HAJIYA BABBA POV.
"Jarma har yanzu ban ga komai ba"
Ta fada tana karewa Jarma dake zaune a gabanta sanye da babbar riga, kansa kuma da rawani.
"Kina gaggawa ne kawai Hajiya, ba gashi mun fara ganin haske ba? Komai a sannu ake binsa"
Ya dauke kai tana kallon wani bangare na dakin.
"Ba Mai Martaba nake magana ba, Shattima shine matsalata a yanzu"
"Da Shattiman za mu fara kamin Mai Martaba ya biyo shi, idan mu ka yi gaggawa to kamar muna fallasa sirrinmu ne, ya kamata mu bi komai a sannu"
"A sannu na ke bin komai Jarma, domin burina dole ne ya tabbata, Talba kadai na ke son ya yi mulkin garin nan, so na ke na ga Ammy na zubar da hawayen bakinciki, shekarun da ta saka na yi a damuwa so na ke ta ninka a cikin bakinciki, na san a yanzu tana farinciki da ciwon Mai Martaba saboda tana ganin Shattima ne zai gaje shi ko? Hmmmm"
Ta karasa tana murmushin gefen baki. Jarma ma murmushin yake yana kallonta zuciyarsa na saka masa burinsa.
'Za mu kawar da Shattima da Mai Martaba, amman dan ki ba zai yi milkim garin nan ba, indai ina raye'
A zahiri kuma sai ya gyara babbar rigarsa ya ce.
"Da sannu komai zai wuce Hajiya, kuma kar Salim ya fasa neman Nana"
Sai a lokacin Hajiya ta dawo da kallonta a gurinsa.
"Ai dole ya neme ta, tun da har Mai Martaba ya sallama masa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu, dole ne Ammy da zuri'ar ta su dawo karkashin kulawata, duk abun da tai min a shekarun baya sai na maimaita mata shi"
Ta karasa zancen fuskarta na sauyawa alamar bata son tuna bayan.
"Komai zai wuce Hajiya komai zai zama tarihi da yardar Allah"
Ya daga masa kai tana sauke wani dogon numfashi.
"Haka ne, tashi ka je kar a fara yi mana zargi"
"Zargi kuma na nawa? Sai dai kar a koma"
Ya fada yana mikewa tsaye da murmushi a fuskarsa, sannan ya dan risina mata.
"Na bar ki lafiya"
Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta mike tsaye ta nufi gaban drawer ta dauki wayarta ta aikawa Hajiya Talatu kira bugu daya ta daga tana jerowa Hajiya Balki wani irin kirari da ke kasa kan Hajiya fashewa.
"An gaishe da Talatu Uwargidan Waziri"
Talatu ta risina kamar Hajiyar ce a gabanta.
"Allah ya kara miki lafiya da imani, Surukar Ammy kuma Uwar Sarkin gobe, a ganki a bar ki kuma a bi ki a dole"
Hajiya Bilki ta yi wani irin kasaitaccen murmushi.
"Yanzu Jarma ya fita daga nan"
"Tsohon makiri, Allah yasa dai ba ki masa zan ce na ba, domin tsab zai labartawa Waziri komai ya kashe mim aure a asirance"
"Taya za ayi na bar shi ya san shirin mu Talatu? Bayan na san shi akwai kwadayin masarautar nan a ransa? Ubansa daya fa da Mai Martaba kuma babu yadda be yi ba Mai Taba ya bashi Babbar masauta ya ki, yanzu kuma kike tunanin baya sha'awar wannan?"
Hajiya ta dan yi jimm tana murmushi mai sauti
"Mu dai gama da bangaren sauran ne sannan mu dawo kansa, na kira ki na ji yadda ake ciki"
"Zan shigo da kaina ranki ya dade, domin maganar ba ta waya ba ce"
"Ina jiranki"
"To ranki ya dade"
YOU ARE READING
FULANI
FanfictionFULANI -The story of unwanted girl, she always had a strong sense of destiny...! The story of a Prince and his kingdom. witchcraft, distorted relationships, hidden secrets, selfishness.