"Umma" Ibrahim ya fadi sai kuma yayi shuru.
"Ina jin ka". Umma ta fadi. Gaba daya attention dinta ta tattaro ta maida kan sa tana jiran jin abunda zai fadi.
"Wai dama nace ba..." Ya fadi yana dan susar qeyar sa, kan sa a qasa "Tun da naga ta sama sauki sosai koh za a fara shiri ta tare". Yar murmushi Hajia Falmata tayi kan ta ce.
"Su Ibrahim kenan. Ka qosa mu baka matar ka koh". Kasa dago kansa yayi ya kalla Umma sabida kunya "Toh shikenan zan yi magana da Abbanku anjima In Shaa Allah sai a fara shirye shirye koh". Godia Ibrahim ya mata kan ya miqe ya wuce dama ya shigo gaishe ta ne da safe zai wuce aiki.
Kan ya wuce sai da ya biya dakin Hadiza ya same ta tare da Hansatu suna hira. Gyara murya yayi kan yayi sallama, Hansatu zata miqe ta basu wuri ya tsayar da ita "Ba zama zanyi ba. Zan wuce aiki ne". Ita dai Hadiza kan ta a qasa bata ce komi ba dan har zuwa wannan lokacin nauyin sa take ji. A lokacin kuwa auran su wata uku amma bata daina jin kunyar sa ba.
"In na dawo zamu futa. Bayan Isha'i, sai ki shirya". Ansa shi tayi da toh kan tayi masa fatan alkhairi ya wuce. Yana ficewa Hansatu ta fara zolayar Hadiza wadda kan ta a qasa tayi ta murmushi.
Kulawan da Hadiza ta samu cikin yan watanni ukun da take zama a gidan surukan ta ya sa ta murmure tayi kyau abun ta, hasken ta da tsananin kyaunta suka futo sosai. Duk wanda ya gan ta sai yayi sha'awar ta, kullum fes da ita ga natsuwa da kuma ladabin da take ma Umma yana qara mata farin jini gun Umman wadda take riqe ta da zuciyar ta daya, tamkar diyar ta.
Suna hirar su Umma ta shigo ta same su. "Hira ake haka ne wai" ta fadi kan ta sama wuri ta zauna. "Nikam in Hadiza ta tafi gidanta zan ga yadda Hansatu zata yi". Umma ta fadi tana dariya kan ta qara da "Gashi kuma mijin ta yace mu kai masa matar shi".
"Kai Umma da gaske". Hansatu ta fadi "Da wuri haka". Ta tabe baki.
Yar murmushi Umma tayi "Aikuwa dai yanzu zamu fara shirin kai ma Abba Ganah Hadizan shi". Hadiza duk kunya ya cika ta ta kasa cewa komi sai zama tayi shiru tana sauraron su Umma har ta fara shirye shiryen tarewan ta.
Ibrahim be dawo gida ba ranar da wuri sabida yadda aiki ya masa yawa. Sai dab da sallan isha ya shigo gida, straight ya wuce dakinsa yayi wanka ya shirya ya futo ya wuce masjid. Sai da aka yi sallar isha'i tukun ya dawo gida ya wuce ya sama Hadiza wadda ta shirya tsaf kamar yadda ya umurce ta.
Yana kallon ta ya saki wata iriyar murmushi, wani irin sudden sanyi na ziyartar zuciyar sa. Ganinta ya warware masa gaba daya stress of the whole day. "Mu je koh". Ya fadi yana miqa mata hannu. Yi tayi kamar bata ga hannun da ya miqa mata ba kawai ta miqe ta iso shi. Murmushi yayi kan ya jawo ta zuwa jikinsa, ba zatto taji yayi engulfing dinta in a hug.
"Wana turare ne wannan?" Ya tambaye ta "Yayi mun dadi". Ya fadi yana qara shaqar kamshinta.
"Ya...". Bata qarasa ba taji ya sumbaci saman kan ta kan yace mata "Kinyi kyau sosai". Idanun sa suna kan ta sai dai ita kuma kan ta a qasa ta qi dagowa ta kalle sa. Murmushi yayi son ta yana qara yaduwa zuciyar sa, komi Hadiza tayi burge sa yike. Ji yike tamkar zuciyar sa zata fashe sabida tsananin yawan irin kaunar da yike mata.
Qara matsowa kusa da ita yayi zai kuma sumbatar ta tayi saurin kaucewa, making his lips land on her cheek. Yar dariya yayi kan ya lumshe ido ya matso kusa da kunnen ta.
"Deeza" ya fadi cikin muryar sa me cike da sanyi "Sunan da zan dinga kiran ki da shi kenan daga yanzu. My Deeza".
Gyaran muryar da suka ji anyi ya sa Ibrahim yayi saurin sakin ta. Koh da ya juya Ummah bayan Ummah ya gani ta juya tana komawa ta hanyar da ta futo. Shakka babu ya san sabida halin da ta gan su ciki ya sa ta juya ta koma.
YOU ARE READING
Lawh-Al-Mahfouz
Ficción GeneralIna hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta. Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kow...