Page Sixteen

579 49 2
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Asmeeey_h (Zeeneert💕)*

*Zeeneert*@wattpad

*This book is strictly fiction though Ina kokarin yin book din tayanda zaiyi kamar you're reading a true life story but believe me nothing is true here. Duka concept na imagination dinane, I've no relation with soldier's nor do I consult any of them though naso yin hakan anma bansamu dama ba. So I only use my knowledge and browse few things to make it look real for you to have happy time reading so please no one should come for me. Thank you*

*Page Sixteen*

Message ne yayi popping a screen din wayar Mami,Ameera ne taturo mata Voice message,clicking onto the notification Mami tashiga whatsapp tayi playing VN din. Tambayarta Ameera take ya Hamma and how are things going on between them,dariya Mami tasaki bayan tagama jin VN din sannan tashiga turamata reply using VN itama tace “Waini meyafaru kwanannan kusan kullum sekin tambayeni abunda ke goyin tsakanina da Hamma” dankuwa tunda suka dawo daga Yola kusan kullum setayi inquiring akan Hamma sede in basuyi maganaba. She often ask questions like
“Ina Hammanki Sister inluuuu?” “Hamma yakiraki ne yau,kunyi waya da Hamma ne yau?” “kuna chatting da Hamma?” etc  which is so unlike her,Ameera sam sam ba mutum bace meshiga huruminda bashafeta ba sede inkaika sakota aciki. Ameera tace “Babu komai Sister inluuuu kawai naga kwanaki kafin yadawo you were always complaining baya replying messages dinki dadai sauransu shiyasa nake yawan tambayarki. I want to makesure you people are okay” Mami tayi murmushi tace “Karki damu Ameera,tunkafin indawo daga Yola mukayi resolving differences dinmu and akwai improvement yanzu,with time everything will fall back to its rightful places insha Allah” Ameera tasauke nannauyar ajiyar zuciya tace “I'm relieved to hear that Mami” dankuwa news din bakaramin relieving dinta daga stress datake yawanshiga akan al amarin yayiba lokaci guda.

Can bangaren Muzammil kuwa cikin dare yafara motsi yana mutsu mutsu tsakiyar gadonsa ayayinda yaketa  jujjya kansa,munanan mafarke mafarke regarding attack dinda akayi lokacin yana yaro har aka kasha parents dinshi yakeyii,how people were running for their lives,how so many innocent lives were mercilessly killed harya iso inda mahaifiyarshi kegudu dashi abayanta cikin dokar daji,yaga yanda attackers din ke firing musu wuta non stop wanda hakan yasata ajiyeshi gindin wani katon bishiya meduhuwa tace karyayi motsi yazauna shiru anan yabuya zata leka insun wuce zata dawo tadaukeshi sutafi. Tashinta daga inda yake batayi ko 6 steps ba yaga tafara gudu da alama haduwa tayi da attackers din and before he knows it she was shot to death,wani irin ihu yasaki daganan yafadi yasume agurin. Arazane yafarka daga mafarkin yatashi yazauna a tsakiyar gadon yana fidda numfashi akai akai kamar wanda yayi gudun fanfalaki,haka zuciyarshi tashiga aikin bugawa dasauri dasauri. Jikinshi kuwa gabadaya yajike jilib da gumi dukda kuwa Fan din dakin dake kunne,be kunna AC ba dayake garin akwai dan sanyi. Ba abunda Muzammil ke nanatawa se “innalillahi wa inna ilaihi raji’un,Hasbunallahu wani’imal wakil” seda ya tabbatar bugun zuciyarnashi yaragu sannan ya tsagaita,yamika hannunsa kan bedside yadauko remote din AC dana wutan dakin,wutan dakin yafara kunnawa sannan yakunna ACn . yadauko hankerchief dabaya yawan rabuwa dashi akusa yashiga goge gumin fuskarsa. 

This is how he has been battling with this nightmares tun bayan ankashe parents dinshi,ada kullum yakeyi anma dayake Ummi da Daddy sun tsaya sosai kan abun seda aka samomai magani yadaina frequently se an dan kwana biyu. There was a time dayayi kusan shekaru hudu baiyi mafarkin ko saudayaba wanda har hakan yasa su Ummi sukayi tunanin koya warkene gabadaya. Kwatsam rana daya Yan ta'adda suka shigo unguwarsu dadare sunata harbe harbe harsuka shiga wani gida sukayi kidnapping wani magidanci,bayan komai yalafa suntafi ankokkoma bacci Muzammil bacci yagagara,daya fara rintsawa munanan mafarkan zaiyi tayi haka sukayita fama na kusan sati guda,seda aka dangana da komawa gurin me magani sannan yasamu sauki inda daganan kuma baikuma samun attack dinba seda yatafi South Africa suka fara training,sede inbeji karar bindiga ba toh haka zai raba dare yana wahala, this's how he's been suffering for the past Four years. There were times daya dinga yankan jiki yana Fadi insun fita training yayi witnessing similar scenerious amma kosau daya baitaba fada agidaba yakuma hana Makarantar ma fada tahanyar rokansu. Yasan insu Ummi suka sani hankalinsu tashi zaiyi irin Daddy kanma cewa zaiyi ya hakura da karatun tunda daman can bawai hankalinshi ya kwanda da karatun sojan bane. Haka yadinga battling alone haryagama and here he's still suffering.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now