Alokacin General A.ya shigo da muƙarabansa waɗanda suka rakosa motoci sunfi goma sha,tun daga nesa ya ke kallon kyakkyawar halittar Fahima ga gashinta sai ɗagawa ya ke kamar wara ba indiya ko balarabiya,ya yi tsaye yana kallonta yana mamakin a ina aka samo wannan kyakkyawar yarinyar?.
Dai dai lokacin aka tsuge da ruwan sama mai tattare da ni'ima da ƙanshin ƙasa haɗi dana flowers ɗin gidan,ga wata iska mai daɗi.
Tsalle Fahima ta ke tana wasa da ruwan kana ganinta ka ga yarinya,a hankali Ammar ya biyo ta bayanta ya cire rigar sanyin da ya saka ta sojoji ya lulluɓawa Fahima,da sauri ta juyo cikin tsoro,aka yi rashin sa a ta zame ta faɗo ƙirjin Ammar yadda kasan awani indian film haka abin ya faru,daga shi sai singlet,gashin ƙirjinsa ya ƙwanta kamar wani gashin jariri.
Kallon ƙuda suka shiga yi babu ko ƙiftawa zuciyoyinsu sai bugawa suke kowannensu zai iya juyo ta ɗan uwansa.
A dai dai wannan lokacin kuma hancin motar Hajiya Sakinat ta shigo,bata kula da abin da ke faruwa ba sai da ta fito sai da ta da fa murfin motarta sannan ta iya tsayawa da ƙafafunta,idanunta sunyi jawur kamar gauta wata wutar jaraba da wutar kishi Sakinat taji a ƙirjinta,cikin wani irin mahaukacin sauri ta tunkaro inda su Ammar da Fahima suke.
YOU ARE READING
SILAR FYAƊE
Romancesilar fyaƊe labari ne akan wata yarinya wacce wani ya yi mata fyaƊe wanda ita kanta bata san wanda ya yi mata ciki ba,shima kuma bai san wacce ya yiwa cikin ba,kubiyoni don jin yadda labarin zai ka ya.