⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO**E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE THREE*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Zubawa khalid lulu eyes d'inshi yayi Yana kallon shi da kyar khalid ya iya cewa
"She's unconscious again sikila ce tana bukatar jini har bag biyu"
Runtse idanunshi yayi yana jin tsantsar tausayinta a ranshi kallon khalid yayi yace"Mu je lab"
Sanin jininshi O+ ne yasa ya furta da confidence, Khalid ya kalleshi yace
"Amma yayanmu kai jininka ya zuba be dace a...."
Shiru yayi ganin irin kallon da Abrar ke mishi be sake sauraranshi ba ya wuce, ba yadda khalid ya iya haka ya bi bayanshi....Duk wani karfin hali nashi ya tattara yake driving d'in kaman baze kai ba, duk yadda khalid ya so ya huta bayan gama transferring jinin ya ki ko da kallonshi, Kai tsaye gida ya nufa bayan tabbatar mishi da dr Alfa yayi zatayi atleast 11 hours Bata farka ba...
Narasawa GRA ya nausa wani layi ya shiga da gidajen wujajen ma kawai abin kallo ne, a bakin wani tankamemen Iron Golden gate ya danna Horn, da sauri gate man d'in dake sanye da blue and black uniform ya leko kanshi, da gudu ya koma ya fara kiciniyar bud'e gate d'in, be kai ga gamawa ba ma Abrar ya kutsa kanshi ciki, parking lot da motocinshi ne kawai ciki ya nufa ya parker motar dukda yadda hasken fitilu ya haskake faskeken gidan tarrrr kaman rana hakan be hana shi ganin duhu duhu ba kaman ze yi passing out..A sukwane ya nufi sashen sa bakinshi be dena kiran sunan Allah ba, dab da ze sa hannu akan kofar parlon nashi yaji muryarta runtse idanu yayi yana jan tsiririn tsaki..
"Baby Lafiya?"
Rinannun idanunshi ya watsa mata na second biyu kan ya murd'a kofan yana shirin shiga tayi saurin rike kofar tace cikin karyar da murya.."Haba soja na, ban chanchanci haka daga gareka ba fa tunda na ji Abba babba na fad'awa hajiya yaya tahowarka nake zarya tsakanin sashenmu da sashenka duk kawai sbd na ganka wlh nayi kewarka ka tausaya min ko kalma d'aya ce naji na kyautatawa daga gareka ko zanji sanyi.."
Hannunta dake kofar kawai ya kalla cikin wata iriyar murya da ya had'u da gajiya da kuma jirin da yake ji na shirin zubar dashi yace
"Saki kofar nan"
Sanin halinshi yasa ta saki ta tabbatar tunda yace ta sake d'in In Bata sake ba ranta ne ze fi haka 'baci..Bud'ewa yayi ya shige tana ji ya sanyawa kofar key, hawayen da ta kakaro ta share tare da murmushi se kuma ta had'e rai... a fili ta furta
"Na rantse da Allah se na d'aid'aita rayuwarka Abrar se na tabbatar ka rasa duk wani Farin ciki na duniya... ba zan yi fushi ba kuma ba zan karaya ba.. Sannu Sannu Bata hana zuwa sede a jima ba'a je ba.."Tana kai nan ta juya ta d'auki wani tsiririn hanya me d'auke da flowers masu d'auke hankali gefe da gefe... irin girma da kawa da gidan ke dashi na tsaya kallo, daga gani babban family house ne sbd yafi karfin na mutum d'aya, sashe sashe ne had'add'u masu d'auke hankali sun yi guda 12 a tsare a kuma kawace, sam ba'a wargaje suke ba, akwai tarin parking lots masu d'auke da motoci masu d'auke hankali sbd babu kananun motoci a wurin sede Tabbas na Abrar yafi kowanne d'auke hankali motoci ne guda Biyar a cikin parking lot d'in daga Lexus 2021 model, McLaren MP4-12C, Audi A8, Jaguar XJ, Range Rover Apart from BMW da ya shigo dashi...
Da sauri na dakata da bin motocin da suka kawata akalla parking lot shidda d'in dake gidan, nan na bi bayan buduruwar da ban san sunanta ba, Sanye take da wani had'add'en material golden d'inkin doguwar riga me yanayi da wrap gown se black gyale da ta yafa, Don kyau kyakyawa ce, gata da tsawo da diri Masha Allah, seda ta wuce akalla parts hud'u ko tsoron daren bata ji ko Don sbd gidan be da maraba da rana ne sbd yawan kwaiyaye da hasken wutan lantarki ne ban Sani ba, ta isa wani part kofar ta tura ta shige...