Page 9

1 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na tara*

*Alƙalamin Real Nana Aisha*

Duhun dare da ya mamaye na mujiyarsu ne ya hana su ganin takamaiman halin da Talatu take ciki, da mugun gudu Saude ta ɗauko fitila tana haskawa. Wata irin razananniyar faɗuwa ce ta ziyarci Saude har ba ta san lokacin da ta kurma uban ihu haɗe jefar da fitila ba, sakamakon tozali da jinin da yake bin kafafuwan Talatu da ta yi. Faɗi take,

"Na shiga uku na lalace ni Saude! Wayyo Allahna! Sun kashe min 'ya sun huta don ba su haifi 'ya mace ba, wayyo ni Allah! Na mutu na lalace! Wallahi sai an bi min hakkina don ba zan taɓa yafe muku ba, dangin mayu da suka yi gadon maita tun daga kaka da kakanni."

Faɗin Saude cikin masifa don jinin da ta gani yana ƙwaranya daga kafafuwan Talatu ya yi matuƙar tsorata ta ainun, kuma duk a tunaninta mayu ne suke shan jinin 'yar tata don jinin ya yi mugun ba ta tsoro.  Sai dai babban abin da ya yi matuƙar ɗaure mata kai yadda Talatun take ambaton sunan Kabiru har da su ya cuce ta. Lallai biri ya yi kama da mutum! Ko tantama ba za ta yi ba akwai wata kullalliya a lamarin nan don ruwa ba ya tsamin banza! Amma ba za ta taɓa yarda ba a sha jinin 'yarta a kwana lafiya ba, don ita ɗin murucin kan dutse ce ba ta fito ba sai da ta shirya don haka ko ana ha-maza-ha-mata sai ta yi ƙara da su. Tana shirin magana muryar Umma Hafsat ta ratsa masarrafar sautinta, cikin guɗa haɗe da shewa ta faɗin,

"Ahayye nanaye! Abun kunyar da ake alaƙanta ɗana da shi sai ga shi a ɗakin uwar 'yan mata! Har mu za a yi wa barikanci? An ba wa yarinya maganin zubar da ciki an zo ana mana maganar banza don a raina wa Malam hankali? To mu tsaf muke gane lagon duk wani shege da shegiya eheeee!"
Ta tsahirta haɗe da sakin wata dariya har amsa-amon muryarta yana tashi sama, sannan ta sake kai duban ta ga Talatu da take yashe a ƙasa tana haska mata fitilarta da ta ɗauko saman rumfa sannan ta furta,

"An daɗe ana tafka ruwa ƙasa tana kashewa! Ashe dai an jima ana tsula tsiya a gari tun da har an san a sha maganin zubar da ciki. Lallai karuwancin Talatu ya yi ƙamari a duniyar nan, kodayake uwarta ta ɗaure mata gindi tun da har take saye maganin zubar da ciki."

Hafsat ta idasa maganar tana sakin dariya mai ƙarfi ba tare da ta yi la'akari da talatainin dare ba, tamkar wacce aka yi wa bushara da gidan aljanna, ita kuma duk tana yin haka ne saboda huce haushin sharrin da Saude ne ta yi mata ɗazu da safe.

Yadda kalaman Hafsat suke yi wa Saude dirar mikiya a kunnen tamkar zubar ruwan dalma yake a cikin kunnenta saboda mugun ɗacin su. Sosai kalaman suka samu damar ratsa sako da lungu na jikinta haɗe da samu masauki a ma'adanar sirrinta watau zuciyarta. Gabanta sai dakan tara-tara yake yi, zuciyarta ta yi wani rin tsalle tamkar za ta faso kirjinta ta fito waje, tsabar kaɗuwa da tashin hankali musamman yadda kalaman Hafsat suka dake ta sosai kuma suka samu matsuguni a zuciyarta, ko shakka babu gaskiya ce maganarta in ta yi duba da yadda Talatu take fama da amai kwanan nan, shakka babu ɓarin ciki ne ta yi.
Har wata zufa take tsattsafo mata tsabar tashin hankali, da ta san wannan abun kunyar za ta ganin da ba ta gigin kunnan hasken fitila ba, take ta yi nadamar haske fitalar saboda munanan kalaman Hafsat gare ta.  Amma kasancewar Saude ta ci ta koshi da makirci, cikin borin kunya ta kurma uban ashar kafin daga bisani ta fara masifa tana faɗin,

"A hir ɗinki da kike alaƙanta 'yata da karuwa! Baƙinciki sai dai ya kashe ki a kanta, don ba ki haifi mace ba kullum burinki ki yi mata sharri! Ni da 'yata kainuwa dashen Allah ne kuma muricin kan dutse ne, mu ba mu fito ba sai da muka shirya don haka tsintsayenki su kiyaye gawonmu tun muna shaida juna."
Ta tsahirta haɗe da duban Baffa Jabiru da ya zama kamar gumki yana kallon ikon Allah, sanna ta kalle shi haɗe da faɗin,
"Wallahi Malam in ba ka yi wa matarka kashedi ba sai na kai ƙararta maraya an bi min hakkina ni da 'yata."
Ta sake tsahirtawa don jin ko zai ce wani abu amma a banza wai an tura agwagwa a ruwa, ganin ya ƙi ce mata ci kanki sai ta dora da faɗin,

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now