23&24

99 11 2
                                    

_*🪁SILAR FYAƊE*🪁_

📃BOOK 2

UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

---------
SIRRINKI👂🏻

ƳAR UWA KI KASANCE MAI RUFE SUTURARKI AKO DA YAUSHE,RUFE JIKINKI YANA TAIMAKA MIKI WAJEN YIN RIGAKAFI GA MUTANE DA KUMA SHAIƊANU.

   23🟩24

. . .. Har Ɗaki jakadiya Binta tabi Gimbiya Salimat don tasan tau ya kamata Salimat ta ƙwana a ɗakin mijinta Admiral A.tunda itace uwargidansa don aurenta aka fara ɗaurawa.

Tana zaune ta yi ta gumi ta sameta,Jakadiya ta samu waje ta zauna a ƙasa ta ce"uwar ɗakina idan babu damuwa aƙwai maganar da na ke so muyi da ke".
Salimat tasan maganar don haka bata ce komai ba ta tashi ta shiga bathroom Ɗin da ke manne ajikin Ƙaton ɗakin na ta,ɗan murmushi Jakadiya ta yi tana mamakin hali irin na Salimat kamar ba ita bace ta ke kukan son Aliyu ba,yanzu kuma ta sameshi sai ta yi wasarere dashi,ta yi wa mahaifiyar Salimat alƙawari tun kafin ta rasu za ta kula da Salimat kamar ita ta haifeta.
Kafin ta fito da sauri ta fita daga ɗakin taje ta ɗauko mata wani magani na sirri da ta aika aka kawo mata tun daga garinsu don ta yi dabarar sakawa Salimat a cikin madara don tasan ta da shan madara,shi wannan sirrin na dabanne wanda ke saka mace ta mallake mijinta ta hanyar shimfiɗarta.


***

babu abinda zance da zamana agidan ƙanwar mahaifiyata don babu abinda na nema na rasa,twins sun ƙara yin wani ƙyau da kuma ƙiba don suna samun abinci mai gina jiki,nima jikina ya ƙara ƙyau ni daman ya ya lafiyar kura don jikina jikin manyan mata ne na ƙara cika da ƙiba.

Ɗakina ma kaɗai abin kallo ne saboda yadda aka ƙawata shi gwanin sha'awa ga kuma suturu sai wanda na ke son zaɓa don wadrope ɗina cike ya ke da kaya masu ƙyau.

Rannan da yamma muna zaune a farlon Anty Rabi Layla ta ce"Sister don Allah inason ki rakani super marker in ɗanyo shopping".

ɗan murmushi na yi sannan na ce "babu komai Allah ya kaimu".

Idris ƙanin Layla ya ce"gaskiya ba za'aje da twins ba a barmin su muyi wasa."Dariya na yi na tashi na ce"ai ni daman yanzu na barmaka twins"dariya ya yi tayi yana murna wai na bar masa twins.

Ƴaƴan Anty Rabi huɗu ne uku maza mace ɗaya,maza biyun suna Germany acen suke karatu.
***
Ƙwalliya Salimat ta yi cikin wasu kayan bacci masu matuƙar ɗaukar hankali,sannan ta feshe jikinta da turaruka kala2,Sallama Jakadiya ta yi sannan ta ce"uwar ɗakina ga madara mai sanyi nasan kina so".

amsa Salimat ta yi tasha tana mai jin daɗin madarar,ta saka lifayarta mai ƙyau ta yi hanyar ɗakin oga Admiral A.

Ta saman bene Rasheeda ta hango Salimat za ta je ɓangaren mijinsu,wani irin malolon baƙin ciki ne ya ɗarsu a zuciyarta ta saka a zuciyarta matuƙar tana numfashi sai ta tarwatsa fadar Salimat,don ta yi alƙawarin sai ta wargaza fadar Salimat awajen Aliyu don ta lura tun yanzu fadarta mai yawa ce awajensa.



Kuyi haƙuri matsalar charge na ke da ita.

*Miss green ce*

SILAR FYAƊEWhere stories live. Discover now