ƘAZAMIN TABO
02
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
Momy ganin halin da yake ciki sai ta isa wajensa ta kamo hannunsa ta ja shi zuwa dakinsa dake sama, suna isa ta zaunar da shi a gefen gado ta tsaya a kansa tana cewa.Anas dan Allah ka rika dawowa gida da wuri, kaga Abbanku har yanzu dukanka yake bai lura da ka girma ba, haka yake maka hukunci a gabansu Nabeel, shiyasa wlh ko kunyi min abu nake tsoron fada masa domin irin hukuncin da zai yi muku.
Amma Momy kema kin san bana yawo, meyasa Abba zai rika yi min haka? Yasan fa yanzu na kawo girma bai dace ya rika yi min irin wannan hukuncin ba, sai ka ce dan goye.
Ya fada yana fidda kwalla.
Hakuri zaka yi tunda haka Allah yayi shi, Kai dai ka rika kiyayewa kawai ka zauna lafiya ba tare da ka shiga tarkonsa ba.
Hmmm kawai ya ce yana girgiza kai irin zafin zuciya na kunno shi, ya mike ya cire rigarsa ya wuce toilet, Momy da kallo tabi shi cike da tausayinsa ta fice daga dakin. Anas ya shiga shawa ya sakarwa kansa ruwa idonsa a bude sai hura iska yake daga bakinsa, shi mutum ne me tsananin hakuri amma fa fushinsa bai da kyau, Abbansu wani irin mutum ne mai matukar zafi shiyasa ko sun yiwa Momy laifi bata fada masa saboda tana tsoron irin hukuncin da zai yi musu, Hatta Leema da take auta bai raga mata ba, in sunyi laifi ko da kuskure ne gani yake dagangan ne hade da iskanci, shiyasa yake jibgarsu kamar ya samu fulawa, hakan ya kawo rashin shakuwa a tsakaninsa da yaransa, sai mugun tsoronsa da suke kamar sunga kura, da zarar ya dawo daga kasuwa ko wanne zai na natsu, basa iya kwakkwaran motsi gudun kar suyi laifi.
Alh. Habeebu Maitama asalinsu fulani ne dan katsina, Maitama inkiyar Family dinsu ne, shi kadai ne a wajen iyayensa aiki ya kawo mahaifinsa Ahmad garin kaduna daga nan suka kafu a nan, sunan mahaifiyarsa Aina'u wacce suke kiranta da Kakus, Mahaifinsa ya kwanta dama tun yama matashi, Kakus tayi wani auren ta cigaba da rikonsa wanda Allah be bata wani haihuwar ba, shima mijin ba jimawa ya rasu, hakan yasa ta hakura da aure ta daura Habeebu kan dukiyarsu da yake mahaifinsa ya bar masa makudan kudi, sannan ta kara samun tumunin takaba a rasuwar mijinta na biyu, sai Habeebu ya hade kudin ya cigaba da juyawa tare da zurfafa karatunsa a harkar kasuwanci. Har Allah yasa yayi aure ya samu zuri'a.
Haj. Kausar su uku ne wajen iyayensu Rahma ita ce farko Allah ya yi mata rasuwa, sai Kausar sannan Kamal Wanda yanzu ya kammala karatunsa yana koyarwa a primary dake unguwar sarki, asalinsu mutanen kaduna ne daga karamar hukumar kubau, aikin mahaifinsu na gomnati ya dawo dasu kaduna, in da suke zaune a unguwar sarki, mahaifinsu Alh. Tasi'u ya rasu sai mahaifiyar su Binta wacce suke Kira da Hajja Mama ita ce ta rage musu, shiyasa ko da yaushe su Bushra suna zarya zuwa wajenta, saboda yadda take matukar ji dasu, sabanin Kakus da bata cika sakar musu fuskan wasa ba.
Anas shine babba Wanda yake da shekara ashirin a duniya, ya kammala secondary sai dai result dinsa be yi kyau ba, ya zana har sau biyu ba nasara yanzu ne yake kokarin sake zana wani, ya yi saukar Al-Qur'ani. Sai Nabeel ke bi masa yana da shekara sha bakwai wanda yake a ss2 yana aji biyar a islamiya. Sai Bushra yar shekara sha hudu tana jss 3 tana aji biyu a islamiya, sai auta Ikileema tana da shekara sha biyu a matakin primary 6 tana ajiya daya a islamiya.
Sun taso cike da so da kaunar juna saboda Momy tana kokarin hada kansu, sai dai ita mace ce me sanyi wanda yasa bata iya hukunta su in sunyi mata laifi sai dai ta hadasu da Abbansu, shiyasa take koyar dasu duk wanda ya ci zalinsu su rama. Abba mutum ne me tsantseni akan haram, yana da riko da gaskiya shiyasa bai yarda da cin hanci ba, muddun yaro yaki maida hankali a karatu ba zai taba asarar kudinsa ba wajen siya masa jarabawa, a kullun fade yake sai dai kokarinsu ya tsiratar dasu, shi yasa ya kasance mai matukar tsauri da tsare gira saboda baya son wasa da sakarci, a ganinsa yin hakan ga yaransa shi ne zai sa su zama mutanen kwarai masu riko da gaskiya harma suyi ko yi da shi a nan gaba.
YOU ARE READING
ƘAZAMIN TABO
RandomAkwai ƙalubale me tarin yawa a cikin wannan Hikayar, bance babu soyayya ba sai dai akwai ababen ban mamaki da zasu faru, domin ya tattaru da manyan damuwa, kunci, rikici, abin tausayi, sai soyayya da yake a matsayin madubin labarin.