ADDU'AR GMW D ABOKIN GB K WN MAI IKO 13

76 5 0
                                    

Addu'ar Gamuwa da Abokin Gaba, ko wani mai iko اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ . Allahumma inna naj'aluka fee nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim. Ya Allah! Mu mun sanya ka a gabansu, kuma muna neman tsarinka daga sharrace-sharracensu. اَللَّهُمَّ أَنْتَ عَضُدِي، وَأَنْتَ نَصِيرِي، بِكَ أَجُولُ وَبِكَ أَصُولُ وَبِكَ أُقَاتِلُ. Allahumma anta 'adudee, wa-anta naseeree, bika ajoolu wabika asoolu wabika oqatil. Ya Allah kai ne mai karfafa ni, kuma kai ne mataimakina, da karfinka ne nake yin dabarun yaki, kuma da karfinka ne nake kai hari, kuma da karfinka ne nake yin yaki. حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ. Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel. Allah ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro. اَللَّهُمَّ رَبِّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبِّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَارًا مِنْ (فُلاَنٍ)، وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلاَئِقِكَ؛ أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى، عَزَّ جَارُكَ، وَجَلَّ ثَنَاؤُكَ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ. Allahumma rabba s-mawati s-sab'i wa rabba-l-'arshi-l-'azimi. Kun li jaran min (fulanin) wa ahzabihi min khala'iqika, an yafruta 'alayya ahadun minhum aw yatgha. 'Azza jaruka, wa jalla thana'uka, wa la ilaha illa anta. Ya Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, ka kasance mai tsari gare ni daga wane dan wane, da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare haddi, kariyarka ta buwaya, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai kai. اَللهُ أَكْبَرْ، اَللهُ أَعَزُّ مِنْ خَلْقِهِ جَمِيعاً ، اَللهُ أَعَزُّ مِمَّا أَخَافُ وَأَحْذَرُ، أَعُوذُ بِاللهِ الَّذِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ، الْمُمْسِكِ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ أَنْ يَقَعْنَ عَلَى اْلأَرْضِ إِلاَّ بِإِذْنِهِ، مِنْ شَرِّ عَبْدِكَ فُلاَنٌ، وَجُنُودِهِ وَأَتْبَاعِهِ وَأَشْيَاعِهِ، مِنَ الْجِنِّ وَاْلإِنْسِ، اَللَّهُمَّ كُنْ لِي جَاراً مِنْ شَرِّهِمْ، جَلَّ ثَنَاؤُكَ وَعَزَّ جَارُكَ، وَتَبَارَكَ اِسْمُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ " ثَلاَثَ مَرَّاتٍ. Allahu akbaru. Allahu a'azzu min khalqihi jami'an. Allahu a'azzu mimma akhfu wa ahdharu. A'udhu billahi lazee la ilaha illa huwal mumsikis samawatis sab'i an yaqa'na 'alal-ardi illa bi'izinihi, min sharri 'abdika (fulanin) wa junudihi wa atba'ihi wa ashya'ihi minal-jinni wal-insi. Allahumma kun li jaran min sharrihim Jalla thana'uka wa 'azza jaruka, wa tabaraka smuka, wa la ilaha ghayruka. (3). Allah shi ne mafi girma, Allah shi ne mafi buwaya daga dukkanin halittarsa, shi ne mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin Allah, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai rike sammai daga su ruguzo a kan kasa sai da izininsa, daga sharrin bawanka wane (ya ambai sunansa), Ya Allah! Ka zamo mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma kaiyarka ta buwaya, kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba. (sau uku).

Abin da wanda ya ji tsoron wasu mutane zai fada: اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ. Allahummak finihim bima shi'ita. Ya Allah! Ka isar mini su da abin da Ka so.

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now