Page Eight

516 54 11
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZZAMIL*
( _The Brave warrior_ )

Written by *Zeeneert*💕

*Zeeneert*@wattpad

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thank you and happy reading*.

EID MUBARAQ Everyone. Allah ubangiji yamaimaita Mana.

*Page Eight*

Yawanci Yan Familyn basusan su Daddy suntafi South Africa bikin Yaye Muzammil a makaranta ba dayake tafiyar tazo a bazata. Mami da labari yaje kunnenta bakaramin dadi tajiba dankuwa she's been thinking ya Hamman nata zaiji on his grand day ace babu wanda yaje mishi.

Yau kwana goma da rasuwar Hajja kuma bakin dasuka zo duk yawanci sun kokkoma gidajensu se wadanda basu samu zuwa gaisuwar ba dasuke shigowa sama sama suyi ta aziya sutafi wanda hakan yasa aka tattare kayan Hajja gabadaya akasakashi acikin dakinta aka rufe. Mami  da Ameera duk sundawo sashinsu dankuwa tunda akayi rasuwar acan suke zama tareda Waleeda. Waleedan ma kuma yau takoma gidansu dukda kuwa Daddy da Abba Babba sunyi requesting tacigaba da zama acikin Family house din,aidon Hajja tarasu bawai yana nufin yan uwanta sunkare baneba. Anriga da anzama daya anma seta nuna hakan beyimataba,tafi ganewa takoma gidan dole su Abba Babba sukayi hakuri suka kyaleta.

Mami dayanma lilis tashirya tanufi sashin su Ameera. A parlour tasamesu  duka matan harma da Ummi datakeyi ma Fa'iza kitso.

Mami karasawa tayi gurin Ummi tarungumeta tana murmushi kafin tasami gefenta tazauna tace "Ummi ina wuni?" Ummi tace "Lafiya Lau Daughter. Wannan zuwankun dai kin gujeni" Mami tawara idanu tana dariya tace "wallahi Ummi bahaka baneba rasuwar da akayinnan ne yasa. Gabadaya kowa baya zama" Ummi tajinjinakai tace "dawannan ma. Allah yama Hajja rahama daduk wanda suka rigamu gidan gaskiya" duka yan parlourn suka amsa da "Amin" Mami takarada "Anma karkidamu Ummi,yanzu harse kin gaji daganina" Ummi tayi dariya tace "Mami kintaba gani inda Uwa tagaji da kallon Yarta?" Ameera tace "Uhmmm sabida Hamma yakusa dawowa koh? Aidole kice harseta gaji da kallonki" Mami tadauki throw pillow guda daya tawullah ma Ameera ayayinda Ameera tayi sauri ta kauce tana dariya tareda fadin "miye hakan? Daga fadan gaskiya"

Mami tatura baki cikin sigar shagwaba tace "Ai ita Ummin ma tasani tunda ina zuwa" Ummi dake musu dariya tace "Kyaleta Daughter inkinzo danshi dinma seme? Wani yayi zuciya yakawo nashi mana"
Mami tashiga rawar murna playfully tana ma Ameera dariyar mugunta ganin Ummi tasamo lagwon Ameera,tace "Yauwa Ummi fada matadai. Mutum yayi zuciya yafiddo miji mumishi aure"
Ai lokaci daya bakin Ameera ya mutu. In akwai abunda bataso toh shine Ummi tafara yimata maganar saurayi ko aure. Itan ma nawa take? She's not even 18 yet and talura Ummin sotake tayi mata aure at her early age,if possible ma tahada aurenta dana Hamma lokaci guda bayan itakuma ko saurayi bata tabayiba bare tamayi tunanin may be they can have a feature together,ita duk wanda yatareta a hanya ma koya nuna yana sonta to tsananshi takeyi because gani take he might get in the way na achieving dreams dinta,ita aure is not even part of her closest agender, batada wani buri daya wuce taga ta zurfafa karatunta tazama wani abun fada a rayuwa. She wants to be independent,she wants to become a Medical doctor dazata dinga taimakon mutane tasamu lada.

Sautari in Ummi tafara yimata maganar aure ko saurayi inta fada mata ga kudurinta se Ummin tace "Ameera Aure baya hana karatu dai. There are so many Women out there dasukayi karatu suka zama successful agidajen mazajen su and they are just doing fine" anma setake gani kawaidon Ummin tanason tayi aurenne take fadin irin wadannan maganganun inbahaka ba akanmi za ace tahada karatu da aure bayan tana ganin yanda iyayenta ke wahalar aikace aikace acikin gida dukda kuwa sunada masu tayasu din. Bagasu Aunty Ilham dasu Adda Deenah ba suma aigashi duk sun girme su kuma haryanzu basuyi aurenba karatun su sukeyi.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now