⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO**E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE TWO*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Garin yaya kaji rauni haka Lamido? Subhanallah khalid shigo mana ka duba min shi..."
Tuni ta kama Lamidon zuwa kan gado tana kwance d'aurin da yayiwa wurin da hannayenta gabad'aya ta shiga damuwa, hannunta ya rike yana d'an Murmushi yace
"Amah is not that serious fah...."
Buge hannunshi tayi tace
"Shut up"
Ta juya ta kalli kofa khalid na tsaye kanshi ne kawai ciki duka jikinshi na waje, tace
"Khalid Wai baza ka shigo ba?"
Yana ta Kallon yarinyar da ni kaina ban san wacece ba yace
"Amah baki ga da aljana Yayanmu ya dawo ba? Ko kema baki ganinta kaman shi? Ni kad'ai nake kallonta?"
Se lokacin hankalin Amah ya je kan yarinyar, bata kawo komai ba ta nufe ta tana cewa
"Subhanallah baiwar A...."Ihun da ta tsala tana komawa bayan shi ta rike riganshi seda ya tsorata su duka, shi Amah take kallo yayinda shi kuwa idanunshi ke kan hannunta dake damtsen shi, seconds biyar ya d'auke idanun shi tare da kallon Amah, khalid kam tuni ya koma ko kan nashi ba'a gani.
A sanyaye Amah tace
"Lamido ina ka samo ta? Bata da lafiya ne?"
Cewa yayi cikin gajiya
"Amah taimakonta nayi I think bandits sunyi kidnapping d'inta se Allah ya turo ni ta hanyar na taimaketa but since then taki magana sannan motsi kad'an se ta rikeni I don't know why"Cike da tsantsar tausayinta har hawaye na cika a idanunta tace
"Allah sarki baiwar Allah..."
juyawa tayi tana duba khalid sede ba shi ba alamun shi, dariya tayi tana girgiza kai tace
"Kaikam khalid matarka na kokari..."
Juyowa tayi tace
"Lamido bari In dubo khalid d'innan se ya zo ya duba Ku gabad'aya ko zata samu sauki samu Mu san inda ahalinta suke na san duk in da suke hankalinsu ba a kwance ba"Mikewa yayi yace
"Amah bara na duboshi kema fah baki da lafiya"
Cewa tayi
"No gwara in je sbd ita bazata yarda ta zauna dani ba, kuma be dace kana tafiya da ita a haka ba ba d'an kwali ba takalmi tana bukatar hutu"Bata jira cewarshi ba ta fice, kallon ta yayi kanta na kasa gashinta Har yanzu ya rufe mata fuska ruf, Allah ya sa ba masifa ya nemarwa kanshi ba, idan ze tuna tunda ya ceceta banda muryan kukanta be ji tayi magana ba, sannan wannan nanukewar na me? Shi da idan batayi magana ba yana son barinta wurin Amah ya koma aiki in ta samu lafiya daga baya ta koma gida.
Dan kallon d'akin yayi kan cabinet d'in gadon ya kalli robber lin da alamu wani abin aka warware dashi, d'aukowa yayi ya dawo ya zauna, a ranshi yana furta
'I'm just helping you, duk abinda zanyi miki I will do it out of pity...'
Hannunta ya kama ya zaunar bakin gadon ya saka hannayensa biyu ya had'e gashin nata zuwa baya ya d'aure mata tare da kurawa fuskanta ido.....Abinda be ta'ba yi ba a rayuwarshi wai ya kurawa mace ido na fiye da minti d'aya se a kanta, ko ba komai baze mantata ba ta kafa tarihi a rayuwarshi, 'Tana da kyau' ya Ayyana hakan yana kallon daran darán idanunta da suke kasa.
"Baiwar Allah...!"
Shiru bata d'ago ba, yace
"Ya sunanki?"
Kawai se ta fashe da Kuka, Sossai take Kuka tare da rike hannun shi se ta fara nuna mishi waje, idanunta da suke zubar da hawaye yake kallo, zuwa lips d'inta da take motsawa a hankali alamun tana so tayi magana sede ta kasa ne be sani ba....Rubbing goshin shi yayi yana kara kasa da murya sbd kanshi da ya fara sarawa yace
"Is Ohk.... is Ohk baki so a tambayi sunanki? Toh bazan sake ba i will just call you Amatullah... Ohk?"