11

156 5 0
                                    

ƘAZAMIN TABO

11

Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir.

*karshen freepage*

Pay N200 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card 09034940106, a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu

Abba yana isa gidan Alh. Abba ya yi parking a tsakar gidan yana kokarin  kirashinsa sai ga Alh. Abban ya fito saboda yaji karar shugowar motarsa, ya mika masa hannu suka gaisa, a yadda yaga Abba a ya yamutse yasan babu lafiya, sai ya jashi zuwa falonsa suka shiga suka zauna Alh. Abba yace. 

Abokina yana ganka haka? Ince dai ko lafiya? 

Alh. Abba komai ma ya faru, kafin na fada maka abinda ya faru, ina so ka fadamin ko maganin nan yana sanya mutum ya fita hayyacinsa? 

Gaskiya baya haka sai dai in ka sha wani magani bayan shi wata kila su hadu su gusar maka da hankali, sannan tunda nake sha bai taba yimin haka ba, da fatan bai jefaka a matsala ba. 

Hmmm a babbar matsala kuwa ya jefani, domin yasa na aikata abinda ya zamemin mummunar kazamin tabo wanda harna koma ga Allah ba zai gogu ba. 

Meya faru ne haka Alh. Auwal? 

Alh. Abba ya fada yana tashi zaune daga jinginar da yayi a kujera, idanun Abba suka yi ja kamar zai fasa kuka, sai ya danne zuciyarsa ya shiga ba shi labarin duk abinda ya faru. A tsananin zabura Alh. Abba ya mike tsaye yana rafka salati, ya daura da cewa cikin damuwa. 

Wannan wace irin kaddara ce, wlh dana san wannan abin zai faru da tun farko ban baka ka sha ba, kaicona.

Aikin gama ya riga ya faru sai dai ban san ta ina zan fuskanci matsalar ba, khadija ta kwashe kayanta dana Amira tabar gidan da asubahi, tsorona karta fallasa wannan barnan da nayi, ban san da wani ido zan kalli iyayenmu ba da mutanen gari, ina cikin tashin hankali Alh. Abba, yanzu menene mafita? 

Alh. Abba ya koma ya zauna cike da zurfafa tunaninsa sai da ya dauki minti biyar kafin ya sauke numfashi yace cikin damuwa. 

Daga can gidansu an kiraka? Ko ka kira kaji ko taje can?

Babu wanda ya kirani kuma ban kira kowa ba. 

To ina ganin inda taje gida ya isa zuwa yanzu wani daga mutanen gidan sun kira ka musamman in sun ganta da kaya niki niki. Yanzu ina so ka kira daya daga cikin yayyinta ka tambaya ko ta zo gida muji ta yadda zamu shawo kan matsalar. 

Cikin rawar jiki Abba ya kira yaya Aminu yayi sa'a wayar tana hannunsa, kiran na shigowa ya dauka, suka gaisa kamar yadda suka saba kana Aminun yace. 

Ina me taurin kai? ai jiya sai da ta sha duka, da fatan dai lamura sun fara dai daita. 

Abba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace cikin damuwa. 

Ai yanzu ma kiran dana yi maka kenan akan naji kota zo gida, saboda tun asuba ta kwashe kayanta dana Amira ta bar gidan. 

Amma khadija anyi mai taurin kai, kuma bata zo gida ba, dan yanzu nake baro sashin su Baba kuma ya ce dama zai kira ka akan ka kara hakuri da halinta, ina ga wani gun ta nufa bari yanzu naje na sanar dasu domin susan halin da ake ciki. 

Abba yace masa to kafin ya kashe wayar, ya duba alh. Abba. 

Kaga kuwa bata je gida ba, to ina ta nufa?

Nayi tunanin haka da wuya taje gida, saboda ma kota fadi abinda ya faru babu mai yarda da ita domin zasu yi tunanin bakin kishinta zai sa ta iya yi maka sharri, dan haka mafita shine kafin ta bata ka a gunsu gwara kai kayi hanzarin kare kanka ta hanyar nuna musu tsantsar damuwarka akan barinta gidanka, kuma ka tabbatar musu da jiya data dawo ko magana ba kuyi ba, kawai ka wayi gari ta kwashe kayanta ta bar gidan bayan ka tafi masallaci yin sallar asubahi. Daga nan kuma sai muje wajen malam Ilyasu yayi mana aiki akanta ta yadda zai rufe mata baki ta kasa fadawa kowa abinda ya faru, kaga munyi maganin matsalar. Amma shawara ce in tayi maka to in bata yi ba sai ka yi abinda zuciyarka ta yanke maka. 

ƘAZAMIN TABOWhere stories live. Discover now