11&12

75 7 0
                                    

*🍀SILAR FYAƊE🍀*
           Free Book

          NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN💚)

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444




     11🟦12

. . . .haka muka yi ta kukanmu babu mai rarrashin mu tun daga ranar babu wanda ya Ƙara kukani,Salimat da khadija ko kallon inda na ke ba sayi,Afra ce kawai ke kulani don dama hutun sallah suka zo.



*Bayan wata uku 3*

    Rannan ina ƙwance naji wani mugun ciwo baya ya kamani ga ciwon mara me tsanani ni kaɗai a cikin ɗaki ina ta kiran sunan Allah gwanin ban tausayi abin sai wanda ya gani,na haɗa wata uwar zufa sannu a hankali gumi ya ringa tsattsafomin ɗan cikina ya koma ƙasa baki ɗaya yana ta motsi kamar zai fito.
  Afrah ta shigo kawomin abincin safe taga halin da nake ciki,da sauri ta je ta kirawo su Khadija sai da suka zo buɗe bakin Salimat ta ce"wallahi da ina da dama da sai na kashe Wannan cikin harda uwar ma,don sun jawo mana raini da cin fuska da zagi a gari,ta juya ta kalli Khadija ta ce to ni dai na tafi wajen Asil birthday ɗinshi idan kinga dama ki zauna wajen wannan akuyar idan kin ga dama ki taimake ta".
  tana faɗar hakan ta saka kanta gaba ta yi tafiyarta.

Khadija ma tafiyarta ta yi tana surutai,Afrah ta kalleni cikin tausayi ta ce"Anty jikin da sauƙi yanzu ko in aika akira abba a majalisa".

  Da sauri na girgiza mata hannu alamar kada ta kirasa,ni dai kawai kiran sunan Allah na ke asannu ,a sannu kan ɗa ya fara fitowa na ƙwanta a kan gado ba buɗe ƙafafuna Afra ta riƙe hannuna tana zubar da hawaye,kanta a sunkuye don ba ta son ganin tsiraicina,a haka na dinga faɗin sunan Allah har ɗa ya fito kyakkyawan yaro fari ƙal kamar ɗan larabawa.
Da gudu Afrah ta fita tana haɗa hanya ta shiga gidan Mmn Nusaiba don ta faɗa mata,ta kalli Afrah sheƙeƙe ta ce oh yau Allah ya yi an haifi shege ni da ina da iko da sai na kashe shegen banza".
  Tana faɗin hakan ta yi shigewarta ɗaki tana ta surutai.

  Har ta fito daga gidan ta hango mmn junior kishiyar Maman Nusaiba,ta ce"a ah lfy Afrah me ya farunne?".kunsan maganar gwarawa.

Nan Afrah ta faɗa mata a taƙaice,da sauri Mmn junior ta faɗa gidan tun kafin Afrah ta ƙarasa faɗa mata.

Tana shiga ɗakin ta jiyo nishin Rabiatu da sauri ta ƙarasa ciro mata ƴar budurw Ƙyaƙƙyawar gaske,wani gauran numfashi Rabiatu ta saki tana kiran sunan Allah.

Yaran mmn junior ta fara gyarawa tsaf,sai dai babu kayan saka musu da sauri ta tafi gida ta ɗebo kayan da ta fara tarawa saboda haihuwar da za tayi watan gobe, kala biyar ta ɗebo masu kyau ta sakawa yaran sukayi ƙyau  gwanin sha'awa.

Sannan ta gyara Rabiatu tsaf ta gasata da ruwan zafi sannan ta riƙo ta kamar ƙaramar yarinya,ta saka Afrah ta dafa min ruwan tea da harda madarar ƴan boarding su Afrah.

wani kuka ne yazo min tuna maraici,idan banda maraici me zaisa har mace ta haihuwa a rasa me gyarata,duk da cikin shege ne amman da mahaifiyarta tana nan duk Ƙin da ta ke yiwa yaran za ta kulasu.

Asannan na tuno da AUNTY Rabiatu ƙanwar mahaifiyata wacce ta ke a merica da mijinta,wacce har yanzu bata san yayarta ta rasu ba,saboda sanin irin halin da zata shiga.
***          ***         ***

wani mummunan faɗuwar gaba yaji a take ya zauna yana faɗin sunan Allah messenger ɗinsa ya shigo kawo mai saƙo,da hannu ya nuna mai ya ajje ya tafi,messenger ɗin ya kalli ogan nasa amman babu damar magana saboda halin da ya tsinci kansa alokaci ɗaya,ya shiga kiran sunan Allah har dai abin ya tsagaita masa,amman ranar babu damar aiki don haka ya nufi gida,don har yanzu zuciyarsa zafi ta ke masa.


  ***    ***      ****

"Aliyu abinda ka ke ka yi gaggawar zuwa gida ina son yin magana da kai".

"oky hjy gani nan zuwa".

Hajiya Barakat ta zauna a ɗaki tana jiran zuwan Aliyu,Fatima tace"Hajiya kada ki faɗawa Bro wannan maganar ransa zai ɓaci wallahi".cikin yaren yaroba ta faɗi hakan.

Hajiya Barakat ta daka mata harara ta cigaba da danna wayarta.



*Miss green ce*

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now