3&4

120 8 1
                                    

*🍀SILAR FYAƊE🍀*
           Free Book

          NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN💚

   
       3🟩4

. . . . .Cikin ta kunsa mai kyau da tsari ya fara sakkowa a jirgin ,fari ne ƙal kamar zaka taɓa sa kaga jini tsabar farinsa,yana da jiki da kuma tsayi, ƙyaƙƙyawa ne shi ajin  farko,yana sanye cikin wasu haɗaɗɗun ƙana nan kaya,waɗanda suka amsa sunansu ya cire cort ɗinsa ya riƙe a hannu yana gƴara necktail ɗinsa.

Ayshe ta fara hangosa ta ce"Hajiya ga yaya cen yana sakkowa,gaskiya yaya ya daɗa ƙyau wallahi gaskiya Hajiya yaya ya fimu Ƙyau".

   Rabiatu ta ce"ke kuma kina kishi ko?ke dai wallahi aisha kishi ne da ke wallahi,ke ce ki ka yo dangin Papa shuwa arab kishi ne dasu".

Hajiya ta ce"kuyi wa mutane shiru zaku fara halin ko?".suka ja bakinsu suka yi shiru ita daman Zeenat da Fatima miskilanci ne dasu irin Yayansu.

Zeenat tana da shekara 25,sai Fatima 22,sai Rabiatu shekara 19,sai Fatima auta mai shekara 17.

shi kuma babban gogan yana da shekara 35 a duniya,Har hajiya ta fitar da ran haihuwa sai kuma ta dawo ta haifi mata har huɗu.
Da sauri Hajiya ta ƙarasa ta rungume ɗanta cikin so da ƙaunarsa duk da sojojin da ke bayansa,shi kuwa jan zaki Aliyu Haidar kunya ce dashi sosai,don haka cikin kunya ya rungume ta,shi daman tun yana yaro kunya ce dashi,tun yana shekara 4 ya daina yadda mahaifiyarsa na yi masa wanka,sai dai ya rufe gabansa ta yi masa,haka har ya girma shi mai kunya ne.

Yana cikin cin abinci wayarsa ta kama ringing ɗin wayarsa,ya ƙi ɗauka Hajiya Barakat ta ce"haba son ka ɗauki wayar mana kaji ko menene?".ta faɗi hakan cikin yaran yarbanci,shima cikin yaran ya ce "to momi".

"Haba A/D ka tausayamin ka dinga ɗaga waya ta,kasan dai babu ƙyau wulaƙanta ɗan adam, please ka yadda ina sonka tsakani da Allah".

"oky".

   kawai ya ce mata ya kashe wayar.

Salimat ta goge hawayen da suka zubo mata don matuƙar ba ta auri admiral ba komai zai iya faruwa,ya zamar mata dole Ƙara Ƙaimi wajen yin addu'ah don komai yazo da sauƙi,tana cikin wannan tunanin ta tashi ta shiga bathroom ta ɗauro alwala ta fara yin sallah tana kai kukanta ga mahaliccinmu subhanahu wata ala.




  ***       ***      ***

yau aka yi 7 ɗin mahaifiyata dangi duk sun fara tafiya,har yanzu mutuwar mahaifiyata tana cikin ƙoƙon zuciyata,na share wata ƙwallar da ta cukomin ƙwarmin idanuna,na gogesu ina cigaba da ƙara tsanar wannan bawan Allahn da ya yi sanadin rugujewar rayuwar a halin gidanmu.

Ƙannena uku ne duk suna bording skull,Salimat,Afra,khadija.

Har lokacin kuma ba a gaya musu rasuwar mahaifiyarmu ba,ko ya ya zasuji idan suka ji mahaifiyarmu ta cika oho?.

ina cikin wannan tunanin naji an watsomin ruwan kanzo mai sanyi,don alokacin safiya ce,na waiga don ganin maiyi min wannan izayar,mmn nusaiba ce da kuma Hafsatu,wacce ta  kasance ƙanwa awajen mahaifina.

Suna ta kumfar baki wai na iya munafunci na shiga ɗaki na ƙi fitowa don nasan na yi abin kunya.

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara fitomin a ƙwarmin idanuwa na,na gogesu na fita don yin aikin da suka ce zuciyata tana yimin ƙuna.




*miss green ce*

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now