27&28

143 12 4
                                    

_*🪁SILAR FYAƊE*🪁_

📃BOOK 2

*UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)*

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

   27🟩28

Sosai gabana ya faɗi don ganin wanda na gani,bansanshi ba?ban san daga inda ya ke ba?amman kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba matuƙar ka kalli twins ɗina zakaga babu abinda ya banbanta su kawai abinda ya banbantasu shi babba su kuma yara.

Kasa barin wajen na yi  shi kuwa yana ta siyayyarsa ya fito ta hanyar da na ke,wani glass ne na ɗora hannuna akai ban sani ba ina kallonsa kawai sai naji ya faɗi ƙasa ya tarwatse baki ɗaya,nan ta ke hankalin kowa yayo kaina,nima cikin tsoron na kalli glass ɗin.

Aliyu ma kallo inda yaji ƙarar glass ɗin ya yi sojoji biyu ne a tare dashi,kallona ya shigayi sosai ammanfa bani ɗin ya ke kallo ba hannuna ya ke kallo wanda ya yanke har yana fidda jini amman ni ban san yana fidda jinin ba saboda tsoro da firgici.

A hankali yazo inda na ke nima a lokacin kallon nasa na ke kawai don har yanzu mamakin kamannin na ke.

"Baiwar Allah kina bleeding baki sani ba".da sauri na kalli hannun wanda sai a yanzu naji zafin hannun,alokacin securities ɗin wajen sunzo suna ƙwashe glass ɗin da ya fashe.

Alokacin Layla ta shigo hankalinta a tashe tayo kaina don ganin hannuna yana fidda jini tana tambaya ta me ya faru?amman ban ba ta amsa ba baki na yana rawa na ke nuna mata Aliyu,kallon inda hannuna yabi ta ke yi,a ta ke itama tayo waje da idanuwanta tana kallon inda na ke kallo.

Aliyu mamaki ne ya kamashi ganin suna ta nuna sa alhali basu sanshi ba,ganin shima mamakin ya ke yasa Layla ta buɗe wayarsa ta tako a hankali wajen Aliyu ta buɗe mishi hoton twins.

Shima waro idanu waje ya yi ganin waɗannan yaran masu mugun kama dashi ya yi imanin cewa ko da ƴaƴansa ne da ƙer zasu yi irin wannan kamar.
Da sauri ya ce"baiwar Allah wannan yaran yaranki ne?".

A hankali Layla ta juya ta kalli Rabiatu sanman ta nuna ta da ɗan yatsa,kallon Rabiatu ya yi sosai ganin wai wannan ƴar yarinyar ce mahaifiyar yaran wacce ko a fuskarta bata nuna alamar ta taɓa haihuwa ba a ƙiyasce ma bata fi shekara 18 ba.

A hankali Aliyu ya ta ka ya i'sa wajen da Rabiatu ta ke wacce har a lokacin kallon Aliyu ta ke,a hankali ya ce "baiwar Allah biyo ni waje muɗanyi magana".

Cikin wata iriyar muryar da Rabiatu bata san tana da ita ba tace"in biyo ka kace fa?ka ɗauka zaka ƙara yaudarata yadda ka yaudareni a baya,ka lalata min rayuwata ka cutar dani da gurɓatattun ƴaƴan da ka yi min fyaɗe na haifa maka".

da sauri Aliyu ya juyo jin furucinta fuskarsa ta yi wani irin jajir jijiyoyin kansa suka tashi,da alamar allurar nan ta sojoji za ta tashi,da wani irin sauri ya fita don barin wajen don gani ya ke kamar a mafarki wai yau wata ce ta ke ce masa wai ya yiwa mata ciki.

Da sauri Layla ta kamo hannun Rabiatu don subar wajen don har mutane sun fara taruwa.

Muna fitowa muka iskesa a waje na ta ka a hankali naje inda ya ke,kallonsa na ke gabana yana mugun faɗuwa don ba ko wacce mace ce zata iya kallon Aliyu ta yi masa furucin da na yi masa ba na ce"Bawan Allah idan har kana ja inja akan ba kaine uban waɗannan yaran dana haifa ba muje ayi gwaji hakan shine zai ƙara tabbatar min da zargina don wallahi ko rantsuwa bana yi kaine uban twins.

Da sauri Ola wato sojan dake hannun daman Aliyu zai dakatar dani akan maganar da na kewa ogansu,shima Aliyu da sauri ya ɗaga hannu ya dakatar dashi don ko babu komai wannan yarinyar macece.

Aliyu baice komai ba ya ce"bayin Allah muje asibiti sannan ku ɗauko yaran?don gaskiya ni nasan ban taɓa auren wacce mace na saki ba,ballan tana ace ma wai harni Aliyu inyiwa wacce mace ciki amman ni nasan Allah yana nan.

Motar Aliyu daban tasu Haidar wato Aliyu daban.

Sai da suka shigo layin sannan yaga ashe layin da ya ke ne amman bai ce komai ba.

Atare suka fito harda Mama da kuma su Twins,Mama ma mamaki sosai ta ke na ganin Aliyu don babu abinda zaisa kaƙi cewa shine babansu Twins,shima Aliyu sai yanzu ya ke ganin wata muguwar kamar da sukayi da yaran kallonsu kawai ya ke yana kabbara har a fili.

Wani private hospital suka je aka yi sa a suna zuwa suka shigar da ƙorafinsu aka ɗauki jininsu dukka,shi kuwa Aliyu mamaki kawai ya ke wai yau shine a asibiti ana gwada jininsa wai ana zarginsa da yiwa mace ciki.

Suna zaune wata nurse ta fito ta ce"wai ku shigo dukkanku.

Suna shiga kowa hankalinsa yana kan takaddar gabansa yana faɗuwa,shi kansa likitan sai da gabansa ya faɗi ganin ƴan biyu da kuma Aliyi don kamannin har sunyi yawa.

A hankali ya fara faɗar sakamakon kamar haka;

"a gaskiya wannan gwajin da aka yi ya tabbatar da ƙwatata jinin wannan yaran dana wannan  bawan Allah ƙwata2 ba shine mahaifinsu ba. ..... .

Da wani irin ihu Rabiatu ta yi sannan ta sume a ƙasa sumammiya.


*Tirrrrrƙashi*

anan zan tsaya a wannan littafin na wa mai suna Silar fyaɗe  sai a littafi na gaba wato book3 zamuji tarin tambayoyinku akan waye mahaifinsu twins?bayan ALIYU wa kuke zargi shine nahaifinsu twins?.

kuyi haƙuri Fans wannan litrafin banyo niyyar mayar dashi na kuɗi ba ,saboda wasu abubuwa da suka faru yasa zan mayar dashi kuyi haƙuri👏🏻.

Naira 200kacal ban tsaurara ba ko katin mtn ko ta acc.

Ga masu neman ƙarin bayani ku nemeni ta wannan number tawa.

07068606171
Ummu maher ce👏🏻

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 15, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now