Chapter five

588 7 1
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

05

Kai tsaye office dinshi ya wuce yanata faman tsaki domin har cikin zuciyarshi wani tukuki yakeji..a zahirin gaskia ba iya mgnr da Nur ya fada ne ya bata ranshi kadai ba hadda wnn yarinyar Lamido take ko Gidado...last time daya ganta a clinic sam ba wani tsayawa yayi ya kalleta ba amma dazu despite baya so saida ya kare mata kallo tsaf..kuma a iya kallon da yayi mata ya tabbatar da ta hada jini da fulani...shi sai yanxu ma ya tuna Nur ya taba fada mishi cewar 'yar Gombe ce...lokaci daya yaji gaba daya tsanar yarinyar ya samu matsuguni a zuciyarshi...da yasan bafulatana ce kuma 'yar Gombe da babu dalilinda zaisa ya dauki hannunshi mai daraja yayi mata allura dashi sbd gaba daya Fulani basuyi deserving help ko kuma pity dinshi ba a rayuwa...they are all not worthy of his kindness especially wanda suka fito daga Gombe ya tsanesu..ya tsanesu fiyeda komai..baisan meyasa ganin yarinyar kadai ya dawo mishi da abubuwan da suka faru tsakaninsu da dangin mahaifinsu ba...baisan meyasa tun farkon ganinshi da ita baiyi realising cewa bafulatana bace kuma 'yar Gombe ba har saida yayi mata allura...ya dafe kanshi yasan har abada da ciwon wnn abun zai mutu...yanada riko a rayuwa shiyasa har yanxun ya kasa mance abubuwan da suka faru tsakaninsu da 'yan uwan daddy kimanin shekaru biyar da suka wuce...sam baiji dadin taimakon da yayi mata ba kuma da ace yasan 'yan Gombe zasuzo su cika mashi makaranta da baiyi attempting bude makarantan bama at the first place..haka kuma da yanada damar da zaiyi banning 'yan Gombe and all Fulani from studying at his college da yayi hakan saidai it can never be possible...wnn yarinyan kuwa ji yake kaman yaje ya korata this instant ta bar mashi college dinshi...duk zuciyarshi ta cunkushe ga kuma takaicin da Nuruddeen ya sake dirka mashi duk sun taru suna barazanar fasa mashi zuciya..a fili ya furta"the fool..har wani tunani yake ni inje in zama lecturer dinsu..what nonsense!.."ya karasa mgnr yana dukan table dake gabanshi...haka dai ya karasa yini ranan bai tsinana uwar komi ba a office din...one nayi ya shiga toilet dinshi yayo alwala snn ya fita dan zuwa sallahn jumu'a...driver ya bude mishi kofa ya shiga shima ya zagaya ya shiga saidai kafin ya tayar da motar Nur ya fado cikinta da wani irin sauri kaman wanda aka biyoshi...Bobby bai ce mishi komai sai dan tsaki daya saki tareda kawar da kanshi gefe..shi kuma Nur ya saki hadadden murmushi yana kallonshi yace"i don't mind having a drive with my friend"...da sauri Bobby ya juyo yana kallonshi shima fuska tamke yace"well am not going for a drive as you can see..am going for prayer.. jumu'at prayer sbd haka get out of my car immediately"..kara sakin wani smile Nur yayi yana wani shafa gemunshi yace"i still don't mind going for prayer with my friend and we better get going idan bakaso muyi latti"..tsaki Bobby ya saki yana sakan mishi wani harara murya can kasa yanda driver bazai jiba yace"Fool"..da sauri Nur yace"godia nake my friend..i love you too"..watsa mishi harara kawai Bobby yayi tareda dauke kanshi dan yaga alama idan yaci gabada biyema Nur zai maidashi mahaukaci ne a gaban driver dinshi...shi kuwa Nuru murmushin cin nasara ya kara saki cikin ranshi yace"zakaga rashin mutunchi ai..badai Lamido kayima wulakanci ba dazun?.."tayar da motar driver yayi suka fita daga makarantar...koda suka isa masallacin saida Nur ya sake dirka mashi wani abun haushin..kallon suit dake jikinshi yayi sai ya dan saki tsaki yana girgiza kai yace"yau Friday dinma mutum bazai sa manyan kaya ba..some people need to grow up wlh..basu ajiye komai ba sai shegen zafin rai"...ko kallon inda yake Bobby baiyi ba amma ya shaka iya shaka.😂

