Page 10

0 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na goma*

*Alƙalamin Hussy Sani*

Ko da Mai daddawa ta shiga gidan ta iske Rahane kamar yadda aka faɗa mata akan guiwa, nan fa ta shiga ɗakin ta tisata gaba, zamanta babu daɗewa aka dawo daga samo motar da za ta kaisu birni, ɗaukar Rahane aka yi aka sanyata a mota, nan Mai daddawa da wata dattijuwa suka shiga motar aka sha.
Saboda rashin kyawun hanya ba mai naƙudar ba harsu kansu sai da suka sha wahala, a galabaice suka shiga asibiti, nan aka kawo gadon ɗaukar marasa lafiya aka ɗora Rahane.
Wuri su Mai daddawa suka nema suka zauna, Rahane ta sha baƙar wahala sosai amma haihuwa shiru, jaririn ya gicce mata a ciki sai uwar azaba ta ke sha  amma haihuwa ta yi shiru, hankalin likitoci ya tashi sosai.
Yanke shawarar yi mata aiki suka yi nan aka sanar dasu Mai daddawa, kowa ya nuna alhinin shi akan wannan al'amarin, amma ganin wannan ce kaɗai hanyar da za a iya taimakonta yasa suka amince, nan ta ke mijinta yasa hannu.
Wani sabon tashin hankalin da ya faru kuma an je wurin aikin amma jinin Rahane ya hau sosai ga zuciyarta ta kumbura babu damar yi mata wani aiki.
Wannan abu ya tsoratar dasu matuƙa, ga wahala tana sha amma haihu tsit, duk wanda ya leƙa Rahane kallo ɗaya zai mata ya yi ƙwana saboda tausayi, likitoci sun kai biyar akan Rahane kowa na ƙoƙarin nuna ƙwarewar shi amma abu ya gagara, ganin abun ba na ƙare ba ne yasa likitoci sanar dasu halin da ake ciki.
Kuka kowa ke yi na tausayin halin da Rahane ta ke ciki, ko motsi ta kasa sai dai idanuwa da ta ke bin mutane dasu.
Mai daddawa kuwa kallo ɗaya za kai mata ta baka tausayi saboda irin kukan da ta ke yi, wasu Fulani ne suka kawo 'yar uwarsu haihuwa, kallo ɗaya wani bafillace ya yi ma Mai daddawa jikinta ya ɗauki rawa, gudu-gudu sauri-sauri ta tashi ta bar wurin ta koma can baya.
Ba ta fito ba sai da ta ga ya yi tafiyar shi sannan ta dawo, wasa-wasa mai naƙuda shiru sai baƙar azabar da ta ke sha, sai ga shi har gari ya waye dai babu haihuwa babu labarinta, ga duk lokacin da likitoci za su dubata sai su ga haihuwar ce gata nan kusa.
Washe gari wurin ƙarfe uku har lokacin Rahane ba ta haihu ba tana dai shan baƙar wuyar, likitoci sun rasa yadda za su yi da ita, duk lokacin da aka auna sai a ga jininta a sama ya ke ga zuciya ta kumbura, dole sai dai idanuwa aka tsuba mata tare da binta da addu'a, duk mai imani idan ya kalli irin wahalar da Rahane ke sha sai ya tausaya mata, kamar daga sama sai ga wannan bafillacen na jiya ya dawo, wani ruwa ne ya bada cikin ƙwarya ya ce ga shi a tabbatar da Rahane ta shanyesu yanzu, ganin wahalar da ta ke sha yasa likitocin basu hana bata ruwan ba.
Har ga baki aka kai mata ƙwaryar dan ko yatsanta bata iya ɗagawa, cikin ikon Allah tana shanye ruwan da kamar minti biyu sai ga sabuwar naƙuda ta tashi, babu daɗewa ta haihu amma yaron babu rai.
Tana haihuwa sai jini ya ɓalle mata tamkar an bude famfo, nan ma dai duk iya yin likitoci sun kasa tsayar da jinin, ganin haka yasa wannan bafillacen ya fiddo wata doguwar carbaha daga aljihunsa daga nesa ya saita cikin Rahane ya bugi iska.
Wata irin ƙara Mai daddawa ta saki tare da dafe cikinta, juyowa aka yi ana kallonta.
Durƙushewa ta yi ta ci-gaba da murƙusu a wurin, ta jima sosai tana cikin wannan halin na murƙusu kafin ta miƙe tsaye ta kalli bafillacen cikin azaba ta ce,"Dan Allah kai man rai karka wulaƙantani."  Ko magana bai yi ba sai dai nuna mara hanyar waje da ya yi babu ko sallama ta miƙi hanya ta bar asibitin.
Magana ake mata amma tamkar kurma haka ta kasance a wurinta, kowa zuciyarsa cike da mamakin abun da ya faru dan dai a gaban kowa duk abin da ya wakana ya faru.
Ganin bafillacen ya juya ya yi tafiyarsa nan mata aka rinƙa gulma akan abin da ya faru.
Gawar jaririn aka tafi da ita can ƙauye dan a rufe, nan fa wannan matar da suka je tare ta zayyane duk abin da ya faru a asibiti, nan ta ke surutu ya tashi aka fara raɗe-raɗin Mai daddawa mayya ce.
A kiɗime Mai daddawa ta iso ƙauyensu, tana dawowa kuma ta iske yaranta sun dawo daga tafiyar da suka yi, ganinsu yasa gabanta faɗuwa.

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now