Chapter seven

575 6 1
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

07

Saida ya sake dinke fuskanshi tsaf snn yace"i said speak"..a hankali tayi kasa da kanta tana fidgeting fingers dinta kuma har yanxu gayyar hawaye basu dena sukuwa kan fuskanta ba tace"Sir bacci ne ya daukeni"..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace"da kika jona iron din sai bacci ya daukeki right?.."a hankali ta gyada mishi kai...a fusace yace"how dare you do that?..qona min building kikeso kiyi?.."tayi shiru kanta a kasa..yace"i said qona min building kikesonyi?.."ba tareda ta dago ba ta girgiza kai alaman aah..shi kuma cikin wani additional 6acin rai da yaji yana saukan mishi yace"Billahi if you dare repeat this again you will see the devil side of me..are you mad da zaki jona abu a wuta snn kije kina bacci?.."ya karasa mgn yana wani huci..shi kanshi baisan daga ina wnn 6acin ran ke saukan mishi ba...Nuru ya karaso tareda kama hannunshi yace"zo mu tafi dan Allah what's done is done saidai a kiyaye gaba kuma"..baiyi masa musu ba ya bishi suka fita daga dakin matron ta bi bayansu...suna fita ya daddage ya fizge hannunshi dake cikin na Nuru snn ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga...shima Nur karasawa yayi ya shiga snn ya dauko wayanshi ya kira mai gyara musu wuta yace azo a gyara a yau din nan...bayan ya kammala ya juya yana kallon Bobby daketa faman cika yana batsewa yace" Bobby are sure you are alright?.. wnn 6acin ran duk na meye?.."ko kallon inda yake baiyi ba balle yasa ran samun amsa...shima baiyi expecting amsan nashi dan haka yaci gaba da mgnrshi"you shouldn't have acted like that sai kace secondary school?..besides kudi fa suka biya"..tun kafin ya rufe baki ya juyo yana kallonshi da wani irin karaji yace"seriously bayansu kake bi?..yanxu da sun konamin building zaka iya biyana ne?..kuma da suka biya kudi ai ba kudin building dina suka biya ba kudin zama cikin Hostel suka biya so dole inyi mgn idan naga zaayi min 6arna"...shiru kawai Nuru yayi yana kallonshi deep down yasan da akwai abunda ke damunshi...ya tabbata wnn fushin ba iya na an kusa kona masa building bane dole da akwai wani abun a kasa...har suka koma cikin makaranta ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu...kafin su fita Nuru yace zai sauka dan bai gama aiyukan da yakeyi ba..babu wasting of time driver yayi parking shi kuma ya bude motar ya sauka snn suka cigaba da tafiya...bayan fitarshi Bobby ya sauke wani numfashi da yake rike dashi tun dazu tareda jingina jin seat din da yake hadi da lumshe idanu...baisan wane irin bala'i bane ya hau kanshi yau din nan...shi kanshi haushin kanshi yaji yanaji bai kuma san dalili ba...har ga Allah maganan da Nuru ya fada yasan its not that far from the truth..bai kamata yayi acting kaman yanda yayi ba amma ko Allah ya san shi kanshi baisan abun da ya hau kanshi ba a lokacin..bai kuma san daga ina duk wnn masifan yayita tahowa gareshi ba...kawai shidai ya tsinci kanshi cikin tsananin 6acin rai which he couldn't control..ya lunshe ido yana sake budewa har yanxun idanunshi basu dena hasko mishi ita sanye da kayan 'yan ball ba...ya saki wani tsaki kuma wai sbd tsabar iskanci shine ta juya musu baya wato tunda sun gama ganin gaba su kalli bayan ma knn...yau ya sake tabbatar da cewa ita din sangartacciya ce..idan ba haka ba why yarinya mace kamarta zaa barata tana supporting wani football club kuma har a gidansu a biye mata ana wani siya mata jessy da gajeren wando tana sawa..wai har  bedsheet na Manchester sai kace wata namiji...runste idon yayi yana wani girgiza kai duk a kokarinshi na ya dena ganin pictures din nata saidai to no avail...gaba daya yaji yayi dana sanin zuwa Hostel din ma at the first place..daya sani da Nur ya kirashi kawai yace mishi bazai samu daman zuwa ba da shknn babu shi babu ganin wnn masifa...wnn yarinyar ya rasa wace iri ce ita da take kokarin yi masa kutse cikin rayuwarshi...ya tabbata masifan daya rufeta dashi hadda tsanar da yayi ma 'yan garinsu yasa shi haka...kilan da bai san 'yar Gombe bace bai zama lallai ya aikata abunda yayi ba...jingina ya sakeyi yana kara sakin wani tsakin duk ranshi yabi ya jagule...a daya 6angaren kuma ga wancan mara kunyan da yake kokarin sake kustowa cikin rayuwar 'yar uwarshi again..baisan me yake takama dashi ba har da zai dauki waya ya kirata sbd bashida kunya...sai kuma wnn kaddararren lecture da Mummy tace sai yaje yayima yaran can..shi sam wnn abun bi gamsheshi ba...baima san taya zai fara shiga class ya rike marker yace zaiyi musu lectures ba..baisan ta ina zai fara ba...a takaice har suka kai gida bai dena wadan nan tunane tunanen ba..gaba daya kanshi ya dauki wani zafi kaman wanda ke amfani da wutar lantarki.

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now