*🍀SILAR FYAƊE🍀*
Free BookNA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN💚)Wattpad user name
Rabiatu3335🟥6
"Me Martaba dafatan mun sameku lafiya"?.inji Salimat ta faɗi hakan tana mai sunkuyar da kanta ƙasa alamar girmamawa.
Kallonta Me Martaba ya yi yana yaba hankalin ƴarsa tilo wato Salimat,da ƙer ya buɗe balinsa irin na ƴan sarauta ya ce"lfy ƙlau gimbiya Salima."
shiru Salimat ta yi tana jin kunyar sanar da mahaifinta wannan maganar,gashi kuma babu wanda za ta faɗawa ya faɗa masa don ba ta da uwa araye yau shekarar mahaifiyarta huɗu da rasuwa.
Yasan halin Salimat da kunya saboda haka ya janyo abin rubutu ya miƙa mata ya ce"Gimbiya a rubuta mana anan komene ne?".
cikin sanyi ta amsa ta rubuta abin cikin kunya ta miƙa masa, hannunta yana ta girgiɗi,sai da ta bawa mahaifinta me martaba sannan ta yi dana sanin miƙa masa wannan takaddar.
Mamaki sosai Me martaba ya yi,yana kallon Ƴar ta sa cikin nuna kulawa ya ce"a tashi a tafi zamu nemeki".
Jiki babu ƙwari Salimat ta tashi kamar zata yi kuka,saboda yadda Me martaba ya yi magana don kana jin muryarsa kasan a fushi ya faɗe ta,don tasan abinda ta aikata laifi ne babba a cikin gidan sarauta,kuma gasu fulani kun san yaren fulanj aƘwai kunya,ita dai za ta ɗauki ƙaddarar soyayya don da alama ba tada dacen masoya,ayanzu gimbiya na da shekara 25 aduniya ta ga ƙalubalen soyayya kala2 har kawo i yanzu,saboda wasu don kuɗin mahaifinta suke sonta ba don Allah ba.
*** *** ***Kuka sosai su afra suke kuka bayan sun dawo daga boarding skull don yanzu anyi hutu.
Ina cikin lallashinsu Khadija ta ce"wallahi Anty Rabiatu baki ƙyautawa rayuwarki ba,da ki ka bawa namiji jikinki ya yi miki ciki,yanzu gashinan kin kashe mana uwa da baƙin ciki".
Salimat ma ta ɗora da cewa"Wallahi Anty Rabiatu na tsaneki tsana mafi muni a rayuwata don wallahi ba zamu yafe miki ba,kin kashe mana uwarmu da baƙin cikin ki."ta faɗar hakan ta fita tana hawaye.
Afra ce kawai ta kalleni ta ce"Anty duk da a yanzu shekaru na basu wuce 15 ba amman nasan rayuwa sosai,duk da na girmi Khadija wacce a yanzu tana da sha uku da rabi 1/3,amman ta gane cewa baƙin cikinki ne ya kashe Umma, amman yana da ƙyau mu tsaya muyi miki adalci ke ma,ki faɗa mana abinda ya faru da rayuwarki don wallahi ba zamu yarda da duk wanda ya lala ta miki rayuwa ba".
ƴar dariya kaɗan Rabiatu ta yi sannan ta ce"Afra kenan kina nan da halinki na ƴan jarida?Allah dai ya cika miki wannan burin na ki".
ka saƙe Afra ta yi tana kallon yayar ta cikin tausayi ta ce"Antynmu na sanki da zurfin ciki don Allah ki faɗa min don nima in fita daga sarƙaƙiya please".ta haɗa hannayenta alamar ban haƙuri.
Riƙe hannayen Afrah na yi a hankali na ce"zan faɗa miki Afrah,don hankalinki ya ƙwanta amman a rayuwata ba na son to na asirin kowa,amman ya zama dole shima asirinsa ya tonu".
ina kaiwa nan na tashi na jingina da sip ɗin mahaifiyarmu na fara ba ta labarin.
Labarin ya ɗakko asali ne daga.. .v.
*Miss green ce*
YOU ARE READING
SILAR FYAƊE
Romancesilar fyaƊe labari ne akan wata yarinya wacce wani ya yi mata fyaƊe wanda ita kanta bata san wanda ya yi mata ciki ba,shima kuma bai san wacce ya yiwa cikin ba,kubiyoni don jin yadda labarin zai ka ya.