104- Addu'ar Komowa daga Tafiya: Abdullahi Ibn Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga tafiya wani yaki, ko aikin hajji ko umra, idan ya hau tudu sai ya yi kabbara sau uku, sannan ya ce: اَللهُ أَكْبَرْ، اَللهُ أَكْبَرْ، اَللهُ أَكْبَرْ. لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، آيِبُونَ تَائِبُونَ عَابِدُونَ لِرَبِّنَا حَامِدُونَ، صَدَقَ اللهُ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الأَحْزَابَ وَحْدَهُ. Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar. La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa 'ala kulli shay-in qadeer, ayiboona ta-iboon, 'abidoon, lirabbina hamidoon, sadaqal-lahu wa'dah, wanasara 'abdah, wahazamal-ahzaba wahdah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne (shi kadai), kuma yabo ma nasa ne (Shi kadai); kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Mu masu komawa ne, masu tuba, masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu. Allah Ya gaskata alkawarinsa, ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.
YOU ARE READING
HISNUL MUSLIM
General FictionLittafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni. Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152]. Ya'ay...