⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO**E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE FIVE*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Har ya bud'i baki da niyyar amsawa hajiya yaya ne se ya fasa, waigowa yayi ga Amah yace
"Allah sarki, Allah ubangiji ya bata lafiya me yasa tun jiya d'in Abrar be sanar dani ba ai da da safen nan na tafi na dubo ta, d'a na kowa ne kuma musulmi d'an uwan musulmi ne kinga wani dalili ze sa in hanata zama gidana? Na san inda Allah ze jefa nawa tunda na haihu?"Farin ciki ne ya cika zuciyar Amah wadda har yayi nasarar bayyanuwa saman fuskanta, ta kasa fasalta irin daad'in da taji sbd har ga Allah tausayi da kaunar Amatullah ya riga da ya tasirantu cikin rai da ruhinta, murmushi kayatacce tsohon ya saki ganin farin ciki kan fuskar matar tashi, Hajiya Yaya da ta had'e rai cike da takaici tace
"Amma dae Alhaji..." hannu ya d'aga mata yace
"Dakata Halimatu.! ina da yakinin Abrar baze ta'ba kawo abinda ze cutar damu ba, kai ko wani ne ya kawo se inda karfinshi ya kare wurin kare mu.. dan haka ki saurara min.."Cike da takaici tace
"Au kenan yanzu da ni kake?"
'Dago ido yayi ya zuba mata kallon da yayi mata yasa ta fice fuu, d'age kafad'a yayi ya sani ita ma kuma ta sani ta sanadiyarta suka kusa rasa shi ba don kariyar ubangiji da kuma Abrar da Allah ya bashi ba da yanzu sede wani ba shi ba, yana godiya wa Allah da ya bashi d'a irin shi tabbas Abrar kyauta ne na mussaman a gareshi kuma za'babbe shi yasa ko da yaushe akan uzuri yake mishi sbd maganar Aure,sanin kuma waye Abrar yasa be yi yunkurin fitar da mace ya aura mishi ba dukda umarni kawai ze bashi ya cika.... maganar Amah ce ta dawo dashi daga duniyar tunani da ya tafi suka hau hira irin ta asalin masoya waenda tsufa ko girma be sa soyayyar da sukewa juna ta ragu ba sema karuwa da take a kullum...*****
Cikin yanayin tafiyarshi ya d'auki doguwar varender d'in da zata sadashi da Amenity,kanshi kasa as usual bakinshi na motsi a hankali jin kaman ana kallonshi ne yasa ya d'ago a natse ya kalli gabanshi sau d'aya ya cigaba da tafiya,har ya d'an wuce da taku biyu chakk ya tsaya tare da waiwayowa...
"Brigadier General Muhammad Abrar Muhammad Magashi"
Matashin mutumin ya ambata wadda hakan ya tilastawa Abrar dakatawa tare da waiwayowa, a shekaru ze iya bashi shekaru uku zuwa hud'u, bayanshi sojoji ne guda biyu rike da bindigunsu cikin cikakken shiri sa'banin mutumin dake sanye da personal wear, kankance idanunshi yayi kan ya furta
"Wlh na tsaneka.."'Dan wara idanu Abrar yayi yana d'age gira yace
"Na sani,sai me?"
"Nayi alkawari matukar ina numfashi a doron kasa se na kaskantar dakai mafi munin kaskantarwa,ba haka kake yawo ba kai wai me tausayin na kasa dashi? Muje zuwa.."
Baki ya ta'be tare da d'age kafad'a yace
"Wadda ya isa ya kuma yarda da kanshi shi ne ze iya yawo haka sa'banin matsoraci da ya riski matsayi ba tare da chanchanta ba,ka ta'ba ganin zaki ya tafi farauta a gayya? Ina so ka kwana da sanin cewa kai kai d'in nan colonel Nura bukar baka isa yiwa Muhammad Abrar muhammad magashi komai ba se abinda Allah ya hukunta. If you don't have any important thing to say fi amanillah"Daga haka ya juya yayi tafiyarshi cikin kasaita da kuma isa wadda duk ya had'e su Amah d'iyar sarkin Gombe ce 'Lamido Muhammad' ce wadda ya ci sunan mahaifin nata kuma tsab ya gaje kasaitar da ita bata dashi sede jini duk inda aka ce jinin sarauta se kaga hakan a d'abi'ar mutum...
'Dakin ya tura ba tare da yayi magana ba da sauri Amatullah dake raku'be karshen gado ta d'ago kai idanunta jage jage da hawaye, ganinshi yasa tayi saurin dira ta nufoshi kan ta isa gareshi ya d'aga mata hannu sbd ya san haramcin ta'ba macen da ba tashi ba, a tausashe kaman yadda yake magana cikin rashin hayaniya yace