ISTIGFARI (NEMAN GAFARA) 82

110 4 0
                                    

Istigfari (Neman Gafara) Da tuba zuwa ga Allah Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Na rantse da Allah! Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau saba'in. Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare shi sau dari. Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "wanda ya ce; أَسْتَغْفِرُ اللهَ الَّذِي لاَ إِلَهَ إلاَّ هُوَ الْحَيُّ القَيّوُمُ وأَتُوبُ إِلَيهِ. Astaghfirul-lahal-lazee la ilaha illa huwal-hayyul-qayyoomu wa-atoobu ilayh. Ina neman gafarar Allah, Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye, Mai tsayuwa da komai, kuma ina tuba zuwa gare shi. ... Allah zai gafarta masa zunubansa ko da zunubin gudua daga fagen fama ne". Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "Mafi kusancin da Allah yake kasancewa da bawansa a tsakiyar karshen dare ne. Don haka idan kana da ikon kasancewa cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin to ka kasance". Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, "mafin kusancin da bawa yake kasancewa da Ubangijinsa yayin da yake sujada ne, don haka ku yawaita addu'a (a cikin sujada)". Kuma manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Hakika a kan lullube zuciyata, kuma ni ina neman gafarar Allah sau dari a rana".

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now