⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO**E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE SIX*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
A sadda ya taka wawan birki a kofar gidan be jira gate man ya bud'e gate d'in ba ya sauka ya tura karamar kofar ya shiga cikin hanzari kaman an koroshi, cikin zafin nama ya tura kofar parlorn wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ganinta zaune kan kujera khalid duke a gabanta hannunshi da ruwa me rangwamen sanyi yana bata, gefenta ya karasa ya zauna yana kallonta har lokacin kirjinshi be dena bugawa da sauri sauri ba.
Mikawa khalid tayi cup d'in ruwan a sanyaye take kallon Abrar d'in ta san baze iya magana ba sbd da gaske ya tsorata bata ta'ba ganin abinda ke tsorata Lamidon ta ba irin ace bata da lafiya, hannunshi ta rike tace
"Karka d'aga hankalinka ba wani Abu bane... ya Amatullah?"
Ganin yana so yayi magana kaman ya kasa yasa ta sake kar'ban cup da ruwa dake hannun khalid yana kallonsu ta tsiyaya ta bashi ya sha.Shiru na mintuna kan yace
"Amah me ya sameki?"
Tace
"Ba komai lamido kawai jiri naji ina fitowa daga sashen Hajiya Babba, ya Amatullah d'in hope da sauki?"
Ya san ta fad'a ne kawai sede akwai abinda ya faru d'in ze yi magana Abbu ya shigo sashen wadda ya sa khalid mikewa, idanunshi a kansu ya karaso fuskanshi har lokacin ba walwala...Khalid mikewa yayi ya fice ranshi a 'bace tsohuwar nan tana bukatar a taka mata birki babu me iya aikata hakan se Yayansu amma ya rasa me yasa ya ke kau da kai akansu daga ita har Hajiya Yaya dukda ya san tsawatawa babba baya daga cikin tarbiyarsu, motar shi ya shige ko side d'inshi be koma ba ya kira matarshi a waya ta fito suka tafi asibiti wurin Amatullah...
A parlor kuwa Da ido Amah tabi Abbu har ya zauna kanshi a kasa zatayi magana yace
"Kiyi hakuri... ki kara a kan wadda kike."Abrar da ya runtse idanunshi ne ya mike yana shirin fita Abbu ya kirashi ya dawo ya zauna, yana jin yadda Abbun ke kara bata hakuri, itama hakuri ta bashi ta nuna mishi ai Hajiya Babba itama a matsayin mahaifiya take wurinta duk abinda tayi daidai ne, yaji daad'i sossai nan ya sanar mata ya samu ya shawo kanta ta amince, tattaunawa sukayi sossai kan Amatullah wadda su biyun ke maganganun shi be saka baki ba yana de jinsu.
Bayan sun gama yace da dare da kanshi za shi ya dubata, a nan ma seda suka yiwa yaron nasu fad'a akan aure, kanshi dae kasa yana sauraronsu, shi fa be ce ze yi aure ba gani yake kaman masu uzzurawa iyayen nashi har su ta'azzareshi zasu yi su gaji...
Har bayan kwana biyu baya cikin walwala a gidan sbd maganan auren da suke matsa mishi yau yana Neman cika sati biyu hutun da ya d'auka, kuma a jibi yake son tafiya, yana tunanin ta yadda ze tafi ya bar Amatullah a situation d'in da take ciki, bata ta'ba yarda hindu, ruqayya ko Aisha su taimaka mata tayi wanka in ba yana zaune d'akin ba abinci kuwa se in shine ze bata da kanshi, dukda yanzu baya wani yi mata magana don akwai randa ta so tada mishi fitina ya tsawatar mata har ta samu attack hakan ya sa ya ma rage d'an saukin hali da yake nuna mata, ita kuwa kaman me tsoronshi kaman kuwa shi kad'ai ta yarda dashi a duniya har gwara Amah ta kan yarda da ita, a sati biyun kyaunta ya kara fitowa da hasken fatarta sbd gyara da kulan da take samu...
Sau d'aya Hajiya Yaya da yaranta tare da Nadra suka zo abin be yi daad'i ba sossai suka sake tsoratata wadda dalilin da ya sa ma kenan har lokacin ba'a sallameta ba, Aunty da ba ruwanta bata shiga harkar Amah idan aka cire gaisuwa sannan bata zagi ko ya'ba mata habaice habaice irin na hajiya yaya dukda itama 'ya'yanta duka mata ne sau biyu tana zuwa duba Amatullah haka matan daddy ma su biyu sun zo sun dubata matar Uncle maraq da bata nan ne kawai bata je ba se hajiya Babba..