankin ma kuma ba wai an bar ta bane, kira, aike, girki duk tana yi kuma ba halin tace ta gaji. Rabon ta da abinci kuwa tun safe dan bata isa ta ci abinci ba bata gama aiki ba."Me ya faru da ita?" Hadiza ta tambaya Fusam da ta shigo gidan a few minutes after.
"Wane?". Ta tambaya. Hadiza tace mata taga Mairam ta shigo gida da hawaye "Gaskia ban sani ba. Qilan laifi tayi a aji koh kuma ta sake rigima da wasu, kinsan Mairam da tsokana". Daga nan cigaba suka yi da hirar su, Fusam zata sa hannu a wanki Hadiza tace mata aah ta fara cin abinci tukunna.
Tsakar gidan Yaburra ta futo tare da Mairam da har zuwa lokacin bata daina kuka ba. Wani irin kallon tsana ta watsowa su Hadiza kan tace ma Fusam "Dan baqin hali kina kallo ana dukar mun diyata kika tsaya kina kallo koh, bazaki iya hanawa ba. Baqar makira". Duka Hadiza da Fusam suka kalle ta fuskokin su cike da confusion sai maganganu take ta watso musu ta inda take shiga ba nan take futa ba. Zagi ba irin wanda bata ma Fusam ba tana nuna mata bayan Mairam da aka tsaga shi da bulala. Ta nema fadan seniors dinsu bayan an tashi suka tare ta suka sama tsumagiya suka mata dukan tsiya. Fusam da bata san anyi haka ba laifin ya dawo kan ta. Haquri su biyun su suka shiga ba Yaburra wadda bata koh tanka su ba ta ja hannun diyarta suka koma cikin daki tana rarrashin ta. Shatu kam kan ta juya ta koma ciki sai da ta wuce inda Fusam ta ije farantin abincin da aka ije musu ta kabar da shi abincin duk ya watse a qasa. Harara ta galla musu ta ja tsaki ta wuce ciki. Hawaye Hadiza ta fara, ita kam Fusam da yike me zuciya ce da wani irin haushi ya dibe ta miqewa tayi tayi kan Shatu ta ja ta tana neman kai mata duka tana tambayar ta takan me zata kabar masu da abinci. Hadiza ce tayi saurin isa gun yar uwar ta tana kokarin jan ta daga jikin Shatu wadda har an kai ta qasa dan dama bakin ne kawai amma ba qarfin fada. Hayaniyar ya kuma futar da Yaburra wadda ta finciko Fusam daga jikin Shatu ta watsar da ita gefe. Ba tare da tace musu komi ba ta saka Shatu a gaba suka koma cikin daki ta yi banging qofar ta.
"Da kin rabu da ita Fusam" Hadiza ta fadi tana kuka "Da kin rabu da ita. Yanzu shikenan mun rasa na rana mun rasa na dare". Ta fadi hawayen ta na qaruwa.
"How long zamu bar su suna mana haka Hadiza. Na gaji! Mu da gidan uban mu? Masu aikin wani gida sun fi mu daraja fa. Wallahi na gaji guduwa zanyi". Jawo ta zuwa jikinta Hadiza tayi tana fadin ba zancen guduwa. Rarrashin juna suka dinga yi har sai da hawayen suka tsaya tukun suka qarasa wankin tare suka gama suka koma daki.
Gab da aikin yamma Yaburra ta futo ta kwalawa Fusam kira. Tana zuwa ta miqa mata kudi tace taje shago ta siyo mata jakar gishiri guda da reza sabuwa. Ba musu ta anshi kudin ta tafi inda aka aike ta ta siyo abubuwan ta dawo. Tana miqa mata kayan zata wuce dakinsu Yaburra tace mata "Kira yar uwar ki kuzo". Suna zuwa Yaburra ta cewa Fusam ta tube rigar jikin ta. Tsayawa Fusam tayi fuskar ta dauke da mamaki "Zaki tube koh sai na miki na taya ki tube shi! Tube wannan tsumar da ke jikinki". Ta fadi. Tana kuka Fusam ta cire rigar kan Yaburra ta ce mata ta kwanta ruf da ciki. Sabuwar rezan da taje ta siyo mata Yaburra ta bude ta fara yanka fatar bayan Fusam da shi. Wani irin ihu Fusam ta saki ta yunqura zata miqe Yaburra tace mata wallahi in ta miqe sai ta kashe ta. Shatu ta saka ta danne mata Fusam ta dinga jan mata rezar a jiki tana ji mata ciwo. Kan ka ce mene bayan Fusam yayi jazur sai jini ke zuba kuma dama gata fara ce. Hadiza ce ta zuquna tana roqar Yaburra tayi haquri ta daina.
"Dan Allah baza mu qara ba. Dan Allah Yaburra kiyi haquri". Amma kamar ba da ita take yi ba har sai da tayi wanda ya isheta tukun tace ma Hadiza ta dauko jakar gishirin tazo ta shafawa Fusam kan ciwukan ta. Hadiza na kuka tana roqan ta tana fada mata sun tuba dan Allah tayi haquri amma sai tsawa Yaburra ta daka mata "Zaki yi abunda nace koh kema sai na saba miki". Ba yadda Hadiza ta iya hakan nan tayi kamar yadda Yaburran ta buqata "Ki cuda shi sosai ya shiga jikinta. Gobe zaki qara saka kazamar hannun ki ki dakan mun diyata". Ta fadi tana hankada Fusam da qafarta. Baqin ciki da tashin hankalin da Hadiza ta shiga ranar ba kadan ba. Kwana suka yi kuka, Fusam na kwance jikinta tana kokarin share mata jiki da tsumma da ruwan sanyi. Haka kuma suka kwana ba a basu abinci ba.
YOU ARE READING
Lawh-Al-Mahfouz
General FictionIna hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kow...