17&18

81 9 5
                                    

*🍀SILAR FYAƊE🍀*

NA💋
*UMMU MAHER(MISS GREEN💚)*

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


17🟨18

Wani tsalle na yi na rungume Anty Rabi ƙanwar mahaifiyata wacce naci sunanta,kuka sosai mukayi a ranar tuno da Mama,sannan Anty Rabi ta ce"babu abinda ban sani ba taƙwara na sanki tun kina ƙaramarki nasan abinda zaki aikata nasan wanda ba zaki aikata ba,amman ina mamakin yadda hakan ta faru".

Kuka ne ya ɓalle min ina cewa"Anty Rabi wallahi ba laifina bane ban san sanda abinnan ya faru ba,na rasa yadda zan fassara abin,na rasa wa zai bani shawara".sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Wani kallon rainin hankali su Khadija suke min don gani suke kawai raina wa mutane wayo na ke amman nasan komai,a ganinsu ta ya ya mace za tayi cikin shege sannan wai ta ce bata san wanda ya yi mata ba?.

A hankali na bawa Anty Rabi labarin komai ina kuka kamar raina zai fita.

Shiru ta yi tana ɗan nazari na sannan ta ce"babu komai Rabi atu Allah n daya ɗora miki shine zai warware komai da yardarsa,abinda na keso da ke ki cire wannan tunanin a ranki ki cigaba da addu'ah Allah ya bayyana komai".

Ƙwananta ɗaya ta ce za taje rijiyar zaki gidan kakaninmu sannan za ta dawo mu tafi Abuja tare da ita don zamana anan ba zai yiyu ba.

naji daɗi ta wani ɓangaren don nasan can babu mai zagi na ballan tana hantara,kuma ga su Laila ƴarta kusan sa a ta ce nasan zan samu nutsuwa.

Amman idan na tuno da barin gidanmu sai naji wani kuka ya kufcemin,ina tuno irin rayuwar da su Salimat zasuyi,don tun yanzu Salimat idan ta fita tun safe sai yamma ta ke dawowa,don tun safe idan Abbanmu ya fita sai dare ya ke dawowa,babu yadda ba ayi da Abbanmu ba akan ya yi aure amman ya yi banza da al'amarin.
da wuri na haɗa kaya na,na shirya twins cikin kayan sanyinsu wanda ya ƙarɓesu sosai gwanin sha'awa ɗaya daga cikin wanda Anty Rabi ta kawo mana jiya da tazo.

Har gida naje na yiwa Mmn junior Sallama tana ta kuka,Mmn nusaiba kuwa cewa ta yi Allah ya raka ta ki gona,daga nan ma in huce birnin sin.

Da wuri Anty Rabi ta dawo alokacin Abbanmu yana shirin fita ta ke sanar dashi hukuncin da ta yanke,magana ɗaya ya faɗa wacce sai da na zubar da hawaye ya ce"Allah ya tsare hanya idan taje ma kada ta ƙara tunawa cewa ni ne ubanta".

abin y ƙular da Anty Rabi sosai amman ba tace komai ba har ya tafi,su kuwa ƙannena su Khadija kallona kawai suke yi amman sun kasa cewa komai har muka rabu.

Idanuwa suna zubar da ƙwallar rabuwa da gida shekara 17 kenan da aka haifeni a wannan gida ban taɓa ƙwana awani waje ba idan ba gidanmu ba tunda ba a saba mana da ƙwanan wani waje ba,ko da kuwa Rijiyar zaki ne unguwar iyayen su Mamanmu.

Tun da na ke a rayuwata yau ne rana ta farko dana hau jirgi sai tsoro ya kamani Anty Rabi ta amshi Ammar ni kuma ina riƙe da Afrah.

Cikin lokaci ƙanƙani muka sauka A Abuja,masha Allah kawai na ke faɗa saboda yadda garin ya ke gwanin sha'awa ga shi luf luf da ya ke lokacin sanyi ne.

Ban ƙara mamaki ba sai da muka shigo unguwarsu Anty Rabi ko wani gida da sunan mai gidan,duk gidan da ka gani sai ka ƙara kallonshi saboda ƙyau da tsaruwarsa.

Gidansu Anty Rabi ma gida ne mai ƙyau ga shi ƙato gwanin sha'awa sanyi da Ƙanshin flowers suna ta yi maka barka da zuwa,ji na yi kawai an rungume ni Laila na gani a gaba na tana ta dariya ta amshi Afrah a hannuna ni kuwa sai kallonta na ke yadda ta ƙara fari ƙal ga wata uwar ƙiba da ta yi,acikin lokaci ɗaya na tuno da yadda na ke ada.
***      ***    ****

Motoci ne sun kai goma suka shigo ƙyaƙyawar unguwar a cikin ta tsakiya ne na hango Admiral A.yana zaune da system ɗinsa a hannu,yana ɗan wani nazari bisa wani bincike da ya ke.

Wayar sa ce ta ɗauki ƙara ganin mai kiran ya sa ya ɗauka a hankali,cikin girmamawa ya ke gaishe da mahaifiyar ta sa cikin yaren yoruba.

Ta ke tambayarsa ya iso Nigeria ne? ya ce mata eh ya shigo?nan ta ƙara yi masa nasiha akan ya kula da matansa musamman ma Rasheeda don ita ce ƴar uwarsa,to kawai ya ce mata sannan sukayi sallama.

A cen ɓangaren su Rasheeda da kuma Salimat kowaccensu taci ƙwalliya ta alfarma don taron miji musamman ma da yau suka cika ƙwana biyar a ɗakinsa ba tare da sun saka shi a idanuwansu ba.




*Ummu Maher ce*

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now