⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO**E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE FOUR*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Da sauri Amah ta mike tsaye tana cewa
"Barka da shigowa Hajiya Babba"
Tsaki ta ja tare da cewa
"Ba shi na tambayeki ba... waye ke da matsalar kwakwalwa nace ko Asma d'in ta fara dod'e miki kunne ne Uwar tuzuru?"
Dukansu kai suka dukar suna jin zafin zagin mahaifiyar tasu da ake yayinda shi Abrar gabad'aya ya sa a ranshi sbd shi ne ake iya ciwa Amah zarafi, Auren nan kam dole ne? Mukarrama ita ce macen da ya ta'ba so Allah be yi ya aureta ba ya ce ya kare so ya rufe baabin soyayya suna tunanin wasa yake?
Shi fa ba yaro bañe at his age of 42 yaci ace ya za'barwa kanshi abinda yake ganin shine daidai da rayuwarshi ya ma wuce ma...Yana ji Amah zata fara magana ya katseta
"Patient d'in khalid ce"
Harara ta banka mishi tare da jan tsaki, tace
"Dama Muhammad ne ya matsa min In zo In dubaki a cewarshi baki da Lafiya se kuma na zo na tadda kin saka d'ima d'iman yara a gaba kina basu abinci daga Katon Tuzuru se fand'ararre, kai kuma dena Kallo na da idanu kaman na mayu"Ta dakawa Maher tsawa, da sauri ya dukar da kai, fita tayi tana mitar itakam Muhammad ya auro mata zuriyar mayu en anace gashi Saude bata da zuciya kwata kwata kaman ta yar kare ya lashe, duk abinda suke mata bata nuna ta damu sam...
Ajiye spoon d'in da be kai ga kaiwa bakinshi bane yayi yana shirin Mikewa Amah da kanta ke kasa tana juya chokali cikin abinci tace
"Lamido ina me umurtar ka da ka zauna ka ci abincin nan ka bani plate.."Had'e rai yayi kaman be ta'ba Sanin me dariya ba ya fara cin abincin, duk zuciyarshi Amah Bata rene shi da rashin kunya ba, ta samu wani irin tarbiya daga iyayenta wadda ya iya lankwasa shi tun yana karami, ta san yadda take bi dashi sede In be yi motsi gabanta ba ta san abinda yake nufi, ita ce kawarshi tun daga randa ta fara fahimtar halinshi da Allah ya hallice shi da kayanshi...
Har suka gama cin abincin ba wadda ya sake magana, parlor suka dawo Amah ta umurci Maher ya zo da ruwa da kanta ta 'ballo magungunan ta bashi a tsaye ya sha yana me duba time a wayarshi baya so d'aya ya mishi a gidan sam, sbd jin gidan yake kaman kurkuku, kofa ya nufa yana cewa Amah
"Se na dawo"
Be kai ga fita ba Tace
"Lamido...!"
Dakatawa yayi tare da juyowa, Mikewa tayi ta nufi d'akinta se yabi bayanta sanin magana ne take dashi, Khalid yace
"Aah za'ayi sirri uwa da d'a"
Abdulkadir yace
"Kai kam idan yayanmu na nan me kake nema ne da Amah... duk hankali da kulawarta na kanshi, ni tun Ina kishi har na gaji na kyale"Sadiq ne dake ta kallon jabir dake ta ciccin magani yace
"Ya J, ya akayi ne naga kaman ranka a 'bace ko Hajiya babba ce?"
Duk hankali suka mayar kanshi seda yayi tsaki akallah biyar kan yace
"Ni ce ban yi sa'ar mata ba ko haka duka matan suke ne?"Aisha da suke wasa dashi sossai tace
"Kanwata ta sake laifi kenan Uncle J?"
Kaman yadda yaranta biyu ke kiranshi,
Ze yi magana Abdulkadir yace
"Shhhh... kayi mata nasiha karka kasance me fad'an sirrin gidan ka a ko da yaushe yawan korafi ma matsala ce, hajiya Maman Aslam(Aisha) an kasa kunne don aji gulma ba"
Dariya suka kwashe dashi, Ita kuwa ta fara cewa
"Kai kuwa me bamu sani ba Uncle A? Kaga gwara karka 'Bata bakinka ni da Uncle J kaman 5&6 ne ko ka hanashi magana anan se naji"
Ruqayya matarshi ma ta saka baki akan ai Sumayya kam ko J be fad'a ba ita zata fad'i mutum cikinshi sam ba rike sirri, raha suka ci gaba dayi tsakaninsu... wadda wannan kaman farilla ne in an had'u ba Amah da Uncle Moh(Abrar) kaman yadda yaran kannen suke kiranshi, kaman zasu d'aga gida da hira da Tsokana...