Tsokaci

138 5 1
                                    

ƘAZAMIN TABO

By

Rahma Kabir

*TSOKACI*
ƘAZAMIN TABO wani irin labari ne mai tafiyar hawainiya wadda a ko da yaushe yana rikida ya sauya launi zuwa wani irin tunani mai ban tausayi, tafiya ce mai nisa sai dai a kowani gaba da irin salon da yake sarrafa kansa. Daga jin sunan labarin kawai ya isa sanya mai karatu zurfin tunani domin akwai tarin magana a ciki tare da nuna babban taraliya mai rikitar da lissafi.

Hakika rayuwar wasu yana shayar da mutum abin mamaki tamkar a cikin labarin hikaya, wanda kuma nau'in rayuwa ce ke daukar mutum ya yi yawo da shi zuwa sararin duniyar Kaddara. Wani lokaci rayuwa ta shayar da mutum zuma ko kuma madaci, sai dai duk lokacin da kaddara ta zo, hakika jinkiri da nuna juriya tare da dogaro ga Allah shi ne yake kai mutum zuwa ga matakin samun nasara.

Labari ne da ya ke fuskartar akala har guda biyu,wadda a wani bangare Kaddarar Anas take farawa tun yana matakin bagala har zuwa girmansa ya zame masa KAZAMIN TABO. Hakama ta bangaren Amira yadda kaddara ke bayyana a gareta tun kuruciya tare da fidda ita zakka a cikin dangi har ya zame mata KAZAMIN TABO mai dauke da babban tambari.

Akwai ƙalubale me tarin yawa a cikin wannan Hikayar, bance babu soyayya ba sai dai akwai ababen ban mamaki da zasu faru, domin ya tattaru da manyan damuwa, kunci, rikici, abin tausayi, nadama, sai soyayya da yake a matsayin madubin labarin.

Kamar yadda masana suka ce tafiya mabuɗin ilimi ne, to gamu a wani matakin zango, ban ce zai yi tsawo sosai ba, sannan bance zanyi sauri ba, komai dai zai tafi daki daki cikin salon sarrafa alkamina. Ku kasance tare da ni domin littafin ya fara sauka tun a February 11/2/2022 freepage daga na farko zuwa sha daya, don samun labarin kai tsaye tare da samun cigabansa sai ku biya akan farashi mai sauki N200 kacal.

Pay N200 to 0106956864, Ramatu Muhammad Kabir, Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card  09034940106, a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

Rahma Kabir ce.
MrsMG

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 08, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƘAZAMIN TABOWhere stories live. Discover now