Addu'a Yayin Da wani Abu da Ba ya so ya afku ko abin da ya fi karfinsa. Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Mumini kakkarfa ya fi alheri kuma ya fi soyuwa ga Allah daga mumini mai rauni, a tare da kowanne daga cikinsu kuma akwai alheri. Ka yi kwadayin abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah; kada ka gajiya. Idan wani abu ya same ka, ka kada ka ce; da na aikata kaza da kaza, da kaza ya kasance, sai dai ka ce; قَدَرُ اللهِ وَمَا شَاءَ فَعَلَ Kadarullahi Wama Sha'a Fa'ala Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi yake aikatawa; domin da na sani tana bude kofar aikin shaidan.
YOU ARE READING
HISNUL MUSLIM
General FictionLittafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni. Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152]. Ya'ay...