ƘAZAMIN TABO
06
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir._Masoya ina godiya da comments tare da addu'arku gareni, ina jin dadin hakan, Allah ya kara zumunci ya saka da alkhairi_
Khadija sai wajen karfe biyu da mintuna ta farka daga barci saboda jiya gaba daya bata runtsa ba, sallah ta fara yi kafin ta zauna a falo Matar Yaya Jabiru ta kawo mata abinci tuwan shinkafa miyar taushe, kadan ta tsakura ta ci sai ta kora da ruwa, duk da ta so ta ci sosai amma gaba daya cikin nata a tushe yake sannan bakinta babu apitite ko kadan, ta mike ta koma ciki ta kara kwantawa ba barci take ba sai zurfafa tunani da ta yi akan maganarsu Baba, ta san babu me goyon bayanta dan hak dole ta saduda ta mikawa Allah lamarin, ba zata so ta sabawa iyayenta ba akan Auwal ba, sannan ba zata so ace tsinuwar Baba ya tabbata a kanta ba, dole ne ta danne zuciyarta ta yi abinda suke so, sai dai bata jin Yaya Auwal zai kuma ganin dariyarta balle har wata mu'amalar aure ya kuma shiga tsakaninsu, zata cigaba da zama a gidansa dan yin biyayya ga umarnin iyayenta. Haka ta dinga saka tana warwara har wani barcin ya dauketa.
Sai bayan sallar la'asar ta farka ta yi wanka ta mai da kayan jikinta kafin ta fito ta shiga sashin Yaya Ahmad, matarsa itama hakuri ta kara bata tare da shawarwari wanda zasu amfaneta, haka ta saki jiki sosai suka dan taba hira, daga bisani tayi mata sallama ta wuce sashinta Yaya Abubakar.
_Bangaren Auwal kuwa ya hadu da Alh. Abba a gidan hutu, ya labarta masa duk abinda ya faru tare da cewar.
Wlh na tsorata da lamarin Khadija, banyi zaton fushinta ya kai har ta iya marina ba da zagi.
Kaine baka san halin kishin mata ba Amma wlh fiye da haka ma in wata ce zata yi, kar dai ka nuna Mata gazawarka ka jajirce Mata sosai akan auren babu fashi. A hankali da kanta zata gane gaskiya.
Kafin ta gane kuwa naji jiki wlh.
Ba wani jin jiki sai ka ce ba namiji ba, ka yi mata dubara ka kara shiga jikinta, duk abinda zata yi maka ka shanye a hankali taza bari, ga wani magani na tadanar maka nasan zai maka amfani a wannan lokacin, na karin karfin maza ne duk da nasan baka sha, amma Insha Allah in ka sha shi zaka sha mamaki domin kuwa zaka kashe boss fiye da sau uku lokaci guda, na tabbatar ka yi mata irin wannan zuwan wlh dole ta sara maka ta sauko, Kuma zai kara maka kima sosai a gunta, tunda kace ma'abociya son raya dare ne.
Kwarai kuwa khadija ba tada wasa a shinfida, shiyasa ma kwana biyun nan nake kewarta.
Ka gwada ka gani zaka bani labari.
Abba ya amsa ya kafa kai ya shanye maganin, a karamar gorar swan yake maganin, yana da kyau sosai domin yana maganin basir da sanyi, sannan kuma yana huce takaicin namijin daya iya gamsar da matarsa, yana gama sha yayi gyatsa tare da jin cikinsa ya murda daga nan kuma ya daina. Alh. Abba ya cigaba da cewa.
Yana sanya yawan fitsari sannan kuma wasu yana sanyasu ciwon mara, daga bisani kuma yana taso da makauniyar sha'awa sosai, amma sai zuwa anjima zaka ji shi kafin nan ma ta dawo.
Kwarai ina da yakinin yanzu haka tana gida, domin dazun nayi waya da Yaya Aminu, nasan ba zasu barta ta jima bata dawo ba.
Allah dai ya kara hakurin zama, dan lamarin mata sai an kai zuciya nesa saboda tunaninsu ragagge ne.
Cewar Alh. Abba, haka suka cigaba da tattaunawa har yamma, bayan sunyi sallar la'asar suka isa wani gidan cin abinci suka cika tumbinsu daga nan kuma suka leka kasuwa.
_Su Amira sun dawo hadda tun karfe ukun rana, ganin babu kowa a gidan Mami bata dawo ba sai ta dafa musu indomie suka ci, Nura ya fita tsakar gida ya cigaba da wasa da kekensa ita Kuma ta shiga dakinta ta kwanta, ba jimawa barci ya dauketa, sai wajen biyar da rabi ta farka ta fito ta samu Nura yana kallo a falo tace cikin damuwa.
YOU ARE READING
ƘAZAMIN TABO
AcakAkwai ƙalubale me tarin yawa a cikin wannan Hikayar, bance babu soyayya ba sai dai akwai ababen ban mamaki da zasu faru, domin ya tattaru da manyan damuwa, kunci, rikici, abin tausayi, sai soyayya da yake a matsayin madubin labarin.