Karfe biyu daidai suka baro masallaci...Bobby ba tareda ya dubi Nur dake zaune gefenshi ba yace"a ina zamuyi dropping dinka kasan ba komawa college zanyi ba ni..am going home"..da fara'a Nuru yace"don't worry muje gidan..dama mun kwana biyu bamu gaisa da Mummy ba"..Bobby bai sake yi mishi mgn ba har suka karasa gida...driver na gama parking ko jira ya fito ya bude mishi motan baiyi ba ya bude ya fita abunshi..shi kuma ya dauko briefcase dinshi yabishi a baya...shima Nur fitowa yayi zuwa cikin gidan yana daria kasa kasa gamida girgiza kai dan masifar Bobby daria yake bashi wlh...babu kowa central palor as usual suka wuce parlon Mummy...tana zaune da wasu yammata guda biyu da kallo daya Bobby yayi musu ya wani sake tamke fuska...a hankali ya karasa kusada Mummy ya zauna yanata wani basarwa cikin igbo yace"mummy sannu da gida"...tana murmushi tace"sannu Bobby ya aiki?.."can kasa kasa yace"fine.."Mummy ta maida dubanta ga Nuruddeen daya karaso shima ya zauna kusada Bobby tace"yau an tuna damu knn Nuru"..murmushi yake ya shiga shafa kanshi yace"wlh aiki ne kemin yawa Mummy...duk Bobby ya gama sakar min komai ko taimaka min bayayi"..girgiza kai kawai Mummy tayi tace"to ya aikin?..yasu Mom dinka?.."yace"duk suna lafia Mummy..ina auta?.."tace"auta bai dade da fita ba wai zasuje dubiyan wani abokinsu"..gyada kai Nur yayi alaman gamsuwa...sai yanxu yammatan dake zaune suka samu daman gaishesu...Nur kadai ne ya amsa Bobby kam saima sake tamke fuska da yayi...kallonshi Mummy tayi tace"Bobby bakaga Rayhan bane?.."fuskan nan ba sarari yace"na ganta Mummy"..tace"kuma baka iya amsa gaisuwa ba koh?.."a karkace ya juya yana kallon inda suke murya a dakile yace"lafia lau"..daga haka ya mike ya kama hanyar flat dinshi Mummy ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai..cikin ranta take cewa"Ya Allah ka shiryamin Bobby"...shima Nur mikewa yayi yana duban Mummy yace"Mummy bari in shiga ciki"..kai kawai ta iya daga mishi dan Bobby ba karamin sanyayar mata da jiki yayi ba..ya juya kenan zai tafi aunty sumy da Miemie suka shigo parlon suma...dakatawa yayi da tafiyar tareda wara idanu sosai akan Miemie yace"hey pretty!.."murmushi ta saki itama ta karasa kusa dashi tace"Uncle Nur good evening"yace"evening pretty how are you..how was school?.."tace"Alhamdulillah"...juyawa yayi ga aunty sumy da har ta karasa kusa dasu Mummy ya wani daga hannunshi alamar salute yace"Allah ya taimaki babbar yaya..barka da rana"..aunty sumy na daria tace"barka dai Nur kwana biyu..ya aiki"..yace"normal normal aunty ya naki aikin?.."dan tabe baki tayi kafin tace" babu dadi wlh..duk Bobby ya sakar min komai ni kadai"..daria ya saki yace"nima haka nake fama dashi aunty..saidai hakuri kawai"..yana rufe baki Mummy tace"to ka wuce ka tafi Miemie zata kawo maku abinci yanxun nan"..bai sake mgn ba kuwa ya kama hanyar flat din Bobby...itama aunty sumy mikewa tayi bayan sun gaisa da baqin Mummy ta kama hanyar nata flat din itama...Miemie kuma Mummy tace taje ta cire uniform sai ta kai musu abinci...ba musu ta juya itama zuwa flat din mamanta.

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now