ƘAZAMIN TABO
05
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
Abba ya isa gida ya same su a falo Mami tana koyawa Nura assignment din maths da aka ba shi, sai kuma Amira tana yin nata homework din, shigowarsa yasa suka bar abinda suke yi Nura yaje da gudu ya rungume Abban Yana yi masa oyoyo, Amira kuwa sannu da zuwa tayi masa, Mami ta mike ta isa gareshi tana yi masa sannu ta amsa key hannunsa suka shiga dakinsa, ruwan wanka ta fara hada masa shi kuma ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet, sai ta fito falo ta hada abinci a dinning ta ce su Amira suje daki su karasa assignment din, suka mike suka wuce abinsu ita kuma ta koma daki ta sauya kayan jikinta zuwa kananun kaya wanda suka kamata ta yi kyau sosai tare da daure sumarta da rebom sai ta fito, dai dai shima Abban ya fito falon saye da jallabiya ya wuce dinning ta sameshi a can, ta zuba masa abinci, kamshin turarenta ya sanya sha'awa ta taso masa yaji bukatar matarsa sosai domin tun jiya yake jin sabon sauyi a jikinsa, sai dai duk da yana jin son kasancewa da ita dole ya fadi mata abinda ke dawainiya da shi a zuciya domin ya huta da zullumi, ya soma cin abinci yana lumshe Ido saboda tsananin dadinsa, ya dago kai suka hada Ido Khadija ta kanne masa Ido daya tana fidda shu'umin murmushi, itama fa yau jinta take tamkar sabon mutum tsananin bukatarsa take, a iya haka ta tabbatar da maganin nan yana aiki sosai, Abba yayi murmushi tare da cewa.Abincin nan ya yi dadi kamar yadda nake tsammanin me abincin za ta kara dadi fiye da kullun.
Uhum ai ka san tsakaninmu ko wani rana kara tsumuwa muke na dadi, dan haka kaima nasan zakinka ya karu fiye da kullun.
Madam Khadija kina kara tsumani, yanzu dai ki adana sauran bayani na gama cin abinci.
Ta kyalkyale da dariya shima ya taya ta, haka ya kare cin abincin a daddafe suka mike zuwa falo suka yada zango a cushing, Khadija ta shige jikinta yayi saurin janyewa yana cewa.
Ki na sane dasu Amira ba suyi barci ba, ki bari abincin dana ci ya tsirga min kafin ki tadamin kwadayinki.
Mikewa tayi tana murmushi.
To bari na sallamesu na dawo.
To yace ya cigaba da kallon Film ita kuma ta wuce dakin Amira tace su kwanta tunda gobe Sunday sai su karasa assignment din, ta tasa keyar Nura zuwa nashi dakin shima ya kwanta, sai da ta tabbatar da sun kwanta kafin ta isa dakinta ta bude Waldrop ta shiga zabar rigar bancin da zata sanya, tana tsaye a gurin Abba ya shigo dakin ya sameta a inda take tsaye ya zura mata key din motar daya siya mata a tsakiyar breast dinta, da sauri ta dafe tana juyowa ta sakala hannunnta a wuyansa tana fadin.
Kyautar mena samu ne haka?
Ki duba ki gani mana.
Ta sanya hannun damanta ta ciro key din, sai ta ware idonta waje cike da mamaki da murna.
Yaya Auwal sabuwar mota Kuma? Zaka kasheni da farin ciki, wayyo ni dadi.
Dariya ya yi ya zame jikinsa ya je ya zauna gefen gadonta, sai ta bi shi itama ta zauna gefensa cike da murna.
Abban Amira ka shammatar ni, wato duk kyauta in zaka min sai ka bani surprise ko.
Ga karin wani ma.
Ya ciro damin kudin a aljihu ya mika Mata.
Dubu dari biyar ne ki kara jali.
Rungume shi tayi tana murna sosai ta sake shi ta kara hade bakinsu tayi masa kiss sosai, kafin yayi mata dubara ya zame daga jikinta saboda yana tsoron ya zurma kogon masoya harya kasa fada mata zancen auren, ya nisa tare da dagowa ya kalleta sosai, sai duk tausayinta ya kamashi yadda take farin ciki sosai yasan yanzun nan zai dagula mata lissafi, kallon da yake mata yasata dawowa hayyacinta tace cikin natsuwa.
YOU ARE READING
ƘAZAMIN TABO
RandomAkwai ƙalubale me tarin yawa a cikin wannan Hikayar, bance babu soyayya ba sai dai akwai ababen ban mamaki da zasu faru, domin ya tattaru da manyan damuwa, kunci, rikici, abin tausayi, sai soyayya da yake a matsayin madubin labarin.