1

248 14 4
                                    

*🍀SILAR FYAƊE🍀*
           Free Book

          NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN💚

*MARUBUCIYAR*

1 UWAR GIDA NA
3 AUREN DOLE
4 RUHI ƊAYA
5 FAROUK
6 INAYATULLAH
7 ASANADIN ABAYAR SALLAH
8 AKAN AIKINA
9 JAMILA
10 DR NAWWARA PAID BOOK
11 DARASI PAID BOOK
12 SILAR FYAƊE FREE BOOK

Bismillahir Rahmanir Rahim


           1🟨2

. . . .Kuka na ke kamar raina zai fita tsabar tashin hankali,wai yau ni ce agaban gawar mahaifiyata ina kallonta bata numfashi,wani irin ihu na sake sakawa ina girgiza Ummana cikin kuka na ke ce wa"Ummana don Allah ki tashi kada ki mutu,in dai da gaske ne kin mutu to nima tabbas mutuwa zanyi".

"ke wai wacce irin mahaukaciya ce?saboda uwarki ta mutu sai ki saka mutane a gaba kina wani kukan banza?to wallahi ba a gidannan ba,banza karuwa wacce ta bawa wani ɗa namiji jikinta ya yi mata ciki,ai gashinan yanzu kin kashe uwarki da baƙin ciki kinzo kina wani kukan banza da wofi".

Da sauri na jiyo da idanuwa na da sukayi jawur kamar wuta,tsabar tashin hankalin da na ke ciki bai saka na mayarwa da Maman Nusaiba amsa ba,sai ma ba da ƙaimi da na yi akan kukan da na ke yi,don dole suka fita suka ƙyeleni sai da na yi mai isata sannan na yi shiru,ɗan ciki na naji yana ta motsi kamar zai fito wanda tun da na samu cikin baiyi motsi mai ƙarfi haka ba.
Ina ji ina gani aka fita da gawar Mamana,a duk cikin mutanen da suka zo ta'aziyya babu mai rarrashi na, ni kaɗai na ke kuka na ina share hawaye ranar yini na yi banci ba bansha ba,ƴan uwan Mama na suka kawo abinci katan katan suna ta sha'aninsu ɗaura wannan ɗaura wancen,ni dai ina ɗaki ina tunanin rayuwa ta,a shekaruna da basu wuce 15 ba naga rayuwa kala kala.

Ina ɗaki naji Baba na yana ƙwala min kira,da sauri na fito jiki na sai kakkarwa ya ke saboda rashin cin abinci ga juna biyu a jiki na.

"Ke dan iskanci shine ki ka shige ɗaki ki ka ƙwanta uban waye zai yi miki duk wannan aikin da jama'a su ke maza fito ayi da ke,banza ballagaza kawai yaja wani dogon tsaki ya fita.
Ko da na fara aikin wani irin mugun jiri ne ya dinga ɗiba na ina daurewa don nasan halin Baba yanzu zai dawo,a haka har na gama tatar ƙullin kokon,ina tuno da mahaifiya ta ina ta kuka mai ciwo.




   *             *            *

"Girke2 ake a gidan kana shigowa zaka ji ƙamshi ta ko ina,masu aikin gidan kowa da aikinsa,gida ne ƙaton gida mai ƙyau d tsari kana ganin gidan kasan gida ne na masu kuƊi sosai.

A tsakiyar garden ɗin gidan an saka wata mat ƙatuwa doguwa wacce zata sada ka da cikin gidan mai ɗauke da sunan,WELCOME MY LOVELY SON.

Hajiya Barakat ce ta ke ta zagaya gidan tana ganin irin decoration ɗin da aka yiwa gidan,wanda ya yi tace ya yi wanda baiyi ba ta ce bai yi ba.

Da wuri ta saka ƴaƴanta a gaba ƴan mata guda uku masu suna,Zeenat,Rabiat,Aisha,Fatima.

Suka tafi taro babban yayan nasu sojan sojoji wato admiral Aliyu Muhammad,A.A M.





Miss green ce💚🖊️

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now