Page One

2K 83 7
                                    


👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Asmeeey_h (Zeeneert)*💕

Zeeneert@wattpad

*Bismillahir rahmanir rahim. In the name of Allah,the most graceous and the most merciful*

*NB: Wannan labarin Kirkirane and if incase yayi kama ko daidai da labarin wani ko wata toh that person should find a place in his/her heart to forgive me for akasi akasamu. Thank you*

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thank you and happy reading*. 😍

Page One

*Damaturu,Yobe State*

Unguwar *Sabon pegi* nanan hanyar Maiduguri road dake cikin garin Damaturu. Sabon pegi na daya daga cikin manyan unguwannin dake cikin garin Damaturu hakanan unguwar ta kunshi mutane daban daban,mutane of different standards and classes kama daga kan masu kudi,yan tsakatsakiya harma da talakawa. Unguwace daza'a iya samun manya manyan Malamanmu na addini na kwarai,manya manyan yan siyasa,yan kasuwa,yan boko damakuma masu neman nayau da kullum. In a nutshell,Sabon pegi dai unguwace da is cosmopolitan (unguwar data kunshi mutane from different places,status dakuma asali).

Yau Laraba kuma yanma ne lilis dankuwa rana ma gab take da faduwa wanda hakan yasa unguwar tazama so busy motoci,kekenapeps,masu bicycle dakuma masu tafiyar kafa sai kai kawo sukeyi cikin unguwar kasancewar lokacin yayi daidai da lokacin da yawanci yan garin kedawowa gida gurin iyalansu. Lokacin ne da yawancin Ma aikata suketasowa daga aiki,yan makarantar Jami'a dasuka yini sunayin lecture suma lokacin suke tasowa,yan islamiyar yanma ma around that time suke tashi hakana yan napep suma lokacin komawansu gidane kasancewar napep is not allowed after 6pm agarin. Akwai kuma masu kasuwancin abinci da kayan makulashe every blessed evening irinsu soyayyen dankali,doya da flawa,wainar flawa,arawa,masara dadai sauransu wanda yanzune lokacin fitowarsu. Sekuma Samari masu zaman kashe wando wanda daidai wannan lokaci shine lokacin fitowarsu daga gida su kafa majalisarsu wanda hakan yakesa unguwar kullum yanma yazama so busy.

Daga cikin Yaran dasuka taso daga *Nurool huda Islamic School* nahango wasu Yan mata uku dake tafiya tare suna sanye da Combination na blue and white uniform wanda kusan kansu daya yake. Kowannensu Goye take da school bag dinta abaya. Biyu daga cikin Yan matan hira suke suna dariya da alamadai hirar dasukeyi din tayi musu dadi ayayinda dayar kuma is busy pressing her phone danko kallon gabanta batayi. Bakin daya daga cikin titinan anguwan suka iso zasu tsallaka. Biyu da are so attentive tsayawa sukayi suna jiran motocin dake yawo kan titin su wuce kafin su tsallaka ayayinda budurwa me danne dannen wayar kuma tasaka kai zata hau titin batareda ta lura cewa su summa tsayaba bare har tayi tunanin tsayawan itama. Batakuma duba gefe,gabanta da bayan ta ba bare taga comotion din motoci da kekunan keyi akan titin. She's so engrossed using her phone dama batasan me duniyar take cikiba

Kawaye biyun ganin abunda yar uwarsu ke shirin yi yasa cikin sauri daya daga cikinsu ta janyota baya ayayinda dayar kuma ta daka mata tsawa "Iklima bakida hankaline?" atsorace Iklima tajada baya tana salati dankuwa se alokacin hankalinta yadawo jikinta gakuma motoci dataga sunata wucewa agaban su. Atsorace tace "Innalillahi! Kunsan banmasan mun iso bakin titiba" tayi maganar tana dafe kirjinta looking so tensed,she don't even want imagine mezai faru da kawayen nata baswa tareda ita.

Harararta Kawarta da tajanyotan tayi tace "Ina zaki sani dama kinata aikin danne dannen waya?" Iklima still shocked and at thesame time trying to defend herself tace "Important abu nake karantawa fah Aisha" wannan karan wanda ta daka mata tsawan ne tayi magana "important abun yafi rayuwarki kenan Iklima?" Pouting baki Iklima tayi ashagwabe ganin they're not going easy on her tace "Toh wai yanzun masifa zakuyi tamin kamar wasu tsofaffi instead of kumin jaje. kuskurenefah kuma bazan karaba kunsandai dagangan bazanyi wasa da precious life dina ba" kawayenta biyun dariyar  keta suka saki lokaci guda tareda fadin "Kamar gaske. Allah dai yasatoh"
Iklima tace "Amin" tana harararsu playfully sekuma tashiga fada musu important abunda take karantawar tace "ku kunsan mena kekarantawa yaja hankalina?' Cikin sauri suka girgiza kai curiously
Iklima tace "Sadiya cousin dita ce tasa a status wai za'afara jamb registration this coming Monday shine nashiga Twitter official page dinsu don in tabbatar da zancen banso inbaku fake news kunsan social media da rumours and it turns out dagaske ne" Aisha tace "toh aini tunjiya nasamu labari. Baba dakansa yakirani yake fadamin jiya dadare yaji a labarai a radio. You could've asked dana baki authenticity" Aisha ta karashe maganar tanama Iklima gwaliyo cikin wasa.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now