9&10

84 6 2
                                    

*🍀SILAR FYAƊE🍀*
           Free Book

          NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN💚)

Wattpad user name
   Rabiatu333

 

       9🟫10

. . .. .kuka na fara yi wa Mama ina bata haƙuri,cikin faɗa ta ce"to yanzu ina saƙo na ki ka fara kuka?ko dukanki na yi?",cikin kukan na ce"wallahi Mama saƙon ya faɗi ki yi haƙuri don Allah".

ta fa hannu ta fara yi tana salati ta ce"yanzu Rabi'a yarmin da kuɗin adashin ki ka yi kuɗi dubu hamsin da ɗoriya?amman kin cuce ni Rabi'a yanzu me zance da masu bina bashi"?.

Har yanzu kuka na ke Baba na ya shigo ya ce wa Mama ta yi haƙuri idan ya ɗauki salary zai bata dubu talatin ta rage asara.

Da safe da ƙer na tashi na tafi makaranta gashi muna jarrabawar waec da Neco munyi waec saura Neco,ban rubuta wani abin azo a gani ba,shiru kawai na yi dana shiga ɗakin exam ɗin,na yi ta gumi ina tunanin rayuwa ta,yanzu shikkenan wani cen ya ɓatar min da tantanin budurci na?me zance wa mijin da zan aura?alokaci ɗaya na tuno da Salis gumi ya shiga tsatstsafomin,don tuno da yadda ya ke ƙwatantamin daren farkonmu,to ni ta ina zan nishaɗantar dashi alhali kuma ina on-virgin.

Dukan tebir ɗin dana ke kai wani invigilator ya yi sannan ya ce"lfy me ya faru?can i help u?".

duk lokaci ɗaya ya yi min wannan tambayar yana yimin wani irin kallo,sai a sannan na gane shi malamin daya na ce min sosai kamar wani cingum,na ɗanyi tsaki kaɗan yadda ba zai ji ba,na turo ɗan ƙaramin baki na gwanin sha'awa.
   Lumshe idanu jibril ya yi yana tasbihi a cikin zuciyarsa,don matuƙar ya kalli Rabi'at yana tsintar kansa a cikin wani hali ya juya yana kallonta sosai yarinya kyakkyawa da ita,wato Rabi'at ita ba doguwa ba ita ba gajeriya ba,tsaka tsakiya ta ke,tana da yalwar mazaunai sosai don shiyyasa ma bata saka mayafi kullum sai hijabi,choco colour ce tana da siririn hanci da ɗan ƙaramin bakinta dai dai gwargwado,tana da idanuwa masha Allah waɗanda suka yalwatu da siraran eyelashes masu ɗaukar hankali,pinck lips ɗinta mai matuƙar ɗaukar hankali,tana da gashin jiki wanda ya ƙwanta luf gwanin sha'awa.

To wannan kenan.

Tunda wannan abu ya faru a rayuwata sai na zama so silent wani lokacin sai dai in shiga ɗaki inyi kuka in share hawaye na,abin dai yana matuƙar damuna,Mama tayi2 in faɗa mata abinda ya ke da muna amman abu ya gagara.

Cikin wannan halin ne na yi wani irin fari sosai na ɗashe sosai idanuna sukayi fari ƙal kamar madara,mama na suka ciko sukayi Ɓam dasu,tun abin baya damun mama har ya fara damunta ta shiga bincika ta don yadda na ke matuƘar Ƙellin goshi abin sai wanda ya gani,daman mazaunai ba a maganar su.

On serious Mama ta kafe ni da idanu ta ce"Rabi'atu yaushe rabonki da period?".

Wani irin faɗuwar gaba na ji idanuwa suka kawo ruwa daman ina da matuƙar saurin hawaye,Mama ta daka min tsawa ta ce"me ya faru da ke Rabia na shiga uku me zan gani a gidana?Rabia cikin shege a gidana,mari ta kaimin na kauce ina kuka Baba ya shigo don tambayar ba asi Mama ta hau nu na ni kamar ta ga abin tsoro.

"Ke me ki ka yi mata ta ke nuna ki"?.

ya faɗi hakan cikin tsawa da sauri na ce wai banyi period ba?,gumi ne ya fara tsastsafowa Baba ya ce"Maryam ki faɗa min gaskiya me ya faru da ƴarmu,cikin kuka Mama ta fara faɗa mai duk sauyin dana ke samu,Abba na ya katseta da cewa ta shi mu tafi asibiti zaman gida bai ka ma mu ba.

Test ɗin farko ya nuna ina da shigar ciki har na tsawan wata biyu.

Tun daga wannan ranar Mama ta faɗi jininta ya yi mummunan hawa sosai tun daga nan komai ya canza a gidanmu,idan ka shigo kamad gidan ma ko ki,daman daga ni sai Mama tunda su Afra suna makarantar boarding,yin duniya an tambayeni wanda ya yimin ciki amman naƙi ba da amsa sai kuka har suka gaji suka saka min idanu,ga shi cikin kamar ba na fari ba,don yadda ya ke da matuƙar girma na zama wata babbar mace ko ina ya ciko.

Tun daga ranar da Abba yasan ina da ciki ya daina yimin magana musamman da matarsa ta kamu da ciwo akaina don yana mayuƙar son Mama don yadda kasan layla majno haka suke.sannan Abba ya kori Salis bayan shima yasha tuhuma daga mahaifina don Abba na ƙin yarda ya yi shine ya yi min ciki don yadda muka shaƴu sosai dashi.

Tun daga nan Mama ta yi ta ciwo da ya ke ciwon ba na tashi bane Mama ta mutu,kuka sosai Rabiatu ta farayi don tunowa da mahaifiyarta Afra tana taya ta kukan haka sukayi ta yi babu mai taya su har sukayi shiru.

Cikin kuka Rabiatu tace"wannan shine gaskiyar labarin Afrah,a ina zanga wannan bawan Allah wanda rana ɗaya ya lala tamin rayuwa?da ma ace na ganshi yanzu".sai ta fashe da kuka sosai ya yinda ɗan cikinta ya ke ta wutsil2 babu abinda ya shafe sa.



*Miss green ce*

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now